Rashin Tinubu ya tilasta wa APC ɗage taron jiga-jiganta

Da zarar mun san lokacin da shugaban zai dawo, za mu iya sanya sabuwar rana na yin taron.

Rashin Tinubu ya tilasta wa APC ɗage taron jiga-jiganta

Bayanai sun nuna cewa an ɗage taron Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar APC na kasa ba zato ba tsammani, da aka shirya gudanarwa a ranakun Laraba da Alhamis wato 11 da 12 ga watan Satumba.

Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar na kasa, Mista Felix Morka, ya bayyana hakan a cikin wata gajeruwar sanarwa da ya fitar a daren Litinin, inda ya tabbatar da dage taron.

“Ana sanar da mambobin Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar APC na kasa cewa, an dage taron Kwamitin Zartarwa na kasa da aka shirya gudanarwa a ranakun Laraba da Alhamis, nan gaba za a sanar da sabuwar ranar da za a gudanar da taron.

“Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da wadannan tarurrukan, amma ba a bayyana dalilin dage taron ba.

Sai dai wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa, matakin da Shugaba Tinubu ya dauka na rashin dawowa gida kamar yadda aka tsara tun ranar Lahadi shi ne babban dalilin da ya sa aka dage taron an dab da za a fara shi.

Tuni aka shaida wa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje cewa, shugaban ba zai dawo a daidai lokacin taron ba, wanda hakan ya sa aka dage shi.

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta ce, “ya kamata Shugaban kasar ya dawo daga China tun a ranar Lahadi, amma a maimakon haka ya tafi birnin Paris.

Ya zuwa ranar Litinin, ya bayyana cewa ba zai dawo a wannan lokaci ba, don haka aka dage taron.

Kodayake canjin jadawalin ya zo kwatsam, majiyoyi sun nuna cewa tun makonni da suka gabata akwai alamaun cewa watakila taron ba zai gudana ba kamar yadda aka tsara.

‘‘Duk da cewa an sanya tallace-tallacen taron a jaridu a makon da ya gabata, amma tuni aka fara shakkun ko taron zai yiwu,” in ji wata majiya ta kusa da shugaban jam’iyyar.

Majiyar ta kuma bayyana cewa, bayan da Kwamitin Zartarwa (NWC) ya rubuta wa Shugaba Tinubu yana neman ya sa musu ranar da za su gana, shugaban ya mayar da martani ta bakin Shugaban Ma’aikatansa, inda ya bukace su da su zabi ranar a watan Satumba.

“Shugaban ya gana da Ganduje da wasu jigajigan jam’iyyar guda biyu, inda ya bayyana karara cewa ya yanke shawarar tsayawa kan Ganduje a matsayin shugaba.

“Da baki ya amince a gudanar taron a wadannan ranaku na 11 da 12 ga Satumba,” inji majiyar.

Wata majiya ta ce, ko a ranar Litinin ma akwai fatan cewa Shugaban zai dawo, amma an gayyaci Ganduje zuwa fadar Shugaban kasa, inda aka sanar da shi cewa shugaban zai tafi Amurka don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya.

Majiyar ta bayyana cewa, Masu kula da Shugaban Kasar ba su tsara yadda ayyukan shugaban zai kasance ba yadda ya kamata.

Da farko, lokacin da ya tafi birnin Paris, ba a sa ranar da zai dawo ba, amma sai dai ya yi gaggawar dawowa don rantsar da mukaddashiyar Alkalin Alkalai ta kasar.

Hakan ya faru ne saboda an gano cewa bai mika wa mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima a hukumance ba.

Yanzu dai ana sa ran Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar APC na kasa zai sake haduwa bayan samun cikakken bayani daga fadar Shugaban kasa kan lokacin da Shugaba Tinubu zai halarci taro.

“Da zarar mun san lokacin da shugaban zai dawo, za mu iya sanya sabuwar rana na yin taron,” in ji wani dan jam’iyyar da ya tabbatar da hakan.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda