Rashin tsaro: Addu’o’in da za a yi a Ramadan —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi ya ce a yi wa Najeriya addu’ar samun tsaro a kwanakin karshen Ramadan.

Rashin tsaro: Addu’o’in da za a yi a Ramadan —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci Musulmi su rubanya addu’o’i a kwanaki 10 na karshen watan Ramadan domin samun tsaro da aminci a Najeriya.

Sarkin Musulmin kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ya bukaci ’yan Najeriya da su zama masu lura a yankunansu game da matsalar tsaro da ke addabar kasar.

“Su yawaita yin HasbunaLlahu wani’mal wakeel;  Astagfirullah; La hawla walakuwata ilabiLlahi-l-Aliyi-l-Azeem; La ilaha illa anta Subuhanaka inikuntu mina zalimeen, Allah Ya kawo wa kasar sauki.

“Majalisar na kuma kira ga Musulmi su mara wa duk yunkurin tabbatar da dorewar Najeriya a matsayin kasa day dunkulalliya baya,” inji sakon da Mataimakin Babban Sakataren Majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya fitar.

Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin ’yan kasa su rika taimaka wa hukumomin tsaro domin magance matsalar da ta zama ruwan dare.

Ya yi kiran ne yayin nuna damuwa game da yadda rashin tsaro ya haifar da kashe-kashe da kuma tsoro, zullumi, rudani, da a zukatan ’yan Najeriya.

Don haka, Sanarwar ta da Mataimakin Babban Sakataren Majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya fitar ta bukaci “gwamnati a dukkannin matakai su ninka kokarin da take yi wurin tsare rayuka da dukiyoyin jama’ar kasar.”

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Mutane Biyu Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Ruwan Sama A Gashuwa

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro