Rashin tsaro: Aisha Buhari ta bukaci daukar karin jami’an tsaro
Uwar gidan Buhari ta bukaci a dauki karin jami’an tsaro don yakar ta’addanci.
Mai dakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta bukaci hukumomin tsaron kasar da su kara daukar sabbin jami’an tsaro don yakar matsalar tsaro da ta addabi wasu yankuna na kasar nan.
Ta yi wannan kira ne ranar Litinin yayin da take karbar bakuncin matan Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya yayin ziyarar girmamawa da suka kai mata Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
- Najeriya za ta fara buga wa kasar Gambiya takardun kudade
- Sanata Goje ne ya fi dacewa da Shugabancin APC — Kungiyoyin matasa
Aisha Buhari ta yi kira ga matan hafsoshin da su mara wa mazajensu baya domin samun nasarar nauyin da Shugaban Kasa da al’ummar Najeriya suka dora musu.
Aisha ta bayyana irin rawar da matan hafsoshin ka iya takawa wajen samar da tsaro a fadin Najeriya.
Kazalika, ta umarce su da su kasance masu amince wajen kawo ci gaba ga harkar tsaro a Najeriya.
Ta kuma yi kira da a dinga biyan sojoji da iyalan wanda suka mutu hakkokinsu a kan lokaci don amfana.
Da ta ke nagta jawabin, matar Shugaban Hafsan Tsaro, Misis Victoria Irabor, wacce ta jagoranci tawagar, ta yaba wa Uwar Gidan Shugaba Buharin kan rawar da ta ke takawa a matsayinta na uwa da kuma goyon baya ga iyalan jami’an tsaro.
Ta ce iyalai da dama na wadanda suka jikkata da wanda suka rasu daga soji sun sami tallafi daga uwar gidan Shugaban Kasar.
Daga nan ta kuma ce iyalan sojin kasar nan na nuna jin dadinsu da kuma irin goyon baya da matar shugaban kasa ke ba su.
Daga cikin wanda suka halarci taron akwai matar Sufeton ’Yan Sanda, matar Darakta-Janar na Sashen Bincike da matar mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Sha’anin Tsaro.