Rashin tsaro: An rufe makaratu a kananan hukumomi 20 a Sakkwato

Wani malami da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an sanar da su an rufe makaranta ciki har da wadda yake karantarwa.

Rashin tsaro: An rufe makaratu a kananan hukumomi 20 a Sakkwato

Kujeru a cikin aji a makarantar Bethel Baptist a Damishi, Jihar Kaduna inda ’yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai fiye da 100. (Hoto: Reuters). 

Matsalar tsaro na kara ta’azara a jihar Sakkwato har ta kai ga gwamnatin jihar ta rufe makarantun boko a kananan hukumomi 20 daga cikin 23 da jihar ke da su.

Sanarwar da aka aiwakawa shugabannin makarantu wadda Sakatarensu ya sanya wa hannu, ya ce “an umarce ni na sanar da dukkan shugabanni makarantu a ƙananan hukumomi 20 cewa su rufe makarantunsu daga ranan Litinin sai abin da hali ya yi.”

Ya ce makarantun da ke ƙananan hukumomin Sakkwato ta Kudu da Sakkwato ta Arewa da wasu makarantu da aka zaɓa a ƙananan hukumomin Wamakko da Dange Shuni za su ci gaba da karatu ba sa cikin waɗanda aka rufe.

Wani malami da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an sanar da su an rufe makaranta ciki har da wadda yake karantarwa.

Ya ce suna ganin an rufe makarantun ne saboda matsalar tsaro da ke ƙara yawaita a jihar, ganin kullum sai ’yan bindigar sun shiga gari ko ƙauye a yankin Gabas ko kudancin jihar Sakkwato.

Jami’an gwamnatin Sakkwato sun ƙi aminta su yi magana da waƙilinmu kan matsayar domin an gargaɗe su cewa takardar sirri ce, kar a bari ta fita ga duk wanda hukuma ba ta amince masa ba.

“Saboda harkar tsaro ne ya sa ba a ba da bayani ga manema labarai an rufe makarantun a hukumance ba, amma duk makarantun gefen Sakkwato an rufe su,” kalaman wani jami’in gwamnatin jihar Sakkwato ya bayyana.