Rashin tsaro da ambaliyar ruwa ta raba mutum miliyan 6 da muhallansu

Matsalar tsaro na ci gaba da zama babbar barazana a wasu jihohin Najeriya.

Rashin tsaro da ambaliyar ruwa ta raba mutum miliyan 6 da muhallansu

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Bakin haure ta Kasa, ta bayyana cewa sama da mutum miliyan 6.4 ne suka rasa muhallansu sakamakon matsalar tsaro, ambaliyar ruwa da sauransu.

Shugaban hukumar, Alhaji Tijjani Aliyu ne ya bayyana haka yayin wata ziyara da ya kai Jihar Katsina.

A cewarsa, ya zuwa 2022, alƙaluman hukumar sun nuna cewa mutum kusan miliyan uku ne, suka rasa matsugunansu.

Sai dai ya ce cikin matsalolin akwai matsalar ambaliya da sauran iftila’i, wanda hakan ya sa aka samu karin kashi 100 na irin waɗannan mutanen da suka rabu da gidajensu.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa, “A halin yanzu gwamnati ba za ta iya samar wa kowa da matsuguni ba.

“Saboda haka ne ta samar da shirye-shiryen horar da su sana’o’in hannu da za su taimaka musu wajen dogaro da kai.”.

Idan ba a manta ba a shekarar da ta gabata, an samu mamakon ruwan sama, lamarin da ya haifar da ambaliya a jihohi irin su Bauchi, Katsina, Kano, Zamfara, Sakkwato, Kaduna, Kebbi, Neja, babban birnin tarayya da sauransu.

A gefe guda kuma, matsalar tsaro musamman a Arewacin Najeriya na ci gaba da barazana, lamarin da ya sanya mutane da dama yin ƙaura daga gidajensu.