Rashin tsaro: Kungiyar Izala ta umarci limamai su yi Alkunut

JIBWIS ta ce matsalar tsaro a Najeriya bukatar a koma ga Allah a nemi dauki.

Rashin tsaro: Kungiyar Izala ta umarci limamai su yi Alkunut

Shugaban Kungiyar JIBWIS, Shaikh Abdullahi Bala Lau

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta umarci lamamai su fara yin addu’ar Alkunut a salloli don Allah Ya kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Shugaban JIBWIS na Kasa, Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bayar da umarnin, inda ya ce tabarbarewar sha’anin tsaro a Najeriya na bukatar jama’a su koma ga Allah su tuba gare shi.

A makon jiya wasu masallatan Juma’a sun fara gabatar da addu’ar ta Alkunut wadda ake yi idan aka samu bullar annoba ko wata matsala da ta addabi jama’a.