Rashin tsaro: Malaman Arewa sun shirya addu’o’i na musamman

Malaman sun roki Allah Ya taimaki Janar Christopher da sojoji wajen magance matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma

Rashin tsaro: Malaman Arewa sun shirya addu’o’i na musamman

Malaman Musulunci kimanin 70  daga Arewa maso Yamma suka hallara a Kaduna domin gudanar da taron addu’o’i na musamman da nufin samun da zaman lafiya da cigaban yankin.

Malaman da suka fito daga jihohin Kaduna, Kano, Sakkwato, Jigawa, Zamfara, Kebbi da Katsina, sun kuma yi addu’ar nasara ga Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa da rundunar sojojin Nijeriya.

Sun roki Allah Ya taimaki Janar Christopher wajen magance matsalar ’yan fashin daji da da masu garkuwa da mutane da suka ta addabi yankin.

Jagoran taron addu’ar, Malam Lawal Ibrahim BK, ya nuna damuwarsa bisa yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a yankin.

Ya bayyana fatan addu’ar za ta kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na Arewa maso Yamma

Malamin ya ce “Mun yanke shawarar gudanar da taron addu’o’i ne ga yankin Arewa maso Yamma saboda yankin na fuskantar matsalar tsaro da suka hada da ’yan fashin daji da garkuwa da mutane.

“Mun kuma hada da Babban Hafsan Tsaro da na sojojin Najeriya cikin addu’o’in namu, muna masi fatan Allah Ya ba su ikon shawo kan duk wani kalubale da suke fuskanta,”in ji Malam Lawal Ibrahim.

Ya kuma jaddada cewa malamai 70 da suka halarci taron, wadanda suka fito daga yankin Arewa maso Yamma, su ganau ne a kan matsalar tabarbarewar al’amuran tsaro a yankin.

Manyan malaman da suka halarci taron sun hada da Shaikh Muhammad Nur daga Katsina da Malam Jamilu Ismail daga Kano da Malam Rabiu Al-Mustapha daga Sakkwato da kuma Malam Kamaludeen Ismail daga Zamfara.