Rashin tsaro: Matasan Kiristoci sun yi barazanar juya wa Jonathan baya a zabe

Matasan Kiristocin Najeriya sun ce ba za su kada wa Shugaban kasa Goodluck Jonathan da sauran ’yan takarar mukaman siyasa a kasar nan kuri’unsu ba sai sun samar wa kasar nan zaman lafiya.  Shugaban kungiyar Matasan Kiristoci ta shiyyar Arewa ta Tsakiya, Injiniya Daniel Kadzai ne ya bayyana haka a Lafiya lokacin da yake tattaunawa […]

Rashin tsaro: Matasan Kiristoci sun yi barazanar juya wa Jonathan baya a zabe
Rashin tsaro: Matasan Kiristoci sun yi barazanar juya wa Jonathan baya a zabe

Matasan Kiristocin Najeriya sun ce ba za su kada wa Shugaban kasa Goodluck Jonathan da sauran ’yan takarar mukaman siyasa a kasar nan kuri’unsu ba sai sun samar wa kasar nan zaman lafiya. 

Shugaban kungiyar Matasan Kiristoci ta shiyyar Arewa ta Tsakiya, Injiniya Daniel Kadzai ne ya bayyana haka a Lafiya lokacin da yake tattaunawa da manema labarai kan rikicin Boko Haram da sauran rikice-rikice da suke addabar kasar nan da kuma ayyana niyyar Shugaba Jonathan na sake tsayawa takara a 2015.
Ya ce batun rashin tsaro a kasar nan sai dada karuwa yake yi kullum, musamman idan aka yi la’akari da yadda ’yan Boko Haram ke ci gaba da cin karensu babu babbaka wajen hallaka rayuka da lalata dukiyoyin al’ummar kasar nan da ba su ji ba, ba su gani ba.
Ya ce abin takaici shi ne yadda maimakon Shugaba Jonathan ya yi kokarin tabbatar da tsaro a kasar nan musamman a Arewa maso Gabas sai ya fito yana bayyana cewa zai sake fitowa takara a badi babu kunya. “Mayakan kungiyar Boko Haram sun kwace wasu kananan hukumomi a Arewa maso Gabas da suka hada da Madagali da Michika da Mubi da Hong da Gombi a Jihar Adamawa da Gulani da Buni Yadi a Yobe da wasu kananan hukumomi takwas a Borno, bayan Shugaba Jonathan ya yi alkawari kawo karshen wadannan rikice-rikice tun a shekarar 2012,” inji shi.
Ya kara da cewa a shekarar 2013 ma Shugaba Jonathan ya yi alkawari zai gina sabuwar Najeriya da kowane danta zai yi alfahari da ita. Amma maimakon haka sai mummunar Najeriya yake ginawa, inda talakawa ke rasa rayukansu ba gaira ba dalili.
Shugaban Matasan Kiristocin ya ce tun da aka sace ’yan matan Chibok, Gwamnatin Tarayya ta yi ta alkawari za ta kwato su daga hannun ’yan Boko Haram amma har yanzu ba a san ma inda suke ba, balle a kwato su.
Y ace don haka kungiyar Matasan Kiristocin Najeriya na shiyar Arewa ta Tsakiya ta yanke shawarar kin kada wa Jonathan da sauran ’yan takara a kasar nan kuri’unsu a zabe mai zuwa sai sun tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kowane sashin kasar nan. “A namu bangaren za mu ci gaba da hana matasan Kiristoci kada wa wani dan takarar kujerar siyasa a kasar nan kuri’unsu sai an samu zaman lafiya a kasar nan, wato babu zaman lafiya babu zabe,” inji shugaban.
Ya shawarci shugabannin jihohin Arewa maso Gabas cewa kada ma su yi wahalar zuwa gida don yin kamfen don ba za a zabe su ba sai sun dawo da zaman lafiya a yankunansu.