Rashin tsaro ne ke kawo mana cikas -Dokta Yusuf Mabera
Cibiyar yada addinin Musulunci da tattaunawa kan addinai daban-daban ta ce matsalar rashin tsaro ita ce babbar matsalar da ke ci wa kungiyar tuwo a kwarya.Shugaban cibiyar, Dokta Yusuf Mabera shi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Jihar Legas.Dokta Mabera ya ce, “Cibiyar da muka kafa ta yada addinin Musulunci […]

Cibiyar yada addinin Musulunci da tattaunawa kan addinai daban-daban ta ce matsalar rashin tsaro ita ce babbar matsalar da ke ci wa kungiyar tuwo a kwarya.
Shugaban cibiyar, Dokta Yusuf Mabera shi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Jihar Legas.
Dokta Mabera ya ce, “Cibiyar da muka kafa ta yada addinin Musulunci da tattaunawa kan sauran addinai tana gudanar da ayyukanta kamar yadda ya kamata kuma kiristoci da dama suna zuwa suna karuwa da ilimi, amma daga baya da aka sami matsalar rashin tsaro a yankunan Arewa, sai suka daina zuwa saboda suna tsoron kada wani abu ya same su. Muna fatan abubuwa za su daidaita ta yadda za a sami zaman lafiya a yankin Arewa domin abokanmu kiristoci su ci gaba da zuwa cibayarmu domin neman ilimi. Haka shi zai sa a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasar tattalin arziki a kasa baki daya”.
Sai ya ce cibiyar na gudanar da ayyukanta tsakani da Allah ne don yada addinin Musulunci ba don neman abin duniya ba, kuma abin da ta saka a gabanta shi ne yadda za ta dinke barakar da ke tsakanin musulmi da kiristoci da masu bin sauran addinai na rashin kusantar juna.
“Gaskiya musulmai da kiristoci sun yi nesa da juna. Wannan ne ya sa ba a fahimtar juna kamar yadda ya kamata. Amma da ana kusantar juna ana tattaunawa a tsakani da babu shakka za a fahimci juna sosai kuma kowa zai fahimci inda dayan ya sa gaba. Wannan ita ce matsalar da muke so mu gyara ya zama an sami kusanci a tsakani ta yadda za a fahimci juna’. Inji shi.
A karshe ya bukaci jama’a su ba cibiyar tasu goyon baya don ganin ta cimma burin da ta sa a gaba na karantarwa da wa’azi da kuma ilimantar da jama’a gaskiyar lamarin rayuwa.