“Rashin tsaro ya hana ceto mutum 30 da suka maƙale wajen haƙar ma’adinai”

Shugaban ya ce ba shi tabbacin adadin da aka ceto saboda hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

“Rashin tsaro ya hana ceto mutum 30 da suka maƙale wajen haƙar ma’adinai”

Gwamnatin Jihar Neja, ta ce rashin tsaro ya hana ceto mutum 30 da suka maƙale a wata mahaƙar ma’adinai da ta rufta a Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Ya ce har yanzu hukumar ba ta samu cikakkun bayanai kan adadin da aka ceto ba saboda rashin tsaro a yankin.

Babban daraktan, ya kuma ce hukumar ta samu rahoton yadda ’yan bindiga ke kai hare-hare a yankunan Shiroro da Mashegu a jihar.

Ya ce ’yan bindiga sun kai hari a kauyen Adogo Malam a ranar 2 ga watan Yuni, tare da yin awon gaba da mutum shida.

Ya kuma ce, ’yan bindiga sun yin garkuwa da sama da mutum 20 tare da sace shanu a yankin Tunga Kawo, wani yanki da ke maƙwabtaka da Erena.

Amma a cewarsa tuni suka tura jami’ansu ƙauyen Farin Doki, inda aka samu iftila’in, don ceto mutanen da ke birne a ƙarƙashin ramin.

Rahotanni sun ce gomman mutane ake tsammanin sun mutu, ko da yake hukumomi sun ce adadin yana iya zarta hakan.

Baba-Arah ya ce wajen haƙar ma’adinan ta rufa ne sakamakon mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a yankin.

Ya nuna damuwarsa kan yadda masu ceto suka tsere daga wajen sakamakon ci gaba da rufatawa da ramukan ke yi.

Amma ya ce an tura mutane masu aikin haƙar ma’adinai a yankin domin gudanar da aikin ceto.