Rashin tsaro: Za a sauya wa makarantu 359 wurin zama a Kaduna

Taaddancin ’yan bindiga a Kaduna ya tilasta wa gwamantin jihar tunanin hade wasu makarantu guda 359 da ke yankunan da ake yawan samun hare-hare.

Rashin tsaro: Za a sauya wa makarantu 359 wurin zama a Kaduna

Wata makaranta da aka rufe saboda hare-haren ‘yan bindiga

Taaddancin ’yan bindiga a Kaduna ya tilasta wa gwamantin jihar tunanin hade wasu makarantu guda 359 da ke yankunan da ake yawan samun hare-hare.

Gwamnatin na niyyar hade makarantun ne da wadanda ke yankunan da ke da zaman lafiya a sassa daban-daban na jihar.

A ranar 7 ga watan Maris, ’yan bindiga sun sace dalibai sama da 250 daga makarantar firamare ta LEA Kuriga, inda daga baya aka sako 167 daga cikinsu, makonni biyu bayan wani farmaki da sojoji suka kai musu.

Gwamna Uba Sani wanda shugaban ma’aikatansa Sani Kila ya wakilta, ya sanar da wannan mataki ne yayin wani  taron manyan jihar da kuma horas da sabuwar rundunar kare makarantu da aka kafa.

Hakan wani bangare ne na shirin gwamnatin tarayya na Safe School Initiative, mai nufin inganta matakan tsaro don kare makarantu da dalibai da kuma malamai daga hare-haren da‘yan ta’adda.

Da yake bayyana damuwarsa kan yadda ’yan ta’adda ke kawo cikas ga harkokin tattalin arziki da zamantakewa, Gwamna Uba Sani ya jaddada mahimmancin kare fannin ilimin jihar.

Gwamnan ya ba da misali da yadda aka samu raguwar yaran da ke shiga makarantu firamare da 200,000 a shekrar karatun 2022/2023 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Gwamna Uba Sani ya danganta koma bayan da aka samu da rashin tsaron da ya addabi yankunan Chikun da Birnin Gwari da Kajuru da Giwa da kuma Igabi.

Ya ce “Domin tabbatar da ilimi ga yaran a yankunan da ake fama da rashin tsaro, gwamnati ta fara aikin hade makarantu 359 da wadanda ke yankuna masu tsaro”.

NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga

’Yan bindiga sun lalata tashar wutar lantarkin da ake ginawa a Kogi

Trump ya bai wa Elon Musk muƙami a Gwamnatin Amurka

Dalilin da ke haddasa yawaitar katsewar lantarki — EFCC