Rashin ’yan sanda ba zai hana mu zaɓen ƙananan hukumomi ba — Fubara

Hukumar Zaɓen Jihar Ribas  RSIEC ta ce a shirye take ta gudanar da zaɓen na gobe.

Rashin ’yan sanda ba zai hana mu zaɓen ƙananan hukumomi ba — Fubara

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara

Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya bayyana cewa za su gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar a gobe Asabar ko da babu tsaron ’yan sanda.

Mista Fubara ya ce a madadin haka, wasu jami’an tsaron za su bayar da tsaron da ake buƙata a yayin zaɓen na gode.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake bayyana mamakinsa game da zargin ‘yan sanda da yunƙurin mamaye harabar Hukumar Zaɓen Jihar (RSIEC) da nufin kawo cikas ga zaɓen ƙananan hukumomin da ake shirin gudanarwa.

A jawabinsa yayin wani taron manema labarai a birnin Fatakwal a yau Juma’a, Gwamna Fubara ya ce yunƙurin ya zo da mamaki kasancewar ya samu labari a baya da ke nuna cewar ‘yan sanda na niyyar janyewa daga zaɓen ƙananan hukumomin.

Ya kuma yi tambayar ko mene ne dalilin da ya sa Jihar Ribas ta fita daban, musamman abinda ya bayyana da sa ido mara tushe a kan hukumar zaɓen da ke ƙarƙashin hurumin jiha.

Ya kara da cewar hukuncin Kotun Abuja ya umarci ‘yan sanda ne kawai da kada su samar da tsaro, amma ba wai su mamaye harabar hukumar zaɓen jihar ko kuma yin katsalandan a zaɓen ba.

A cewar gwamna Fubara, kamata ya yi a bai wa hukuncin Babbar Kotun Jihar Ribas fifiko, kasancewar shi aka fara bayarwa.

Ba za mu shiga zaɓen ba — ’Yan sanda

Rundunar ‘yan sandan Ribas ta bayyana cewa za ta aiwatar da umarnin kotu game da zaɓen ƙananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a faɗin jihar a gobe Asabar.

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da kakakinta, SP Grace Iringe-Koko, ta fitar mai taken: “zaben shugabannin ƙananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a ranar 5 ga watan Oktoban da muke ciki.”

A cikin sanarwar, rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da samun umarnin kotun da ya hana ta gudanar da aikin tabbatar da tsaro yayin zaɓen ƙananan hukumomin.

Rundunar ta ƙara da cewa tana sane da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta zartar na ranar 30 ga watan Satumbar da ya gabata wanda ya hana ta shiga a dama da ita a zaɓen.

Sanarwar ta ci gaba da cewa sashen harkokin shari’a na rundunar ya ba da shawarar cewar hukuncin kotun na 30 ga watan Satumba ya fi muhimmanci.

Mun shirya tsaf — RSIEC

A nata ɓangaren, Hukumar Zaɓen Jihar Ribas  RSIEC ta ce a shirye take ta gudanar da zaɓen na gobe, inda ta ce za ta gudanar da zaɓen kamar yadda dokokinta suka tanada.

Shugaban RSIEC, Adolphus Enebeli ya ce suna la’akari ne da hukuncin Kotun Ƙoli, wanda ya ce dole a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a dukkan jihohin Najeriya, sannan ya ƙaryata batun cewa ba su fitar da rajistar masu kaɗa ƙuri’a ba.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025