Rashin ‘yanci ga kananan Hukumomi ne ya haifar da koma-baya – Rimi
Tsohon Shugaban karamar Hukumar Sumaila dake Jihar Kano, Alhaji Abdulhamid Idris Rimi ya yi kira na musamman da a baiwa kananan hukumomi cikakken ‘yancin su ta yadda za a sami ingantaccen ci gaba a kasar nan. Ya yi wannan kira ne cikin zantawar su da wakilinmu, inda ya nunar da cewa rashin ‘yanci ga […]

Tsohon Shugaban karamar Hukumar Sumaila dake Jihar Kano, Alhaji Abdulhamid Idris Rimi ya yi kira na musamman da a baiwa kananan hukumomi cikakken ‘yancin su ta yadda za a sami ingantaccen ci gaba a kasar nan.
Ya yi wannan kira ne cikin zantawar su da wakilinmu, inda ya nunar da cewa rashin ‘yanci ga majalisun kananan hukumomi ne ya haifar da koma baya musamman a yankunan karkara, inda aka fi dogaro da su.
Ya ce a lokacin da kananan hukumomin kasar nan suke da cikakken ‘yanci kowa ya ga irin ci gaban da aka samu bisa yadda suke yin amfani da dan abinda suke karba daga asusun tarayya wajen aiwatar da ayyukan raya kasa, sabanin yadda lamarin yake a yanzu na tsarin asusun hadaka da gwamnatocin jihohi wadda ke haifar da kashin dankali.
Dangane da zargin da ake yi cewa ana tafka barnar dukiyoyin al’uma a kananan hukumomi kuwa, tsohon shugaban karamar hukumar ta Sumaila ya ce “Wannan zargi ba gaskiya ba ne, inda ya bada misalin cewa har yanzu babu wata hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da ta sami wani shugaba na karamar hukuma da wani laifi na satar dukiyar al’umma, don haka zargin da ake yi wa kananan hukumomi ba shi da tushe” in jishi.
A karshe Rimi ya sanar da cewa duk da kasancewar sun yi shugabanci cikin yanayi na karancin kudi a kasa amma sun yi bakin kokarin su wajen aiwatar da ayyukan hada garuruwa da wutar lantarki da samar da ruwan sha da tabbatar da tsaro da kuma gyaran hanyoyi bisa goyon bayan da ya samu daga gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.