Rashin zaben APC a dukkan matakai matsala ne – Adamu Damboa

Wani tsohon dan siyasa kuma jigo a Jam’iyyar APC a yankin Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Adamu Shuwa Damboa ya bukaci al’ummar Najeriya su zabi jam’iyyar daga sama har kasa domin tabbatar da sauyi mai ma’ana a kasar nan. Alhaji Adamu Damboa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Abuja, inda ya […]

Rashin zaben APC a dukkan matakai matsala ne – Adamu Damboa
Rashin zaben APC a dukkan matakai matsala ne – Adamu Damboa

Wani tsohon dan siyasa kuma jigo a Jam’iyyar APC a yankin Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Adamu Shuwa Damboa ya bukaci al’ummar Najeriya su zabi jam’iyyar daga sama har kasa domin tabbatar da sauyi mai ma’ana a kasar nan.

Alhaji Adamu Damboa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Abuja, inda ya ce kuskure ne wasu ’yan siyasa su rika cewa za su zabi APC a sama saboda Janar Muhammadu Buhari ya zama Shugaban kasa, amma a kasa za su zabi wasu jam’iyyun daban.
Alhaji Damboa ya ce, idan aka zabi Buhari a matsayin Shugaban kasa, ba a zabi ’yan Majalisar Dattawa da ta Wakilai da zai samu rinjayen da yake bukata don gudanar da mulki ba matsala ba, an yi aikin baban giwa ke nan.
Ya ce Janar Muhammadu Buhari wanda alama ta nuna shi ne zai lashe zabe mai zuwa in Allah Ya so, yana bukatar rinjaye a majalisun biyu da kuma gwamnoni domin ya samu damar aiwatar da ayyuka cikin sauki da nasara, kuma ya samu goyon baya wajen sake mayar da kasar nan kan gwadabe nagari.
Alhaji Adamu Damboa ya ce, zaben Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa wajibi ne, idan aka lura da yadda al’amura suka tabarbare a kasar nan, “Domin haka wajibi ne jama’a su yi watsi da PDP domin kawo sauyin da zai sa su koma cikin hayyacinsu, maimakon zaman fargaba da tsoro da mugun mulki da PDP ta haifar musu. “Ni jigo a PDP a da, amma yadda al’amura suka tabarbare ne suka sanya muka fice daga jam’iyyar tun lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya fara fitowa takara a karon farko,” inji shi.
Alhaji Adamu Damboa ya ce, duk yadda Janar Buhari ya kai da kwazo yana bukatar mataimaka, da za su taimaka masa wajen kawo gyara a kasar nan.
Ya ce, masu zargin cewa idan Buhari ya zama Shugaban kasa, zai yi kama-karya irin na zamanin soja suna soki burutsu ne kawai, kuma gara mulkin kama-karya da mulkin kama-kashe da ake fama da shi a kasar nan a yanzu.
Ya ce, galibin wadanda suke kewaye da Shugaba Jonathan ba masu kaunar kasar nan ba ne, mutane ne da babu abin da ya dame su sai cika aljihunsu kawai, kuma shi ya sa al’amura suka tabarbare ba tare da suna nuna damuwarsu ba.