Rasuwar Adamu Fika: Mun yi rashin dattijon arziki a Yobe – Mai Mala Buni

Gwamnan ya ce zai yi wahala a iya cike gibin da ya bari

Rasuwar Adamu Fika: Mun yi rashin dattijon arziki a Yobe – Mai Mala Buni

Wazirin Fika, Marigayi Alhaji Adamu Fika

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya nuna alhininsa dangane da rasuwar tsohon Shugaban Ma’aikatan na Tarayya kuma dan asalin Jihar, Alhaji Adamu Fika.

Marigayin, wanda kuma shi ne Wazirin Fika, ya rasu ne yana da shekara 90 a duniya, bayan ya sha fama da jinya.

Gwamna Buni ya bayyana rasuwar Wazirin na Fika a matsayin babban rashi na kasa, ba wai kawai ga iyalansa, masarautar Fika ko Jihar Yobe kawai ba.

Mai Mala, a cikin wata sanarwa ranar Laraba ya ce, “Hakika mun yi rashin babban shugaba, mai ba da shawara mai hikima, abin alfahari ga jiharmu, kuma mai kishin gaskiya da adalci.

“Rasuwar Alhaji Adamu Fika ta rufe kofar tuntubar gwamnatinmu tare da samar da wani gibi na karbar shawarwari daga ƙwararren ma’aikacin gwamnati,” in ji Gwamna Buni.

Ya kuma ce, “Ina fata, a madadin kaina, gwamnati da kuma al’ummar Jihar Yobe, in yi ta’aziyya ga iyalansa da Masarautar Fika.

“Ina rokon Allah (SWT) Ya gafarta masa kura-kuransa, ya kuma sa ya huta a Aljannatul Firdaus.

“Ina kuma rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya bai wa iyalansa da masarautar Fika kwarin gwiwar jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba,” in ji Gwamnan na Yobe.