Rasuwar Ali Mazrui babban rashi ne ga duniya

A safiyar ranar Litinin da ta gabata ne Allah Ya yi wa fitaccen marubuci Farfesa Ali al-Amin Mazrui rasuwa a birnin New York na kasar Amurka, bayan ya kwashe watanni yana jinya. Kafin rasuwarsa, malami ne a Jami’ar Binghamton da ke Amurka. Kuma ya yi fice ne wajen rubuce-rubuce musamman a kan siyasar duniya da […]

Rasuwar Ali Mazrui babban rashi ne ga duniya
Rasuwar Ali Mazrui babban rashi ne ga duniya

A safiyar ranar Litinin da ta gabata ne Allah Ya yi wa fitaccen marubuci Farfesa Ali al-Amin Mazrui rasuwa a birnin New York na kasar Amurka, bayan ya kwashe watanni yana jinya.

Kafin rasuwarsa, malami ne a Jami’ar Binghamton da ke Amurka. Kuma ya yi fice ne wajen rubuce-rubuce musamman a kan siyasar duniya da kuma addinin Musulunci. An haife Farfesa Mazrui ne a ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 1933 a birnin Mombasa na kasar Kenya.
A sakon ta’aziyarsa Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana bakin cikinsa da rasuwar mamacin, kuma ya ce nahiyar Afirka ce ta yi asarar babbar shehun malaminta. “Wanda kuma ya yi aiki tukuru wajen bunkasa fanin ilimi a nahiyar.” Ya yi kuma fatan Ubangiji ya ba iyalansa da duniya baki daya juriyar jure wannan rashin.
A lokacin daya daga cikin shirye-shiryensa a sashen talabijin na BBC a shekarar 1990, marigayin ya wallafa littattafai a kalla guda 30 akan maudu’ai daban-daban da suka shafi nahiyar Afirka.
Dokta Abubakar danlami Alhassan, malami ne a Jami’ar Bayero ta Kano, wanda kuma ya yi wa marigayin farin sani. A zantawarsa da sashen Hausa na BBC, ya ce “A gaskiya mun yi babban rashi, amma Alhamdulillahi ba ma bakin ciki da rasuwar marigayin saboda ayyukansa na alheri da ya yi za su zama masa sadakatul jariya,”inji shi.
Ya kara da cewa: “Marigayin ya karantar a dukkannin nahiyoyin duniya, ya koyar a nahiyar Austereliya da Afirka da Amurka da kuma Turai. Farfesa Mazrui, mutum ne da ya tabbatar da maganar Hausawa inda suke cewa ‘Ba maraya, sai rago’. Misali yana kammala makarantar sakandare, Allah Ya yi wa mahaifinsa rasuwa, amma hakan bai sa shi ya yi kasa a gwiwa ba, ya himmatu ya samu taimako zuwa Jami’ar Manchester da ke kasar Birtaniya, inda ya yi digiri ya kuma kammala da digiri mai daraja ta daya. Daga nan ya tafi Jami’ar Colombia da ke kasar Amurka, inda ya yi digiri na biyu. Sai kuma digiri na uku wanda ya samu daga Jami’ar Odford da ke Ingila. Daga nan ya fara koyar wa a wata Jami’a da ke kasar Uganda. Kodayake da mulkin marigayi Shugaba Idi Amin ya yi kamar, sai ya yi hijira, ya koma kasar Amurka. Daga can sai kafar yada labarai ta BBC ta gayyace shi, ya rubuta, ya kuma gabatar da shirin ‘The Africans: A Triple Heritage’, wanda ya yi farin jini matuka. Kuma yake nuni da yadda yawancin ’yan Afirka rayuwarsu ta ta’allaka kan abubuwa guda uku: addinin Musulunci, al’adunsu da kuma cudanyansu da Turawa da suka yi masu mulkin mallaka,”inji shi.
Dokta Alhassan ya kuma bayyana dangantakarsa da marigayin, inda ya ce: “Alakata da marigayin ta dalibi ne da malami, na wanda ya karanci ayyukanssa daga bisani ya san shi, ya kuma taimaka mini na tafi karatu zuwa Amurka. Daga nan na san iyalansa. Shi ke nan dai, wannan itace babbar alakar. Marigayin ya fito da nahiyar Afirka a duniya saboda ba wani shiri game da Afirka da aka taba yi a duniya da aka fassara shi zuwa harsuna bila’adadin, aka kuma nuna shi a kasashe kusan 50 kamar wannan shirin nasa na BBC. Duka matsalolin Afirka, hatta wadanda muke fama da su a yau, Farfesa Mazrui ya yi bayaninsu a shirin, ya kuma fadi me ne mafita game da wadannan hali da Afirka take ciki kuma ya nuna cewa Afirka ba wai kasa ce, ko nahiya ce wadda ba ta da mafita ba. Daga nan aka fara karkatowa aka fahimci cewa nahiyar za a iya mayar da ita mai ci gaba, wasu Turawa suma suka karkato san nan wasu shugabannin mu suka fara fahimtar cewa za a iya ciyar da mutane gaba da inganta rayuwar mutane. Da kuma dalibai bila’adadin da ya koyar a Turai, su ne yanzu suke mulki, suke fada a ji. Irinsu Shugaba Barack Obama, kodayake bai karantar da shi kai-tsaye ba, amma ya karanta aikace-aikacensa. Kuma za ka ga a yadda yake hulda da mutanen Afirka yana da fahimtar cewa mu din nan mutanen kwarai ne. Kuma za mu iya yin abin kwari,” inji shi.
Har ila yau, marigayin ya taba zama Uban Jami’ar Aikin Gona da Fasaha ta Jomo Kenyatta da ke kasar Kenya. Hakazalika, akwai dimbin kyaututtukan girmamawa da mukamai masu dama da ya rike lokacin rayuwarsa. Ya rasu yana da shekara 81, ya bar mata daya da ’ya’ya shida. Muna yi masa kyakkyawan fatan ya dace da Aljannar Firdaus.