Rasuwar Arisekola Alao ta girgiza al’umma
Labarin rasuwar Sarkin Musulmin kasar Yarbawa, Aare Musulmi Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao a shekaranjiya Laraba a wani asibiti da ke kasar Switzerland, ta girgiza dubban mutane a birnin Ibadan hedkwatar Jihar Oyo, musamman manyan attajiran da ’yan kasuwa da malaman addini da ma’akatan gwamnati da sauran jama’a. Da yawa daga cikin ’yan kasuwa a […]
Labarin rasuwar Sarkin Musulmin kasar Yarbawa, Aare Musulmi Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao a shekaranjiya Laraba a wani asibiti da ke kasar Switzerland, ta girgiza dubban mutane a birnin Ibadan hedkwatar Jihar Oyo, musamman manyan attajiran da ’yan kasuwa da malaman addini da ma’akatan gwamnati da sauran jama’a.
Da yawa daga cikin ’yan kasuwa a manyan kasuwannin birnin da suka hada da Gbagi da Ogunpa da Agbeni da Aleshinloye da Dugbe, sun rufe shagunansu jim kadan da samun labarin rasuwar, yayin da ma’aikatan gwamnati suka tashi daga ofisoshinsu tun kafin lokacin tashi domin nuna bakin cikinsu da wannan babban rashi.
Limamin Babban Masallacin Ibadan, Sheikh Suara Haruna, ya jagoranci wasu manyan malaman addinin Musulunci zuwa gidan marigayi da ke unguwar Basorun a Ibadan domin fara zaman makoki.
Marigayi Aare Musulmi, Arisekola Alao mai shekara 69, shi ne Musulmi na farko da ya fara zama Sarkin Musulmin kasar Yarbawa da aka tabbatar da nadinsa a 1980.
Kafin rasuwarsa Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao, yana rike da mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar koli ta Addinin Musulunci ta Najeriya. dan kasuwa ne da ya taba kafa kamfanin buga jaridun Monitor a birnin Ibadan.
A ranar 23 ga Mayu ne aka yi wa marigayin gani na karshe a bainar jama’a lokacin da ya halarci bikin bude sabon masallacin Juma’a na Bodija da ke Ibadan wanda Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar ya halarta.
Wakilinmu ya ce, ba za a taba mantawa da gudunmawar da marigayin ya bayar a fannonin ci gaban al’ummar Ibadan da kewaye ba, musamman ta fannin daukar nauyin aikewa da dalibai Musulmi zuwa kasashen duniya domin neman ilimin addini da na zamani da bayar da gudunmawar kudi ga gina masallatai da kanana da manyan makarantun Islamiya.
Akwai wani katafaren masallacin Juma’a da ke kan hanyar Iwo Road a Ibadan da ya gina da kudinsa wanda aka rada wa masallacin suna “Masallacin Arisekola Alao.”
A lokutan azumin Ramadan da karamar Sallah da Babbar Sallah talakawa maza da mata kan yi tururuwa zuwa gidansa domin nema tallafin kayan abinci da dabbobi da kudi domin hidimomin azumi da bukukuwan Sallah.
A cikin sakon ta’aziyya ga iyalai da ’yan uwa da abokan arzikin marigayin, Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya ce ya kadu lokacin da ya samu labarin rasuwar Aare Musulmi Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao, inda ya ce rasuwa ta shafi dukkan Najeriya.
Ya ce marigayin ya rasu ne a daidai lokacin da Najeriya take matukar bakatarsa.