‘Rasuwar Dokta Bawa Abdullahi Wase babban rashi ne ga Najeriya’

Allah Ya yi wa Jakadan Najeriya a kasar katar, Dokta Bawa Abdullahi Wase rasuwa. Jakadan ya rasu ne a ranar Juma’a da ta gabata da karfe 9 na dare a birnin Doha na katar. Shugaba Buhari ne ya nada marigayin Jakadan Najeriya a katar a shekarar 2016. Marigayin mutum ne da ya yi suna wajen […]

‘Rasuwar Dokta Bawa Abdullahi Wase babban rashi ne ga Najeriya’
‘Rasuwar Dokta Bawa Abdullahi Wase babban rashi ne ga Najeriya’

Allah Ya yi wa Jakadan Najeriya a kasar katar, Dokta Bawa Abdullahi Wase rasuwa. Jakadan ya rasu ne a ranar Juma’a da ta gabata da karfe 9 na dare a birnin Doha na katar.

Shugaba Buhari ne ya nada marigayin Jakadan Najeriya a katar a shekarar 2016. Marigayin mutum ne da ya yi suna wajen yin shirhi kan harkokin tsaro a kafofin watsa labarai na Najeriya da kasashen waje.

Dokta Bawa Wase ya yi kokarin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Filato, tun lokacin da aka fara samun rikice-rikice a jihar.

Marigayin ya rasu ya bar matan aure 2 da ’ya’ya 5 kuma an yi jana’izarsa a can katar, a ranar Asabar da ta gabata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna juyayinsa kan rasuwar marigayin, a cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Garba Shehu ya fitar.

Shugaban ya yaba wa marigayin kan gudunmawar da ya bayar, wajen ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Filato.

Ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalansa da gwamnati da al’ummar Jihar Filato.

A lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya a gidan marigayin da ke Jos, Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong, ya bayyana marigayin da dan Jihar Filato nagari, wanda ya rasu a lokacin da jihar take bukatarsa, musamman a wannan lokaci da ake da bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Gwamna Lalong ya mika ta’aziya ga iyalan marigayin da Masarautar Wase da al’ummar Jihar Filato baki daya.

A lokacin ya jagoranci ayarin ’yan Majalisar Dokokin Jihar Filato wajen kai ta’aziyya zuwa gidan marigayin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Joshua Izang Madaki ya ce Majalisar Dokokin Jihar Filato ta yi matukar kaduwa da jin labarin rasuwar wannan babban uba a Jihar Filato da kasa baki daya. Ya ce babu shakka marigayin ya rasu a lokacin da ake bukatarsa.

Don haka ya mika sakon ta’aziyyarsu ga Masarautar Wase da Gwamnan Jihar Filato da al’ummar jihar da Shugaban kasa kan wannan rashi da aka yi, wanda ya shafi Najeriya ne baki daya.

dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Barikin Ladi da Riyom, Istafanus Dung Gyang ya ce marigayin mutum ne mai fadar ra’ayinsa a kowanne abu da aka kawo. “Marigayin ya ba da gudunmawa wajen kawo zaman lafiya a Jihar Filato.  Mutum ne mai kishin kasa. Najeriya ta amfana da shi a wurare da dama.”

Ita ma Majalisar Malamai ta Jihar Filato, a wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hannun Mataimakin Sakataren Majalisar, Malam Ahmad Muhammad Ashiru, ta nuna juyayi da alhininta kan rasuwar marigayin.

Sanarwar ta ce, Shugaban Majalisar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir da dukan ’yan majalisar sun kadu da wannan babban rashi da aka yi. Don haka majalisar ta mika sakon ta’aziyyarta ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong da Masarautar Wase da iyalan marigayin kan wannan rashi da aka yi.

Galadiman Wase Alhaji Mustafa Umar cewa ya yi marigayin ya tafiyar da ga baki dayan rayuwarsa wajen taimaka wa al’umma, musamman wajen gina zaman lafiya. Ya ce marigayin ya halarci babban taron zaman lafiyar da aka gudanar a Jihar Filato a shekarar 2004, inda ya bayar gagarumar gudunmawa wajen ganin an samu zaman lafiya a jihar, bayan da aka samu rikice-rikice a lokacin.

Har ila yau ya ce wannan bawan Allah ya tafiyar da rayuwa mai sauki a lokacin rayuwarsa, kuma mutum ne mai biyayya da natsuwa.

Wani mai taimaka wa marigayin na musamman, Salisu Muhammad Wase, cewa ya yi a gaskiya an yi wa Jihar Filato da kasa baki daya babban rashi. Ya ce marigayin mutum ne da yake tsaye a kan dukan al’amuransa na rayuwa. Idan ya ce zai yi abu zai yi, idan ya ce ba zai yi abu ba, ba zai yi ba. Kuma shi mutum ne da ba ya da abokin fada.

daya daga cikin ’ya’yan marigayin, Usman Bawa Abdullahi Wase, cewa ya yi marigayin mutum ne wanda bai taba ganin irinsa ba. “Idan na kira shi mahaifi, ina ganin na yi kaskanci wajen misalta shi, domin shi uba ne ba ga mu kadai ba, shi uba ne ga al’umma baki daya. Don haka muna yi masa addu’ar Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa kura-kurensa.”