Rasuwar Inunu babban rashi ne ga duniya baki daya

Da daren Juma’ar makon jiya ne, Allah Ya jarabce mu da babban rashin Shugaban kungiyar Zabi Sonka ta kasa da kuma Nahiyarmu ta Afirka, Alhaji Inunu Mai Dankalin Turawa, wanda ya rasu bayan  ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.Mutuwar tasa ta girgiza jama’a matuka, musamman ma ganin jinyar kwanaki biyu kawai ya yi yana […]

Rasuwar Inunu babban rashi ne ga duniya baki daya

Da daren Juma’ar makon jiya ne, Allah Ya jarabce mu da babban rashin Shugaban kungiyar Zabi Sonka ta kasa da kuma Nahiyarmu ta Afirka, Alhaji Inunu Mai Dankalin Turawa, wanda ya rasu bayan  ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Mutuwar tasa ta girgiza jama’a matuka, musamman ma ganin jinyar kwanaki biyu kawai ya yi yana fama da ciwon amai-da-gudawa kafin ya rasuwarsa ranar Alhamis a Asibitin Musulmi da ke Tudun Wada, Kaduna da misalin karfe 10:00 na dare.
Wadanda suka san Alhaji Inunu suna cigaba da bayyana shi da mutum mai son jama’a da saukin kai da kuma aiki tukuru, lamarin da ya sa sunansa ya karade ciki da wajen Najeriya cikin kankanen lokaci da kuma harkokin zabi sonka da ya shafe shekaru da dama yana yi.
Shugaban Inunu, kamar yadda aka fi saninsa, mutum ne mai kyauta da cika alkawari da kuma tausaya wa na kasa da shi. Wadanda Allah Ya albarkace su da yin mu’amala da shi a lokacin da yake raye, shaidu ne kan haka.
Babu shakka jan aiki ne da jajircewa kan kawo irin wannan kyakkyawan yabo. Marigayin daya ne daga cikin mutane kalilan da suka siffantu da halayen kwarai. Ya sha gwagwarmaya a matakai daban-daban, a lokuta daban-daban ba tare da gajiyawa ba. Ya yi sana’o’i da dama,  kamar su sana’ar goro da kayan gwanjo, kafin ya tsaya kan sana’o’i biyu da jama’a suka fi saninsa da su wato dankalin Turawa da kuma zabi sonka.
An haifi marigayi Alhaji Inunu Mai Dankalin Turawa a garin Garko da ke Jihar Kano kimanin shekaru 80 da suka wuce, amma ya taso ne a garin Jos. A shekarar 1958 ya koma Kaduna, inda a nan ne ya fara sana’ar dankalin Turawa a babbar kasuwar Kaduna.
Kafin rasuwar tasa, marigayin ya yi fice ne a ciki da wajen kasar nan a harkar zabi sonka, inda albarkacin hakan ya ziyarci kasashe da dama ciki har da kasar Jamus da Ingila da kuma China.
A gaskiya shi abokin kowa ne, musamman ma masu aikin yada labarai, dalilin da za a dade ana tunawa da shi. Bugu da kari ga kuma gagarumar gudunmuwar da ya ba da a bangaren zabi sonka da kuma kokarinsa na ganin an kakkafa kungiyoyin ci gaban al’umma. Na tabbata ko wadansunmu sun manta, tarihi kansa ba zai manta da shi ba.
 daya daga cikin ’ya’yansa Muhammadu Nazifi (Sabo Yaro) ya  bayyana  mahaifin nasu ne da uba, wanda kowane da zai so ya yi alfahari da shi saboda irin nasasorin da ya cimma a rayuwarsa. Ya kuma ce shi mai ja n’ya’yansa ne a jika, abin da ya kara sa marigayin soyuwa sosai a gare su.
Alhaji Bala Kiyales ya bayyana yadda mutuwar tasa ta haifar da babban gibi kasancewarsa daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar zabi sonka na kasar nan. Kuma ya yi fatan Allah Ya rahamshe shi.
A ta’aziyyarsa kan rasuwar, Shugaban Gidajen Rediyon Tarayya (FRCN), Alhaji Ladan Salihu ya ce ya girgiza matuka da samun labarin mutuwar mamacin inda ya bayyana  hakan da wani babban rashi, wanda bai tsaya ga kungiyoyin zabi sonka ba kawai, amma ga kasa da ma duniya baki daya. Ya kuma yi fatan Allah Ya jikan mamacin da rahama da kuma fatan Allah Ya ba iyalinsa da jama’a baki daya hakurin jure wanan babban rashin.
Shi ma Shugaban Gidan Rediyon Nagarta, Alhaji Yusuf Saulawa ya halarci gidan mamacin da ke Titin Gwarzo inda ya yi fatan Allah Ya jikan mamacin da rahama. Ya kuma bayyyana shi da mutumin kirki mai son ci gaban al’’umma.
Haka dai iyalan mamacin suke ci gaba da karbar ta’aziyya ba dare, ba rana, daga kungiyoyin Zabi Sonka da kungiyoyi Masu Zaman Kansu da kungiyoyin ’Yan Kasuwa da Jami’an Gwamnati da dai sauran ’yan uwa da abokan arziki na nesa, da na kusa.
Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya biyar da kuma jikoki 22. Muna yi masa kyakkyawan fatan ya dace da Aljannar Firdaus, kuma Allah Ya ba mu hakurin jure wannan babban rashin. Amin.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50