Rasuwar Lawal Kaita: Najeriya ta yi babban rashi

A ranar Talatar da ta gabata ne Allah Ya yi wa tsohon Gwamnan tsohuwar Jahar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita rasuwa a yammacin ranar a asibitin Turkish dake Abuja bayan doguwar jinya da ya yi fama da ita, kamar yadda iyalansa suka shaida.    Dattijon mai shekaru 85 ya yi suna a fagen siyasar Najeriya wanda […]

Rasuwar Lawal Kaita: Najeriya ta yi babban rashi

A ranar Talatar da ta gabata ne Allah Ya yi wa tsohon Gwamnan tsohuwar Jahar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita rasuwa a yammacin ranar a asibitin Turkish dake Abuja bayan doguwar jinya da ya yi fama da ita, kamar yadda iyalansa suka shaida. 

 

Dattijon mai shekaru 85 ya yi suna a fagen siyasar Najeriya wanda har ake yi wa kirari da ‘Kakan Siyasa’. Alhaji Lawal Kaita bai dade da hawa kujerar Gwamnan Jahar Kaduna a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula a shekarar 1983. 

 

Ya taba rike mukamin Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ta Jahar Kaduna a shekarar 1977. Sannan daga bisa ya shiga harkokin siyasa, inda ya zama dan Majalisar Dokoki a shekarar 1977 zuwa 1978. Daga bisani kuma ya zama mai taimakawa shugaban kasa na musamman daga 1980 zuwa 1982. Ya fara takarar neman kujerar gwamnan Jihar Kaduna a 1979, inda ya fadi zabe a karkashin Jam’iyyar NPN, inda Alhaji Balarabe Musa na Jam’iyyar PRP ya dare kujerar, wanda kuma rashin nasarar ce da ya yi shugaban kasa Shehu Shagari ya nada shi wakilin shugaban kasa a ofishin tuntuba dake Kano. 

 

Bayan wancan matsayi ne ya sake shiga takarar Gwamnan na Jahar Kaduna kuma Allah Y aba shi nasara ya lashe zaben, daga bisani aka yi masu wancan juyin mulkin. Har’ila yau, Alhaji Lawal Kaita na daga cikin tsatson gidan sarautar sullubawa dake Katsina, wanda har ya nemi takarar kujerar masarautar bayan mutuwar sarkin Katsina, Alhaji Muhammadu Kabir Usman. 

 

Kazalika, kafin rasuwarsa shi ne shugaba na din-din-din na kungiyar wasan Polo na Katsina, bayan rikon kwarya na kungiyar ta kasa da ya yi. Yana daga cikin wadanda suka yi kokarin kai wasan Polon a gwamnatin tarayya domin ganin cewa wasan Polon ya shiga cikin sahun wasannin da za a rika baiwa muhimmanci a gwamnatance. An kuma samu nasara a bisa wancan yunkuri nasa, inda kungiyar ta koma NPF (Nigeiria Polo Federation) daga NPA (Nigeiria Polo Association).

Marigayi Alhaji Lawal Kaita ya bayar da gudunmuwa ta wajen ganin arewacin na Najeriya na rike da matsayinsa ta fuskar siyasa da kuma shugabanci. An san shi bisa kalubalantar duk wani abin da ya san zai taba arewa, yana daga cikin wadanda suka kafa jam’iyar PDP a 1998, kana daga bisani ya bar ta ya koma Jam’iyyar AC a 2006. Kazalika mutun ne na kowa wanda abin duniya bai rude shi ba, domin yana bayar da dukiyarsa ga mabukata da kuma abin da ya shafi addini. An yi ta yada jita-jitar mutuwarsa a kwanakin baya ta kafofin sadarwar zamani. Alhaji Lawal Kaita ya rasu yana da shekaru 85 ya bar mata daya da ‘ya’ya takwas a duniya, sannan an yi jana’izarsa a ranar Laraba kamar yadda Addinin Musulunci ya tsara.