‘Rasuwar Malam Habibu babura babban rashi ne ga duniyar Hausa’
A ranar Talatar da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitaccen masanin Hausar nan Dokta Habibu Sani babura wanda aka fi sani da ‘Baba Habibu’ rasuwa bayan ya yi fama da jinya na mako daya, inda ya kwanta a Asibitin Malam Aminu Kano. Kafin rasuwarsa Malam Habibu Sani babura (Talban babura), malami ne a […]

A ranar Talatar da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitaccen masanin Hausar nan Dokta Habibu Sani babura wanda aka fi sani da ‘Baba Habibu’ rasuwa bayan ya yi fama da jinya na mako daya, inda ya kwanta a Asibitin Malam Aminu Kano.
Kafin rasuwarsa Malam Habibu Sani babura (Talban babura), malami ne a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero Kano, duk da cewa ya yi ritaya a watan Disamban bara.
Marigayin ya yi karatun firamare a Makarantar Firamare da ke garin babura daga 1960 zuwa 1967. Bayan ya kammala sai ya tafi Kwalejin Gwamnati ta Kano, wacce ake kira da Kwalejin Rumfa a yanzu. Bayan ya kammala a 1973 sai ya tafi Jami’ar Abdullahi Bayero Kano, wacce ta rikide zuwa Jami’ar Bayero. Ya yi karatu a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya a jami’ar, inda ya kammala a 1977.
A1978 ne ya yi hidimar kasa a Jihar Borno, inda ya koyar a makarantun gaba da sakandare. Bayan ya kammala hidimar kasa ce ya samu aikin koyarwa a Jami’ar Bayero, inda aka dauke shi a matsayin mataimakin malami a Sahen Koyar da Harsunan Najeriya.
A 1981 marigayin ya koma karatu don samun digiri na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Sai dai wannan abu bai kai ga samuwa ba domin a 1982 ya hadu da hadari a daidia kofar Kabuga da ke kusa da Jami’ar Bayero, lokacin da yake kokarin zuwa gidansa da ke cikin harabar tsohuwar Jami’ar Bayero. Tun daga wannan hadari ne marigayin ya gamu da cutar laka, inda ya kare rayuwarsa a kan keken guragu.
Malam Habibu babura kwararen malami ne a bangarori uku na nazarin harshe da suka hada da Kimiyyar Harshen Hausa da Adabi da kuma Al’adu.
Dokta Ibrahim Garba Satatima shi ne Shugaban Sashen Koyar da Harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero, ya bayyana cewa ba wai Jami’ar Bayero ko Sashen Hausa ne kadai ya yi rashi ba, harshen Hausa da al’adunsa ne suka tafi. “Marigayi Malam Habibu, wanda ni kaina malamina ne, mun san irin kwazo da sani da yake da shi a kan wannan harshe. Mutanen da ke saurarensa a kafafen watsa labarai za su san haka, domin babu banagren da bai yi fice ba. Idan ka dauko harshen Hausa kansa, sai ka ce a nan ya fi kwarewa, haka idan aka koma bangaren al’ada. Babu shakka rasuwarsa rashi ne ga dukan Hausawa da duk wani mai magana da harshen Hausa, musamamn wadanda suke burin ganin bunkasar harshen,” inji shi.
Shi ma makusancinsa a cikin abokan aikinsa a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya a Jami’ar Bayero, Farfesa Aliyu Mu’azu ya bayyana marigayin a matsayin magani a kan kowace irin matsala. “Bayan kasancewrsa hazikin malami wanda bai yarda da nakasa ba, domin a kullum shi bai taba yarda nakasar da yake da ita ta hana shi yin abubuwa na neman ilimi da zumunci da sauransu ba. Sannan ni ina yi masa take da maganin kowace matsala, domin duk irin matsalar da ka je wa Baba Habibu, to insha Allahu zai warware maka ita.”
Har ila yau Farfesa Aliyu Mu’azu ya bayyana rashin Malam Habibu a matsayin gibi na biyu da Sashen Koyar da Harshen Hausa ya yi a kwanan nan, domin a kwanakin baya ma sashen ya rasa Farfesa Mu’azu Sani Zariya.