Rasuwar Sardauna: Ba a rabu da Bukar ba
Yau Juma’a ne cikan shekaru 50 da ‘yan kudu, musamman ma mutanen shiyyar Kudu-maso Gabas, suka fitar da maitarsu a fili, suka dakile Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato daga doron kasa, wanda ya kasance daya daga cikin firimiyoyin jihohi guda hudu da ke fadin tarayyar Najeriya. A rana guda aka kashe shi tare da Firayim […]
Yau Juma’a ne cikan shekaru 50 da ‘yan kudu, musamman ma mutanen shiyyar Kudu-maso Gabas, suka fitar da maitarsu a fili, suka dakile Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato daga doron kasa, wanda ya kasance daya daga cikin firimiyoyin jihohi guda hudu da ke fadin tarayyar Najeriya. A rana guda aka kashe shi tare da Firayim Minista, kuma shugaban gwamnatin tarayyar Najeriya, Sa Abubakar Tafawa |alewa da mininsa, takwaransa na Jihar Yamma, Cif Samyuel Ladoke Akintola. Hakan kuwa ya faru ne sakamakon siyasar bakar gaba da kiyayya da daukacin ‘yan siyasar kudancin kasar nan suka nuna wa ‘yan Arewar da suke kukan cewa, sun hana su rawar gaban hantsi a fanin mulki, sun kuma hana rowan su gudu a fagen siyasa a wancan lokacin.
Ba wani abu ne ya kai ga haka ba kuwa, illa tsabar hassada da ganin kyashin Arewa, wacce kwarewar shugabanninta bisa mulki da kuma gwanancewarsu wajen shimfida adalci da tsananin kamanta gaskiya suka bambanta jihar da sauran takwarorinta guda uku. Wadannan ne halayen da suka inganta matsayin Arewa cikin dan kankanen lokaci, har ta yi kunnen doki da jihohin kudancin da suka yi mata fintinkau a dukkan fannonin raya kasa; kuma a bisan su ne magabatan farko, kamar su Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa |alewa da Malam Aminu Kano, suka aza harsashin gina Najeriya.
Da ma an ce wanda duk ya riga ka barci zai riga ka tashi. To mutanen kudanci sun tsere wa ‘yan Arewa da shekaru fiye da 70 a fannonin zamani, tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka kasar nan. Shi ya sa suke ganin cewa Jihar Arewa ba komai ba ce, domin jama’arta ba su da ilmi kamar takwarorinsu da ke jihohin Gabas da Yamma, saboda haka nan tilas ne su kasance kaskantattun da za a rika ja tamkar dabbobin da za a kai mayanka.
To, amma ba hakan al’amura suka kasance ba. Jihar Arewar da suka dauka gajerar kuka ce mai saukin hawa sai ga shi ta gagare su tankwarawa; ta buwaya a fagen siyasa da difulomasiyya; ta zame ‘yar lelen Turawan da suka fahimci cewa, ita ce kadai za ta iya tsara kyakkyawar manufar da za ta kai ga samun ‘yancin kasar cikin lumana da kwanciyar hankali; sa’annan kuma ita ce ke da halaye da kamilallun shugabannin da za su ririta ‘yancin da za a samu don kai wa ga ci gaba mai ma’ana, kuma cikin hanzari. To, tun kafin samun ‘yanci likkafar ‘yan Arewa da jam’iyyarsu ta NPC ke ta yin gaba-gaba, kamar kwaryar roro, aka kuma samu sukunin sassaka su bisa muhimman mukamai a gwamnatin tarayya, suka kuma zamanto zakakurai a majalisar wakilai, sai yadda suke so za a gudanar da al’amuran gwamnati don nakaltar da suka yi wa siyasa da yadda ake sarrafa ta don biyan bukatar ‘yan Arewar da ke da rinjaye a cikin majalisar.
Kafin samun ‘yanci, ‘yan kudu sun mamaye Arewa; su ne ke rike da muhimman mukamai a kamfanonin kasuwanci da manyan ma’aikatun gwamnatin Arewa, abin da ya kai sai da Sardauna Ahmadu Bello ya bullo da wata manufa ta danka ragamar jan Arewa a hannun ‘yan Arewa, wacce ake kira Northernisation Policy, don a tabbatar cewa, kafin samun ‘yanci ‘yan Arewa ne ke sarrafa al’amuransu da kansu, ba ‘yan kudun da ke masu danniya. Wannan abu bai yi wa mutanen Jihar Gabashin Najeriya dadi ba, domin kuwa su ne manufar ta fi shafa, saboda a lokacin hatta masu wanke gyambo a asibitocin gruruwa da kauyukan Arewa, ba ma akawunnai da manyan jami’an gwamnati ba, duk mutanen can ne.
Ko a fannin siyasa ‘yan kudu sun kasa yin galba akan ‘yan Arewa, domin ta yadda duk aka kada, aka kuma raya, ‘yan Arewar ne dai ke yin galba wajen kafa gwamnatin tarayya, su ne kuma ke bisa sauran al’amurra, kaman alu-ja. ‘Yan kudun sun nemi yin kawance da wasu ‘yan siyasar jihar Arewa don a rarraba kan ‘yan’yanta, amma hakan bai ba sa hakarsu ta cimma ruwa ba game da hankoronsu na ganin an karkasa Jihar Arewa gida-gida don su ji dadin farraka jama’anta. daukacin al’ummomin Arewa, sarakunansu da talakawansu duk sun nuna cikakken goyon baya da biyayya ga Sardauna Ahmadu Bello wanda ya kare masu mutunci, ya daukaka matsayinsu, sa’anan kuma ya hade kawunan kabilun Arewa sama da 250 wuri guda.
Sardauna Ahmadu ya hana ‘yan kudu kurdowa don karfafa rikice-rikicen addini da suka fara haddasawa a yankin a zamaninsa don wargaza hadin kan Arewa, sa’annan ya wanzar da muhimman ayyukan ci gaba, kwatankwacin wadanda jihohin Gabas da ta Yamma ke tinkaho sun yi a yankunansu, fiye ma da yadda suka tsara nasu.
A takaice dai Sardauna ya mayar da yankin Arewa abar sha’awa; abar kwaikwayo; wurin zaman lumana da karuwar arziki; inda ‘yan kudu suka yi ta tuttudowa, suna cin arziki ba tare da kyara ko wata tsangwama ba. Amma wannan bai sa sun gode Allah, sun hadiye bakar gabar da suke nunawa al’ummar da suke amfana da ita ba.
Rashin samun damar da ‘yan Kudu ba su yi ne ba don mamaye Arewa ya haddasa bakar kiyayyar mutanen Arewa a zukatansu, har hakan ya yi sanadiyyar kisan gillar da suka yi wa Sa Ahmadu Bello, da Mataimakinsa a siyasance, kuma Shugaban gwamnatin tarayya, Sa Abubakar Tafawa balewa da amininsu na siyasa, Clief Samuel Ladoke Akintola, Firemiyar Jihar Yamma da Festus Okotie-Eboh don dai a kawo karshen mulkin ‘yan Arewa da makararrabansu na Kudu a Najeriya. Wannan manufa ta yi sanadiyyar yakin basasar da ya jawo hasarar miliyoyin rayukan ‘yan Najeriya a banza, a wofi.
Mutanen yankin Gabas na nan kan bakarsu, suna ci gaba da rura wutar kiyayya da haddasa rikice-rikicen bambancin addini da na kabilanci a kasar, ba don komai ba kuwa, sai don su kassara Arewa ne, su kuma hana ‘ya’yanta rawar gaban hantsi a wannan marrar.
A lokutan da shugabannin siyasar Arewa suka yi ta kakkafa gwamnatocin tarayya tare da su ake tafiya, amma suka yi ta kwashe musu kafa, har ta kai sai da suka kassara su. A yanzu kuma bayan Yarbawa sun gane wautarsu ta kin tafiya da ‘yan Arewa tun can fil-azal, sun komo sun hade tare, hakan kuma ya bayar da damar kafa kwakkwarar jam’iyyar da ta kwace gwamnatinsu ta kabilanci, sun ki hada kai, suna neman su yi sanadiyyar wargajewar kasar, idan suka balle daga cikinta. Watau dai har yanzu suna nan kan bakarsu ta kirkiro tyasu kasar ta dabam, watau Biafra. ba a rabu da Bukar ba, an haifi Abu.