Rasuwar Sarkin Biu rashi ne ga Najeriya – Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar Sarkin Biu, Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu a matsayin babban rashi ga al’ummar masarautarsa da jihar Borno da Najeriya baki daya. Shugaban Kasar ya bayyana haka ne a sakonsa na ta’aziyya da ya aike ga gwamnati da al’ummar jihar Borno da kuma masarautar Biu da iyalan marigayi Sarkin, […]
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar Sarkin Biu, Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu a matsayin babban rashi ga al’ummar masarautarsa da jihar Borno da Najeriya baki daya.
Shugaban Kasar ya bayyana haka ne a sakonsa na ta’aziyya da ya aike ga gwamnati da al’ummar jihar Borno da kuma masarautar Biu da iyalan marigayi Sarkin, inda ya yabi marigayin kan yadda ya jagoranci jama’arsa cikin natsuwa da sadaukarwa a shekara 31 da ya yi a kan gado na sarauta.
- Takaitaccen tarihin Sarkin Biu Marigayi Mustapha Aliyu
- An kama limamai 2 bisa zargin yi wa ’yar bautar kasa fyade
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Mista Femi Adesina ya fitar ta ce, Shugaban kasar ya bayyana marigayi Sarkin a matsayin mutum mai son zaman lafiya da son ci gaban kasa da jama’arsa da kuma hangen nesa wanda ya yi kokarin zamanantar da garin Biu ta hanyar mara baya ga kafa manyan makarantu a yankin.
Shugaban kasar ya yi nuni da cewa tsarin da Sarkin ya yi amfani da shi wajen gudanar da mulkinsa a tsawon lokacin da ya shafe a gadon sarauta, ya sanya ya samu amincewa da girmamawa daga al’ummarsa, a lokaci guda kuma da wurin sauran ’yan Najeriya da suka fito daga bangarori daban-daban.
Shugaba Buhari ya ce ya na da yakinin ayyuka masu kyau da Sarkin ya gudanar a yayin rayuwarsa za su zamo abin tunawa a Biu da Jihar Borno da sauran sassan Arewa maso Gabas da kuma Najeriya baki daya.
Ya yi addu’ar Allah Madaukaki Ya jikansa kuma Ya ba mutanen Masarautar Biu da iyalansa da gwamnati da al’ummar Jihar Borno hakurin jure wannan babban rashi.
A ranar Litinin da ta gabata da dare ne marigayi Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu ya rasu a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe bayan gajeriyar jinya.