Rasuwar Sarkin Damaturu Na Farko A Saudiya
Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri, Sarkin Damaturu na Farko, ya rasu a Saudiyya, yana da shekaru 82 a duniya
A ranar Lahadi Allah Ya yi wa Sarkin Damaturu na farko, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri, rasuwa sakamakon fama da lafiya a kasar Saudiyya.
Ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, ya bar ’ya’ya da matarsa kamar yadda dan n uwansa Mai Aliyu Usman Biriri ya bayyana wa Aminiya.
Shi dai Marigayi Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri an nada shi a matsayin Sarkin Damaturu a zamanin Marigayi gwamna Sanata Bukar Abba Ibrahim a watan Agusta 1993.
A cikin kankanin lokaci da aka samu juyin mulkin soja sai gwamnatin soja ta tsige shi a watan Janairun 1995, kasa da shekaru biyu da hawansa karagar sarautar ta Damaturu.
- Yadda ’yar shekara 11 ta rasu bayan malami ya yi mata fyade
- NAJERIYA A YAU: Matakan Kauce Wa Yaɗuwar Cutuka A Makarantu Saboda Tsananin Zafi
Kafin zamansa sarki, Alhaji Biriri ya rike mukamai da dama, ciki har da kwamishinan kudi a shekarar 1984 a tsohuwar jihar Borno.
Ya kuma taka rawar gani wajen jagorantar musanya kudin da gwamnatin mulkin soja ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi a shekarar 1984.
Bugu da kari, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri ya taba rike mukamin Manajan Daraktan Hukumar samar da takardun kudi ta kasa.
Ya kuma rike Kwamishinan Hukumar kidaya ta kasa mai kula da Jiharsa ta Yobe da sauran mukamai.
Tunin dai aka yi jana’izarsa a Masallacin Harami da ke Makkaha kasar Saudiyya.