Kisan Sarkin Gobir: Abin da Tinubu ya ce a saƙon ta’aziyya

’Yan ta’adda sun kashe sarkin mai shekaru 72 wanda ya haura shekaru 40 a kan mulki duk da cewa ana shirin kai musu kuɗin fansa

Kisan Sarkin Gobir: Abin da Tinubu ya ce a saƙon ta’aziyya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya mika ta’aziyyarsa kan rasuwar Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa, wanda ’yan bindiga suka yi wa kisan gilla.

A ranar Laraba ne Masarautar Gobir ta tabbatar da rasuwar sarkin mai shekara 72, wanda ya yi fiye da shekara 40 yana sarauta, a hannun masu garkuwa da shi.

A saƙon Tinubu ga iyalansa da Masarautar Gobir da Gwamnatin Sakkwato da Fadar Sarkin Musulmi, ya bayyana kaɗuwa da kisan wulaƙanci da aka yi wa basaraken, yana mai rokon Allah Ya yi masa rahama.

Sakon da ke ɗauke da sa hannun kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya ba ’yan Najeriya tabbacin cewa Gwamnatin Tinubu “tana aiwatar da kwararan matakai domin tabbatar da tsaro da kuma muttsike waɗannan ’yan ta’adda.”

A makonnin da suka gabata ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da basaraken tare da dansa da wani dan uwansa a yankin Kwanar Maharba da ke Jihar Sakkwo, hanyarsu ta dawowa daga wani aiki.

Daga bisani masu garkuwa da shi suka saki bidiyo yadda suke azabtar da shi da kuma wulakantawa.

An kuma ga bidiyon yadda suka daure shi, inda a ciki  yake neman Gwamnatin Jihar Sakkwato ta biya su kudin fansa da suka buƙata, in ba haka ba za su hallaka shi idan wa’adin ya cika ba a biya ba.

Marigayi Alhaji Isa Muhammad Bawa shi ne Hakimin Gatawa a yankin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato.

Ƙanen sarkin, Ibrahim S. Gobir, wanda kuma shi ne yake tattaunawa da ’yan bindigar domin a sake shi, ya bayyana cewa masu garkuwa da sarkin sun kashe shi ne duk da cewa an tattara kuɗin fansa da ya kai Naira miliyan 60 domin tura musu.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin mai shekara 72, wanda ya yi fiye da shekara 40 yana sarauta, tare da ɗansa da kuma wani ɗan’uwansa.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos