‘Rasuwar Sarkin Misau rashi ne ga kasa’
Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Mohammed Abdullahi Abubakar da Shugaban Majalisar Wakilai ta kasa Barista Yakubu Dogara sun bayyana rasuwar Mai martaba Sarkin Misau Alhaji Muhammadu Manga na III a matsayin babban rashi ga kasar nan.Shugabannin biyu sun bayyana haka ne a sakonnin ta’aziyyarsu da suka gabatar ga al’ummar Masarautar Misau da gwamnati da jama’ar Jihar […]
Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Mohammed Abdullahi Abubakar da Shugaban Majalisar Wakilai ta kasa Barista Yakubu Dogara sun bayyana rasuwar Mai martaba Sarkin Misau Alhaji Muhammadu Manga na III a matsayin babban rashi ga kasar nan.
Shugabannin biyu sun bayyana haka ne a sakonnin ta’aziyyarsu da suka gabatar ga al’ummar Masarautar Misau da gwamnati da jama’ar Jihar Bauchi a lokuta daban-daban.
Gwamna Mohammed Abubakar, a ta’zaiyyarsa ga al’ummar jihar bayan kammala jana’izar marigayi Sarkin a garin Misau ya ce Jihar Bauchi da kasar nan sun yi rashin babban dattijo mai fada a ji, inda ya roki Allah Ya gafarta wa Sarkin.
Shi kuwa Barista Yakubu Dogara a sakon da ya aike ta hannun Kakakinsa Turaki A. Hassan ya bayyana marigayi Sarki Muhammadu Manga a matsayin uba ga jama’a kuma daya daga cikin shugabannin da ake bukatar a kasar nan. Dogara ya ce rashin Sarkin ban a al’ummar masarautar Misau ko Jihar Bauchi kadai ba ne, rashi ne na daukacin al’ummar Najeriya, inda ya yi fatar samun rahamar Allah ga Sarkin.
A ranar Litinin da ta gabata ne Allah wa Mai martaba Sarkin Misau Alhaji Muhammadu Manga na III rasuwa bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Shugaban riko na karamar Hukumar Misau, Alhaji Ado Aska ya tabbatar wa Aminiya da rasuwar Sarkin.
Babban Limamin Misau Alhji Usman Baba ne ya jagoranci sallar janaza da aka yi wa marigayin a kofar Fadar Misau.
Manyan mutanen da suka halarci jana’izarsa sun hada da wakilan Majalisar Dokoki ta kasa da suka hada da sanatoci biyar a karkashin jagorancin Sanata Muhammad danjuma Goje, sai tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Alhaji Mahmud Yayale Ahmed da sarakuna 10.
An haifi marigayi Muhammadu Manga 1937, kuma ya yi makarantar firamare a Makarantar Santaral da ke Misau tare da halartar kwasa-kwasai a ciki da wajen Najeriya ciki har da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya yi karatu a sashin harkokin mulki na jami’ar.
Sarkin ya rasu ya bar mata hudu da ’ya’ya 27.