Rasuwar Sheikh Babantine babban rashi ne ga al’umma – Sheikh Rigachikun

A ranan Litinin da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Usman Abubakar Babantine rasuwa. Ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya ta tsawon wata daya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya. Kafin rasuwarsa, Sheikh Babantine shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a […]

Rasuwar Sheikh Babantine babban rashi ne ga al’umma – Sheikh Rigachikun
Rasuwar Sheikh Babantine babban rashi ne ga al’umma – Sheikh Rigachikun

A ranan Litinin da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Usman Abubakar Babantine rasuwa.

Ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya ta tsawon wata daya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya.

Kafin rasuwarsa, Sheikh Babantine shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a na Matatar Mai ta Kaduna, kuma shi ne Shugaban Majalisar Limamai da Malamai ta Jihar Kaduna. Marigayin shi ne kuma magajin Malam Abubakar Mahmod Gumi wajen karantar da littafi Mukhtasar Khalil a Masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna. 

Marigayin ya yi gwagwarmaya wajan yada addinin Musulunci, kamar yadda daya daga cikin malaman da suka gudanar da aikin da’awa tare, Sheikh Yusuf Sambo Rigacikum ya bayyana, bayan gabatar da addu’arsa a wajen jana’izar marigayin.

“Babu shakka an yi babban rashi ba a garin Zariya kadai ba, kai har ma a Najeriya, domin  malami ne mai himma da kokari wajen karantar da al’umma da kuma rubuce-rubuce. Bayan rasuwar babban malamimmu Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, marigayin ne ya dauki ragamar ci gaba da karantar da littafin Mukhtasar Khalil a kan kujerar da marigayi Sheikh Abubakar Gumi yake karantarwa, kuma har zuwa lokacin da ya koma zuwa ga Allah, bai bar karantar da wannan darasi ba. Kuma Malam Babantine ya rubuta littafi a kan Zakkah kuma ya yi rubuce rubuce daban-daban wadanda aka buga su, aka fitar da su kuma yana daya daga cikin shugabannin matasan kungiyar Jama’atu Nasril Islam. Yana daga cikin wadanda suka yi wa Sunnah hidima a kasar nan baki daya,” inji Sheikh Yusuf Sambo.

Ya ci gaba da cewa “Don haka mun yi babban rashi na rasuwar babban malami Babantine. Muna fata Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa. Kuma babban abin da za a rika tunawa da marigayin shi ne, tsayuwa wajen karantar da al’umma da dagewa  wajen tsai da Sunnah. Kuma a duk lokacin da wata matsala ta taso a kokarin warware abin da Annabi Muhammadu (SAW) ya tafi a kansa, Usman Babantine shi ne kan gaba wajen da za a kalubalanci wadannan abubuwa.”

“Ba na mantawa da wadansu suka taso da wani rudani na neman raba mutane da bin tafarkin magabata a nan Kaduna, suna ta soke-soken littattafan fikihu, suna sukar su Imamu Buhari da Muslim da sauransu, Sheikh Usman shi ne ya jagoranci wa’azi a kan wannan a cikin gari da duk inda ya kamata a je a yi wa’azi, domin karantar da al’umma a kan su yi watsi da bin su, duk babu lungun da ba mu shiga da shi ba, domin wa’azi,” inji shi.

Marigayi, kafin rasuwarsa ya wallafa littattafai wadanda ake amfani da su a duniyar Musulunci a yau guda 21 kuma ya rasu yana da mata hudu da ’ya’ya 21. Ya rasu yana da shekara 75 a duniya.