Rasuwar wani ta kawo takaddama a Kano
Rasuwar wani magidanci mai matsakaicin shekaru, Alhaji Dauda Musa dankaka da wasu ’yan bindiga suka kashe a Unguwar Shagari Kwatas ta haifar da takaddama a yayin da ’yan kabilarsa suka bukaci su dauki gawarsa zuwa garinsu don su yi masa jana’iza, amma mutanen unguwar suka ki amincewa, gudun kada a yi masa wata jana’iza daban, […]

Rasuwar wani magidanci mai matsakaicin shekaru, Alhaji Dauda Musa dankaka da wasu ’yan bindiga suka kashe a Unguwar Shagari Kwatas ta haifar da takaddama a yayin da ’yan kabilarsa suka bukaci su dauki gawarsa zuwa garinsu don su yi masa jana’iza, amma mutanen unguwar suka ki amincewa, gudun kada a yi masa wata jana’iza daban, alhali shi Musulmi ne.
Said a ’yan Hisbah da ’yan sanda suka sanya baki kafin a cimma yarjejeniyar yi masa jana’iza a unguwar tasu.
Darakta Janar na Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Alhaji Abba Sa’idu Sufi ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce“Sai da muka kirawo dukkan shugabnnin kabilu mazauna Kano muka tattauna, kafin a yi wa mutumin jana’iza ta Musulunci, shi Musulmi ne har masallaci ya gina a jikin gidansu, inda ake yin Sallah tare da shi, kafin ya rasu.”
A game da kisan marigayin kuwa, matarsa Hajiya Farida Shu’aibu Bello ta ce abin ya faru a ranar Lahadin da ta gabata da daddare suna tare a dakin hutawa, bayan ta kai masa abinci. “Muna zaune sai aka yi masa waya, sai ya ce min mai yi masa gyaran mota da ke aiki da ita a kamfaninsa na ruwan leda ne ke son ya biya shi kudin aikinsa. Sai na hana shi fita, na ce ya
bari gari ya waye tukuna.”
Ta ce ya ce da ita mutumin talaka ne watakila yana bukatar kudin kafin safiya ne. Ta ce ba ta san lokacin da ya fita ba, sai jin karar motar ta yi ya tafi kai wa mutumin kudinsa.
Hajiya Farida ta ce bayan zuwa karfe 10:05 na dare, sai ta fara tunanin me ya tsayar da shi bai dawo ba? Ta ce ta tashi ta kunna maganin sauro tana ci gaba da jira, can da ta je za ta kulle taga, sai ta ji karar ham din motarsa ya dawo, zai shiga gida. Amma kafin ta je ta bude masa kofar, sai ta ji kara sai ta dauka karar taransfoma ce. Amma sai ta ga yarinya ta shigo gidan a guje tana cewa, “Sun harbe shi! “Sun harbe shi!” Da na tambaye ta wa aka harba? Sai ta ce Baba (Daddy) aka harbe.” Ta ce da ta bude kofar gidan sai ta hangi motarsa a tsaye kofarta a bude shi kuma a kwance. Hajiya Farida ta mutanen da suka yi kisan sun gudu, ba tare da an kama su ba, ta ce wasu ’yan unguwar sun ce mutum biyu ne, kuma sun je wurin ne a cikin mota kirar Golf.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan jihar, Magaji Musa Majiya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce har zuwa lokacin ba a kama ’yan bindigar ba, amma suna ci gaba da binciken lamarin.