Rasuwar ’Yan Maulidi 40: Tinubu ya mika ta’aziyya
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar samun rahama ga mamatan da kuma samun sauƙi ga waɗanda suka samu raunuka
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa bisa rasuwar ’yan Maulidi 40 da suka rasu a hatsarin mota a Jihar Filato.
Tinubu ta bakin kakakin sa, Bayo Onanuga, ya yi addu’ar samun rahama ga mamatan da kuma samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
Hakazalika shugaban ƙasan ya jya ajanta wa iyalansu da shugabannin Ɗarikar Tijjaniyya da gwamnatocin jihohin Filato da Kaduna bisa ibtila’in.
Ya kuma umarci Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa (FRSC) ta da inganta ayyuka a fadin ƙasa domin kawar da aukuwar irin haka.
- Sojoji sun kashe ’yan bindiga 4 sun ceto mutane 20 a Kaduna
- Ambaliya: Fursunoni 281 sun tsere a Maiduguri — NCS
A ranar Lahadi ne ɗaliban Islamiyya da ke hanyarsu ta halartar taron Maulidi suka gamu da ajalinsu, bayan da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tirela a yankin Kwandari da ke Jihar Filato.
’Yan Maulidin sun taso ne nufin halartar taron a garin Saminaka da ke Ƙaramar Hukumar Lere a Jihar Kaduna.