Rawar koroso na inganta lafiya- Yahaya dan koroso

Wani matashi mai kidan koroso a gidan wasan gargajiya na Freedom Theater  da ke jihar Legas da ake kira Yahaya Garba ya ce rawar koroso na inganta lafiya, saboda motsa jikin da ake yi. Yahaya Garba dan asalin garin Gwarzo da ke Jihar Kano ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a […]

Rawar koroso na inganta lafiya- Yahaya dan koroso
Rawar koroso na inganta lafiya- Yahaya dan koroso

Yahaya Garba mai kidan koroso (a tsakiya) tare da masu taimaka masa.Wani matashi mai kidan koroso a gidan wasan gargajiya na Freedom Theater  da ke jihar Legas da ake kira Yahaya Garba ya ce rawar koroso na inganta lafiya, saboda motsa jikin da ake yi.
Yahaya Garba dan asalin garin Gwarzo da ke Jihar Kano ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.
Ya ce “A yayin rawar koroso akan jijjiga jiki, kuma masana kiwon lafiya sun ce motsa jiki na kara inganta lafiya.”
Ya ce, shi wannan kida suna kiransa kidan koroso na gargajiya. Ana yin sa nau’i-nau’i ga ’yan dambe da ’yan kokawa da masu rawar koroso na gargajiya. Duk kidan da mai kalangu zai yi za su iya yi, amma mai kalangu ba zai iya wani nau’in kidan da za su yi ba. Kida ne wanda yake yana da sirri da samun alheri a cikinsa.
Ya ci gaba da cewa “Babu shakka na samu rufin asiri da alheri da yawa a kidan kuma na mallaki  abubuwa da yawa a cikinsa. Domin na yi kidan a Jihar Kano da Kaduna da Birnin Gwari da garin Maska da Marabar Jos da kuma Legas kuma na samu alheri da yawa na san jama’a kuma jama’a sun san ni.”
Garba wanda ya shefe fiye da shekaru 20 yana kidan koroso ya bayyana cewa ya shiga kidan ne saboda sha’awar da yake da ita.
Ya bayyana cewa yana amfani da gangunan da ake kira Kwangwas da gangar Bas da Duman girke da Duma da Das da gangar Tsilluwa da kuma Kazagi.
“Wadannan ganguna su ne suke gyara kidan, suke kara masa armashi ta yadda wanda yake nesa da zarar ya ji kidan zai ji sauti mai dadin gaske. Ka san shi kidan koroso iyawa ne ba kowane makidi ne ke yin sa ba sai wanda ya kware. Saboda ganguna da yawa za a jera maka idan ba ka san yadda za ka kida su ba sai ka rikice, saboda kowace ganga da irin sautinta da kuma sautin da take bayarwa. Abin sai wanda ya kware’.  In ji shi.
 Ya kara da cewa yakan yi kidan buta da wasan dirama da rawar koroso da kuma kokawa, amma yanzu ya fi yin kidan koroso kawai.
Ya ce akwai lokacin da aka taba zagin iyayensa kuma aka doke shi, amma duk da haka bai daina kidan ba, saboda ita ce hanyar cin abincinsa.
Saboda haka sai ya ce sojoji da ’yan sanda da jama’ar gari da biki da aure duk jama’a suna gayyatar su.
Shi ma Muhammed Sani da ke kida wa Yahaya Garba gangar Kazagi dan asalin Jihar Zamfara ya ce ya yi shekara fiye da 15 yana kidan gangar Kazagi