Ra’yoyin jama’a kan karin kudin man fetur
‘Yan Najeriya na ci gaba da tsokaci game da karin farashin man fetur da gwamnatin kasar ta yi. Wasunsu na zargin gidajen mai da kin rage farashi idan gwamnati ta rage, amma kuma suke karawa nan take da zarar an kara, ko da sun saya ne a tsohon farashi mai sauki. A kan haka ne […]
‘Yan Najeriya na ci gaba da tsokaci game da karin farashin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.
Wasunsu na zargin gidajen mai da kin rage farashi idan gwamnati ta rage, amma kuma suke karawa nan take da zarar an kara, ko da sun saya ne a tsohon farashi mai sauki.
A kan haka ne wasu masu karanta shafukan zumunta na Aminiya suka bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Al-amin Yusuf: Wannan yana daya daga cikin rashin adalcin ’yan kasuwarmu, domin da zarar gwamnati ta yi ragi, ba za a gabatar da wannan ragin ba sai a ce wai tsohon kaya ne. Amma da zarar gwamnati ta yi kari sai dai ka ji karin daga wannan lokaci babu maganar tsohon kaya ko sabo. Kuma saboda rashin adalci sai ka ji ana zagin gwamnati ba’a duba halin ’yan kasuwa duk dai saboda a kuntata wa talaka. Don haka muna mika kukanmu ga Allah Ya mana maganin duk wani azzalumi walau dan kasuwa ko gwamnati.
Hassan Usman: Ya kamata gwamnati ta sa ido sosai a kan gidajen mai, duk wanda ya kara to a rufe gidan na wani lokaci tare da gargadinsa, idan ya sake karawa za a kwace gidan gaba daya, wannan shi ne zai magance matsalar.
Yahya Yusuf Koki: Ai dama su kadan suke jira, amma da ragi ne sai su yi ta cewa “tsohuwar saukewa ce”, don haka kafin su rage sai lokaci mai tsayi.
Nazyr Abuttahir Al-Sheikh: Zalunci, handama, babakere da neman sai an yi kudi ta ko wace hanya. Me ye bambancinsu da ’yan ***? Suna amfani da rayuwar al’umma wajen tara dukiya.
Engr Suleiman Hadi: Wane ra’ayi talakan kasa yake da shi, sai fatan Allah Ya ba mu damar ci gaba da saya, Ya kawo mana sauki da shugabanni adalai.
Hamza Saidu: Wannan haka ne. Wallahi yau na je gidan mai da sassafe ni ne na farkon ba wa mai a gidan man, tuni sun canza litarsu cikin dare.
Ibrahim A Saad: Allah Ya hukunta su a kan wannan laifin nasu.
Abubakar Ibrahim: Ai sai dai addu’a amma kasar duk haka take.
Abubakar Salisu Gozaki: ‘Yan kasuwarmu ku ji tsoron Allah har gwamnati ta mai da litar 123 amma ta gaza shaida hakan. Amma daga mai da shi 143 a yanzu har kun maida, kuna cin kudi, kowa dai ya yi da kyau ya sani.
Hussen Ismail Safana Hussen: Allah Ya shige mana gaba a al’ammuranmu duniya da lahira mu yi fatan alheri
Sani Dan Baiwa: Allah Ya kara taimaka mana da alhairinsa. Ko nawa za su sai da litar man fetur su sayar za mu saya insha Allah ai sauki yana wurin Allah dama.
Musa Aliyu: Me za mu ce kuwa banda mu ce komai na tafiya daidai. Masu neman gwamnati da sharri kawai dama ba alfarma aka yi mana ba saboda corona. Baba aiki na tafiya daidai yadda ake so.
Ina wacce Kesona: Abin bai mana dadi ba, da wanne talaka zai ji, tsadar rayuwa ko karin kudin, komai ma sun kara mai kudi. Wannan gwamnatin dai ta taba cewa komai zai sauko kafin ta hau, yanzu ta hau kuma komai ya kara. To ta gaza wallahi kin ba mu kunya.
Mansur Nuhu Danmahawahi: Allah Ya shirye su.
Basiru M Adam: Zalinci ne na ‘yan kasuwa.
Sarkinsamarin Sarkin Zamfara: Allah Ya hore mana abin saya.