Rayuka kusan 2000 ‘yan fashi suka kashe a Zamfara – Hukumar NEMA
An bayyana cewa Jihar Zamfara ta rasa rayukan mutane 1,622 cikin wata tara da suka gabata, a sakamakon ’yan fashi da ake zargin suna far wa al’umma da kisa das ace-sace.Babban Darakta na Hukumar Agajin Gaggawa Ta kasa (NEMA), Alhaji Sani Sidi ne ya bayyana haka ta bakin wakilcin Alhaji Alhassan Nuhu; a lokacin taron […]
An bayyana cewa Jihar Zamfara ta rasa rayukan mutane 1,622 cikin wata tara da suka gabata, a sakamakon ’yan fashi da ake zargin suna far wa al’umma da kisa das ace-sace.
Babban Darakta na Hukumar Agajin Gaggawa Ta kasa (NEMA), Alhaji Sani Sidi ne ya bayyana haka ta bakin wakilcin Alhaji Alhassan Nuhu; a lokacin taron ba da tallafin agaji da Gwamnatin Tarayya ta samar.
Ya kara da cewa tallafin, wanda ya hada da kayan abinci da kayan kwanciya da kwanon rufi da kusa da makamantansu, an gabatar da shi ne saboda tausayawa da jajantawa ga al’ummar da abin ya shafa.
Kamar yadda Daraktan ya ce, an bayar da tallafin ne ta hannun Ministan Kudi, Alhaji Bashir Yuguda, wanda shi kuma ya nada kwamitin da ya dauki alhakin raba su, domin a tabbatar da cewa abin da aka raba ya kai inda ake bukata, bai fada hannun wasu bata gari ba.