Rayuwa da ayyukan Babban Joji (mai ritaya) Saddik A. Mahuta a littattafai biyu

A ranar Juma’a, 24 ga Mayu na bana Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Saddik Abdullahi Mahuta ya yi ritaya daga aiki, bayan ya shafe shekaru 22 bisa wannan mukami. A yayin bikin ajiyewar tasa, an gabatar da littattafai guda biyu, daya mai taken Times to Remember: Biography of Justice Saddik Abdullahi Mahuta, OFR da […]

Rayuwa da ayyukan Babban Joji (mai ritaya) Saddik A. Mahuta a littattafai biyu
Rayuwa da ayyukan Babban Joji (mai ritaya) Saddik A. Mahuta a littattafai biyu

A ranar Juma’a, 24 ga Mayu na bana Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Saddik Abdullahi Mahuta ya yi ritaya daga aiki, bayan ya shafe shekaru 22 bisa wannan mukami. A yayin bikin ajiyewar tasa, an gabatar da littattafai guda biyu, daya mai taken Times to Remember: Biography of Justice Saddik Abdullahi Mahuta, OFR da kuma na biyun mai taken Contemporary Legal Issues and kuentessential Jurist: Essays in Honour of Hon, Justice Saddik A. Mahuta, OFR. A tattaunawarsa da wakilinmu, Babban Jojin mai ritaya ya bayyana wasu daga cikin fadi-tashin da ya sha da kalubalen da ya fuskanta a rayuwarsa, wadanda kuma su ne kunshiyar littattafan nan biyu, musamman ma littafin Times To Remember, wanda taubashinsa, Alhaji Bello Musa dankano ya rubuta. Ga abin da mai shari’ar ya fada da kansa:
Basher Yahuza Malumfashi, a Katsina

Kamar dai yadda aka sani, sunana Saddik Abdullahi Mahuta. An haife ni ne a cikin garin Katsina, ranar 24 ga Mayu, 1949, a babban asibitin garin Katsina, a lokacin nan mahaifina yana aiki ne a can. Daga nan, ina kamar dan shekara biyar, a cikin watan Afrilu, 1964 sai aka ba shi mahaifin nawa sarautar Galadiman Katsina, Hakimin Malumfashi. Daga nan ne muka koma can Malumfashi, tare da shi.
Bayan kamar shekara daya, 1966, aka sanya mu makaranta, ni da dan uwana Aminu Abdullahi a garin Mahuta. A lokacin nan muka yi ta mamaki, saboda me za a kai mu karatu Mahuta maimakon a sanya mu a cikin garin Malumfashi, wanda birni ne? Shi dai mahaifin namu bai gaya mana dalilin yin haka ba, domin kuwa mu ba mu tambaye shi ba’asi ba. Daga baya ne ni a karan kaina, tunanina ya ba ni cewa ga dalilin da ya sanya aka yi mana haka. Ka san ita rayuwa ta kauye, tana da wani abu muhimmi guda. Idan ka lura a kauyukanmu, yaro yakan zama ya kammala hankalinsa nan da nan, ya zama mai dogaro da kansa da wuri fiye da yaron da ya tashi a birni. To ni abin da na yi zato ke nan ya sanya aka kai mu makaranta kauye maimakon birni.
Ala ayyihalin dai, na yi makaranta a Mahuta, na dawo Malumfashi kuma dayake na yi rashin lafiya kwarai kuma ga shi a nan babu wata babbar asibiti. Kan haka sai aka yi tunanin cewa tun da yayana, Dokta Tukur Abdullahi yana aiki a babbar asibiti a Hadeja, bari in koma can wurinsa, domin in rika samun kulawa fiye da nan Malumfashi. Saboda da haka sai na koma can wurin nasa, daga nan kuma muka dawo Katsina. Har ila yau kuma na sake dawowa Malumfashi, inda nan na kammala karatuna na babbar firamare, a 1963.
Daga nan ne kuma sai na wuce zuwa Sakandaren Gwamnati ta Funtuwa, inda na kammala a 1967. Bayan na gama sai na fara karatu a Zariya, a Kwalejin da yanzu ake kira da Kufena College. Ita ma saboda matsalar da na samu, sai na bari, na dawo gida na kama aiki a Hukumar Kasuwanci (Marketing Board) a matsayin Akawu. Daga nan kuma, bisa jagorancin shi Dokta Tukur Abdullahi da kuma dai yardar Allah, na zo na sake rubuta jarabawar Afrika Ta Yamma (WASC), wacce yanzu ake kira da WAEC.
Wannan jarabawa ce ta ba ni damar na koma makaranta a Kwalejin Abdulahi Bayero Kano, a lokacin nan tana like da Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, yanzu kuwa take Jami’ar Bayero. A nan ne na yi karatun share fagen shiga jami’a. Bayan na gama sai na je Zariya, inda na yi karatun Shari’ar Zamani (Law). Haka kuma da na kammala sai na tafi Makarantar Shari’ar Zamani a Legas, inda na samu kwarewa da cancantar zama Barista. Bayan na kammala ne sai na yi hidimar kasa a Minna, a Hukumar Shari’a ta Jihar Neja.
Da na kammala wannan hidimar kasa sai na dawo Kaduna, inda na kama aiki a Hukumar Shari’a ta Jihar Kaduna. Ban dade a nan ba sai aka samu wani gurbin aiki a Bankin Manoma na Jihar Kaduna (Kaduna Co-operatibe Bank), na koma can na fara aiki a bangaren kula da shari’a na bankin. Nan na yi aiki har na kai ga mukamin Babban Lauya kuma Sakatare na bankin.
Na bar wannan aiki a 1983, na je na kafa ofishi na kaina, inda na rika gudanar da aikin lauya mai zaman kansa. Ina nan kan wannan aiki, wata rana na je Legas game da irin wannan aiki. Na gama aikin da ya kai ni, na dawo gida da yamma, a daren ranar 23 ga Satumba, 1987; ina zaune ni kadai a gidan wani dan uwana, marigayi Mansur Mahuta sai na bude talabijin domin jin labarai. Nan kawai sai na ci karo da labarin cewa an kirkiro Jihar Katsina da kuma Jihar Akwa-Ibom. Wannan labarin, sai na ji shi a jikina, don haka ina dawowa Kaduna sai yayana, Dokta Tukur Abdullahi ya ce mani in je in ga Alhaji Bala Kuki. Lokacin nan an ba shi mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina na riko, za su shirya su tafi domin kafa sabon mulkin jihar.
Da na je na same shi, na taya shi murna sai ya ce mani: “Za mu neme ka.”
Ni kuwa da na ji haka sai na ce masa a gaskiya ni babu yadda za a yi in kara yin aikin gwamnati. Ya ce shi ke nan.
Ana nan bayan sun taho Katsina da mako biyu sai aka yo mani waya, aka ce Gwamna yana nema na. Na je na samu Alhaji Bala Kuki, muka tafi ofishin Gwamna Abdullahi Sarki Mukhtar. Bayan mun gaisa da shi sai ya shaida mani cewa suna so ne in zo in yi aikin kafa Hukumar Shari’a ta Jihar Katsina. Nan take na gaya masa cewa ba na sha’awar aikin gwamnati, domin na riga na kafa ofishina, inda nake cin gashin kaina kuma ina jin dadin tafiyar da al’amurana.
Jin haka sai ya ce mani: “A’a, ku Katsinawa wadanne irin mutane ne?” Na ce masa me ya faru? Ya ce mani: “Ai Mamman danmusa na fara yi wa magana, shi ma ya ce ba zai yi aiki da soja ba, dayake shi dan siyasa ne. To, kai kuma na tuntube ka ka kawo wani uzuri.” Ni to ba zan iya tilasta ka ba amma dai ka sani cewa, wannan aiki Katsina za a yi mawa, ni kuma ba dan jiha ba ne, aiki ne ya kawo ni Katsina, don haka ina neman taimakon Katsinawan da nake jin za su iya yin aiki tare da ni.”
Daga nan na ce masa a bar ni, zan je in yi tunani.
Da muka fito tare da Alhaji Bala Kuki, bayan mun yi wa Gwamna godiya, sai na ce masa, wallahi ranka ya dade ba na son aikin gwamnati. Shi ne ya ce mani:
“Akwai wasu abubuwa a rayuwa da za ka yi ba don kanka ba. Kamar wani lokaci in kana aiki, kana wani mukami, saboda ganinka a wurin ana iya raga wa wani, wani kuma na iya cin amfani, koda kai ba ka ci wani amfani kai tsaye daga aikin ba.”
Da na yi tunani, sai wannan magana ta shiga jikina kwarai. Na ce masa na amince, zan zo in yi aiki da ku.
A haka na je Katsina, na zama Babban Sakatare a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Katsina, muka kafa wannan ma’aikata, dama tun daga farko mun zo da lauyoyi hudu daga Jihar Kaduna, domin su ’yan asalin Jihar Katsina ne. Daga nan muka dauki wasu sabbi, muka ci gaba da aiki, aka kafa ma’aikatar ta kankama sosai.
Daga nan ne na ce ba ni da sha’awar ci gaba da aiki da gwamnati. Da ma tun farko niyyata ita ce, idan na zo muka kafa ma’aikatar sai in koma Kaduna in ci gaba da harkar gabana da na fara a baya.
Ana nan, ran nan na zo kotu na fito, a lokacin nan Mai Shari’a Umaru Abdullahi shi ne Babban Jojin Jihar Katsina, dama shi daga Kotun daukaka kara ta Tarayya ce aka ce masa ya zo Katsina ya taimaka a kafa Ma’aikatar Shari’a ta jihar Katsina. Ba karamar sadaukar da kai ya yi ba da ya amince ya zo. Da na shiga ofis dinsa don mu gaisa, sai ya ce mani: “Na rubuta sunanka cikin wadanda za mu aika domin a ba su mukamin masu shari’a.”
Na ce masa, haba ranka ya dade, ni da nake son ma in bude sabon ofis a nan garin, in ci gaba da zama lauya mai zaman kansa? Na ce masa na gaji da aikin gwamnati haka nan.
Ya ce mani: “A’a, ai ba ka isa ba.” Nan muka yi wasa da dariya. Haka dai abu ya kammala, aka zo aka nada mu a 1989, aka rantsar da mu a mukamin alkalan babbar kotu, da ni da wani Inyamuri, Mista Onorah, ya rasu – mutum mai kokari kwarai da gaske.
Da muka zo muka fara aiki, muna nan, bayan shekara biyu sai Umaru Abdullahi ya ce zai koma wajen aikinsa da ya baro. Ya je ya yi magana da manya, su Mai Shari’a Muhammad Bello da Mai Shari’a Mamman Nasir, da ma su suka bukace shi da ya zo ya yi wannan aiki, domin ganin cewa an samu kyakkyawan tushe a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Katsina. Da zai tafi sai ya ba da sunana, ya ce yana ba da shawarar da a ba ni mukamin Babban Joji.
Ni kuwa na ga shekarata biyu ke nan da zama mai shari’a a babbar kotu, Allah cikin ikonSa da yardarSa, aka ba ni wannan mukami. An rantsar da ni a ranar Juma’a, 27 ga Disamba, 1992. Muna fitowa daga wajen rantsuwa, na je gida sai ga sako cewa Allah Ya yi wa mahaifinmu rasuwa a wannan rana.
A nan take muka shirya muka tafi Malumfashi. Ka ga ranar Juma’a aka rantsar da ni, sai da na yi shekara 22 kan mukamin Babban Jojin Jihar Katsina ga kuma shekaru biyu da na yi a matsayin mai shari’a a baya. Ke nan na yi shekara 24 ina aikin shari’a.
Wani abin da ya ba ni mamaki kuma na yi juyayi a kansa shi ne, ranar da na aje wannan aiki, sai ta kasance ita ma Juma’a.

’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe