Rayuwa da ayyukan zabiyar Afrika: Oumou Sangare

Oumou Sangare, ita aka fi sani da sunan Umma Sangare a kasar Hausa. Duk da cewa ita ’yar kasar Mali ce, amma saboda baiwar da Allah Ya yi mata ta waka, sunanta ya karade ko’ina da ina, musamman ma a Afrika Ta Yamma. Ko ta yaya zabiyar ta fara waka kuma yaya aka yi ma […]

Rayuwa da ayyukan zabiyar Afrika: Oumou Sangare
Rayuwa da ayyukan zabiyar Afrika: Oumou Sangare

Oumou Sangare, ita aka fi sani da sunan Umma Sangare a kasar Hausa. Duk da cewa ita ’yar kasar Mali ce, amma saboda baiwar da Allah Ya yi mata ta waka, sunanta ya karade ko’ina da ina, musamman ma a Afrika Ta Yamma. Ko ta yaya zabiyar ta fara waka kuma yaya aka yi ma har ta shahara? Domin amsa wadannan tambayoyi da ma wasu da suka dangance ta, wakilinmu ya yi bincike, musamman a madawwamarta ta intanet, wato www.oumousangare.co.uk da kuma Wikipidia, inda ya samo ingantattun bayanai game da mawakiyar.
Kamar yadda binciken Aminiya ya nuna, an haifi Oumou Sangare ne a birnin Bamako na kasar Mali, a ranar 25 ga watan Fabrairu na shekarar 1968. Ita ’yar kabilar Wassulu ce, domin haka da yaren ne ma take rera mafi yawa daga cikin wakokinta.
Ta gaji sana’ar waka daga mahaifiyarta, Aminata Diakite, wacce ta kware wajen kidan amada a gargajiyance. Irin yadda Oomou ta samu amsuwa a sana’arta ta waka, ta samu wani lakani, inda ake kiranta da taken ‘Tsuntsuwa mai waka ta Wassulu.’
Mafi yawan wakokin zabiya Oumou na soyayya ne, musamman kuma tana yin wakokin da ke yaki da al’adar nan ta yi wa mata masu karancin shekaru aure, kamar kuma yadda take yaki da maza masu auren mata da yawa.
Baya ga sana’arta ta waka, zabiyar kuma ta fantsama cikin harkokin kasuwanci, domin kuwa tana taba sana’ar noman zamani, tana da otel-otel da ake gudanarwa domin samun kudin shiga, kamar kuma yadda ta shiga yarjejeniya da wani kamfanin kera sassan motoci na kasar Jafan, inda suke amfani da sunanta wajen sayar da motoci.
Mawakiyar ta mallaki wani babban otel mai suna Hotel Wassoulou, wanda ke da dakuna talatin, a babban birnin kasar Mali, Bamako. A nan ta ware shiyya ta musamman, inda makada da mawaka ke gudanar da sana’arsu, inda ita kanta take yin wasanninta lokaci-lokaci. Kamar yadda ta fadi dalilinta na gina otel din, ta ce: “Na taimaka wa kaina ne na gina otel din. Na yi haka ne domin in nuna wa mata misalin cewa za ki iya kyautata rayuwarki ta hanyar yin aiki tukuru. Haka kuma na nuna cewa mata da yawa suna yin aiki a wannan zamanin. Wasu ma suna kafa kungiyoyi ne, inda suke sana’o’i daban-daban, kamar saka suttura, yin sabulu da sauransu.”
Ganin irin yadda take da himma ga dukkan al’amarin da ta sanya gaba, an taba tambayar ta cewa ko tana da sha’awar shiga harkokin siyasa. Oumou, wacce ta taba zama Jakadar Hukumar Bunkasa Noma da Samar da Abnici ta Majalisar dinkin Duniya (FAO), sai ta amsa da cewa ba za ta iya zama ’yar siyasa ba. Ta fadi dalilinta cewa: “A matsayina na mawakiya, ina da ’yancin fadin albarkacin bakina amma idan na shiga siyasa, zan rika bin wasu ra’ayoyi ne na manyan mutane.”
Oumou Sangare ta kasance ’yar uwa ga fitaccen dan fim din nan na kasar Mali, Omar Sangare. A cikin shekarar 1990 ne ta fara yin tashe, a lokacin da ta fitar da faifan wakarta mai taken Moussolou. Faifan ya yi matukar samun kasuwa, musamman a Afrika Ta Yamma, inda aka ce an sayar da kwafi 250, 000, duk da cewa wasu kwafin faya-fayan an gurza su ne ba da izinin ta ba. Wani abu game da ita shi ne, tana kashe mafi yawan lokacinta ne wajen rubuta wakokin da kuma rerawa.
Tana samun nasarar kama zukatan masu sauraren wakokinta, duk da cewa ba kowa ke fahimtar yaren da take amfani da shi ba. Ba ga bakaken fata ba, hatta kasashen Turawa, an ruwaito cewa ana sauraren wakokinta. Wannan kuwa bai rasa nasaba da irin zaki da launin muryarta da kuma yadda take gwamutsa kayan kidan gargajiya na Afrika da na zamani a mafi yawan wakokinta. Dalilin haka ne ma ya sanya faifanta mai taken Ko Sira, wanda ta fitar a shekarar 1993 ya samu gagarumar kasuwa a Amurka, inda har wani kamfanin buga wakoki ya wallafa shi.
Mawakiya Oumou Sangare, tun tana ’yar karama ta fara waka, inda take taimaka wa mahaifiyarta, wacce ita ma zabiya ce ta gargajiya. Ita da mahaifiyar tata suna sana’ar waka ne domin su samu abincin ciyar da iyali, kasancewar maigidansu ya gudu ya bar su cikin wahala.
Ta fara samun daukaka ne a harkar waka, tun tana ’yar shekara biyar, inda a makarantarsu aka sanya gasar waka kuma ta samu nasarar zama ta farko. A karshen gasar ne ta rera waka gaban ’yan kallo da suka kai mutum dubu shida, a filin wasa na Bamako. Lokacin da ta kai shekara 16 kuwa, sai ta fara fita rangadin waka, tare da wata kungiya mai suna Djioliba. Daga bisani kuma ta yi aiki da kwararren mawakin Mali, Amadou Ba Guindo, inda ya taimaka mata ta buga faifanta na farko, mai taken Moussoulou.  Haka kuma, wani fitaccen mawaki, Ali Farka Toure, ya taimaka mata, inda ta shiga sahun mawakan duniya, wanda a lokacin tana da shekara 21 a duniya.
Wasu daga cikin faya-fayaenta da suka yi tashe sun hada da Moussoulou (1990) da Ko Sira (1993) da Worotan (1996) da Oumou (2004) da kuma na baya-bayan nan, mai suna Seya (2009).
Zabiyar kuma ta samu kyaututtukan karramawa daban-daban saboda wakokinta. A 2001 ne Hukumar UNESCO ta ba ta kyautar karramawa saboda la’akari da gudunmowar da take bayarwa, wajen wayar da kan al’umma da tabbatar da zaman lafiya a duniya, ta hanyar wakokinta.
Lokacin da ta fitar da faifanta na baya-bayan nan mai taken Seya (Farin Ciki) a bara, Oumou ta ce sai da ta kwashe tsawon shekaru uku tana shirya wakokin cikinsa. Ta ce: “Nakan natsu, in zabi wakokina daki-daki.”
An nazarci wakokinta da cewa suna da kama zuciya kuma ga amo mai zaki wanda kan iya sa mutum rawa cikin lokaci, kamar kuma yadda kalmomin wakokin ke dauke da ma’ana. “Ni a wurina, kalmomin wakokina sun fi muhimmanci fiye da amon kidan. Ni nakan rubuta yawancin wakokina, kuma nakan yi la’akari da al’adun Mali na gargajiya. Nakan samu ilhamar tsara wakokina ta hanyar nazarin abubuwan da ke faruwa cikin al’umma. Da zarar na ga wani abu ya faru mai muhimmanci, sai kawai in rubuta shi. Nakan fadi abin da nake so da abin da nake tunani saboda ina da cikakken ’yanci a matsayina na mace. Na yi amanna da cewa, wakokina sun samu gurbin zama sosai a zukatan matan Afrika.” Inji Sangare.
Game da yadda take ji a yayin da take rere waka, Oumou Sangare ta ce: “Gaskiya ne cewa, a duk lokacin da nake rera waka, nakan samu farin ciki da nishadi, amma duk da haka, nakan saka wasu sakonni da za su ilimantar da al’umma.”