Rayuwa irin ta su Azima!
Ina zaune bisa teburin cin abinci, na kammala ci da sha, na yi hamdala, sai uwargidana to leko daga cikin dakinta, tana janye da wata ’yar karamar yarinya. Suka yiwo daidai tsakiyar falon da muke ciki, ta kalle ni, ta kuma sake dubar kanwarta (wato amaryata) da ke zaune kusa da ni, ta ce ‘na […]
Ina zaune bisa teburin cin abinci, na kammala ci da sha, na yi hamdala, sai uwargidana to leko daga cikin dakinta, tana janye da wata ’yar karamar yarinya. Suka yiwo daidai tsakiyar falon da muke ciki, ta kalle ni, ta kuma sake dubar kanwarta (wato amaryata) da ke zaune kusa da ni, ta ce ‘na samo mana ’yar aikin gidan da muka yi magana’. Da farko na dauka ’yar ’yar aikin ce ta jawo wa hannu, ita ’yar aikin na zuwa daga bayanta. Amma da na jira na wasu mintuna ban ga wata mata ta biyo baya ba, sai na hakikance cewa wannan berar da ke tsugune kusa da ita, ita ce ’yar aikin. Ban dai ce komai ba! Amma ai Hausawa na cewa shiru ma magana ce.
Sai da aka samu kamar kwana bakwai da kawo yarinyar sa’annan na samu sukunin nazarinta sosai. Yarinya ce ’yar karama, kila ba ta wuce shekara 11 zuwa 12 ba. Ba ta da tsawo ko kibar jiki, kila shi yana yi mata kallon kankanta sosai, amma irin yadda take fama da aikace-aikacen cikin gida, na fara tunanin ko dai lange-lange ce, domin aikin da take yi a gidan ya kai na katti uku, kuma ba damuwa, ba gajiyawa, ga kuma yawan murmushi da annashuwa.
A daidai wannan lokaci ne na fara yarda cewa bautar bayi da aka yi can da a zamanin zuwan Larabawa da Turawa ta sake kunno kai a tsakanin al’ummarmu. Ba wai nufina ba ne in ce barantaka ko ’yan wanke-wanke da sharar gida bauta ba ce. Ko alama! Amma me ya raba dambe da fada? Babban abin da ya fi takura mini tunani shi ne, ta yadda na yarda aka kimshe wannan abin alhaki a cikin gidana a matsayin ’yar aiki, alhali kuwa ba ’yar aiki ba ce, face wadda aka dauko daga gidan iyayenta ake amfani da ita domin wasu su huta.
Rayuwar kaskanci ko ta shan jinin wadansu domin kawai mutum ya isa ko ya kai matsayi ko yana bisa wani mukami abu ne da ya dade tare da mu; bawa da baiwa da kuma bayi da barwa da kuma barantaka; tamkar cin tuwo da shan ruwa suke tattare da mu, al’adar zama da su ba wai abin damuwa ba ce, domin kuwa ba an gina ta ne domin tabbatar da bauta ba. To amma wannan tada da ta kawo Azima cikin gidana daban take da wadda muke bayani ta tarihi; wannan bauta ce irin ta zamani, ko mu yarda ko kada mu yarda!
Azima dai ba ta yi makaranta ba ko da ta baro kauyensu daga Jihar Kano, ban kuma sani ba ko ta yi karatun Allo ko Islamiyya. Sallah kam ba ta wuce ta, abin da take cewa cikin Sallar shi ne ba zan iya karaswa ba. Wallahi ban san ko ta san Alhamdu ba ko kuma in ta iya Tahiya. Iyakata da ita in ga tana dungure-dungure da duke-duke da salallami, in ta gama zaman Tahiya. Bai taba zuwa min a rai in binciki matsayin ilminta ba, bare in gane ko tana ganawa da Allah da kyau, don gyaran gaba! Ban damu ba! Ba kuma don komai ba sai don jin da nake ai ba a kawo ta gidana domin in yi mata tarbiyya ko in koya mata Sallah ko makamancin haka ba. A kullum sai in tuna abin da Uwargida ta ce da ni, ga ’yar aiki nan na samo mana! Aiki ta zo yi ba addini ko zuwa makarantar boko ko Islamiyya ba. Aiki kurum! Wannan shi ne abin da ya fi damuna. ’Yar aiki! Aikin ko ba ta taba cewa ya gimshe ta ba. Sai na dauka cewa kila tun a gida sai da iyayenta suka yi mata horo na musamman kafin su ‘sayar’ da ita zuwa gare mu kan Naira dubu uku kowane wata, har Mahdi! Ta iya wanki da wanke-wanke. Ita ce sharar filin kwallon gidana; domin kuwa daga turakata zuwa dakunan matana da na yara tamkar filin kwallo ne. Ba ta gajiya wajen sharewa da goge tayils duk tsawon rana. Ita ce goye ko dauke da Zaki ko Abul. Ita ce mai share wa Iman ko Zeezee majina da canja musu wando ko kai su bayan daki, domin fitsari. In na tashi fita zuwa aiki, can za ka ganta a guje ta je bude get. Da na wuce ta yi ciki a guje zuwa barga domin yin shanya, kan ka ce kwabo ta fada kicin tana taya Uwargida ko Amarya dafa abinci. Ba hutu, ba ranar hutawa!
Babban abin da ke zuwa a tunanina shi ne da alama fa ni ma na shiga sahun azzaluman kasar nan, domin kuwa wannan ’yar karamar yarinya kamata ya yi a ce tana makaranta domin karatu, ba ta buge ga barantaka a gidana ba.
Ni a nawa tunanin, ai irin wannan yanayin ne ke sa kullum al’amurran kasar nan ke kara rincabewa da lalacewa! Ina gaskiyar lamari ga Maigida da ke da irin Azima a gida ya bar ta tana bauta wa nasa ’ya’yan da suke ta faman fadi-tashi domin zuwa makaranta! A kullum rana ta Allah na ga ’ya’yana na ta faman homwok, ita ta yi tsuri tana kallon talbijin ko satilayit, sai in ji kamar in yi kuka. Nakan ce a cikin raina, kai ma dai macuci ne kamar saura!
To amma, shin laifina ne idan matana da yarana sun bautar da irin su Azima? Laifina ne da ake safarar irin su Azima zuwa gidajen alfarma domin iyayensu da masu safarar tasu su samu abin kaiwa a bakin salati? Laifina ne?
Tambaya ce mai wuyar amsawa. Amma duk da haka sai da na fahimci wani abu. A gidan iyaye irin na su Azima talauci ya riga ya yi gida ya zauna. Yayyenta sun kai goma, kanne kuwa bakwai. Da ’ya’ya 18, mahaifi irin na Azima kofofin da suka rage masa na ciyar da su da sauran mata da ’yan uwa ba su wuce biyu ba. Kofa ta farko ya tura maza daga cikinsu zuwa ‘karatun allo’ can wata kasa tare da wani malami da shi ma ya kasance macuci ne, ya bautar da su a sabon matsuguninsu. Su ne masu share-share da barace-barace a gidaje irin wadanda Azima ke zaune a ciki ko a gidajen karuwai ko tasha ko shagunan sayar da abinci. Ko kuma ya tura matan, irin su Azima. ta hannun wasu azzaluman, suna barance.
Abin ban haushi shi ne idan aka ba Azima Naira dubu 3 a wata, uwargijiyarta za ta amshe dubu 2, ta aika wa iyayen su Azima da dubu 1. Ita kuwa Azima, awalajarta ba ta wuce wurin kwana da abinci da wahalar aiki ba, ba dare ba rana ba.
Sai dai duk da wannan badakalar Azima da sauran irinta da ’yan uwanta suna ma cikin jin dadin duniya ne, domin kuwa akwai miliyoyi irinsu da ake turowa ba don su yi almajirci ba, ba don barance ba, sai dai domin su fito bakin titi ko Allah Ya sa wani mai mota ya banke su, su mutu, iyayensu su rankaya kotu, domin a biya su diyya. Ina amfanin irin wannan rayuwa ta Azima da wadansu irin ta a doron kasa? Tambaya ce da ke neman amsa!