Rayuwar Abba Hikima da Hamdiyya na cikin haɗari — Amnesty
Dole lauyanta sai da ya nemi kariyar ’yan sanda a zaman kotun da aka yi na ƙarshe saboda fargabar da suke ciki.
Ƙungiyar Kare Haƙƙin bil Adama ta Amnesty International, ta bayyana cewa rayuwar matsahiyar nan Hamdiyya Sidi Sharif da gwamnatin Sakkwato ta gurfanar a kotu da lauyanta Abba Hikima na cikin haɗari.
Ƙungiyar ta buƙaci mahukuntan Nijeriya da su gudanar da bincike game da barazanar da ake yi ga rayuwar matasan biyu.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na Najeriya, Isa Sanusi ya fitar, ya ce, “yanzu haka bayan fuskantar shari’a saboda ta yi amfani da ƴancinta na tofa albarkacin baki, Hamdiyyya Sidi Shariff da lauyanta Abba Hikima suna fuskantar barazana ta hanyar kiraye-kirayen waya da fuskantarsu da wasu ɓatagari ke yi da ma masu iƙirarin cewa su ‘jami’an sirri’ ne.”
Sanarwar ta ƙara da cewa dole lauyanta sai da ya nemi kariyar ’yan sanda a zaman kotun da aka yi na ƙarshe saboda fargabar da suke ciki, “wanda hakan ya sa zuwansu kotun ke da wahala.”
Hamdiyya na fuskantar shari’a ne saboda zargin ɓata sunan Gwamnan Sakkwato, lamarin da ya ɗauki hankalin mutane da dama.