Rayuwar Allah-ba-ku-mu-samu muke yi —Kansilolin Arewa

Yadda matsaloli suka dabaibaye kansiloli a Arewacin Najeriya

Rayuwar Allah-ba-ku-mu-samu muke yi —Kansilolin Arewa

Kansiloli su ne suka fi kusa jama’a, a jerin shugabannin siyasa wanda hakan ya sa suke da saukin gani, sannan ake yawan kai musu koke-koke da bukatun rayuwa.

Sai dai binciken Aminiya na gano cewa rashin sanin hakikanin aikin kansila da yadda har yanzu gwamnoni ba su sake wa kananan hukomomi mara ba, ya taimaka wajen jefa kansilolin a cikin matsala.

Jihar Kano

A tattaunawar da Aminiya ta yi da Kansilan Shahuchi a Karamar Hukumar Birni da Kewaye, Malam Abba Musa, ya ce sakamakon rashin kudi ya sa kansuloli da dama ba su iya zuwa mazabunsu.

“Gaskiya a yanzu ta kai kansiloli da dama suna gaza shiga mazabunsu saboda ba su da kudin da za su iya tunkarar matsalolin al’ummarsu.

“Idan kansilan ya shiga mazabarsa zai iske masu bukatu da yawa suna jiransa, tun daga kan rashin lafiya da masu neman abinci wanda kuma idan ka ga halin da suke ciki dole ka tausaya musu.

“Akwai kuma mutanen da ko ka rantse musu ba ka da kudi ba za su yarda ba, domin gani suke cewa idan ka shiga karamar hukuma kamar kudi ne a ajiye diba kawai za ka yi don haka idan suka kawo bukatunsu dole ka biya musu,” inji shi.

Kansilan ya kuma yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Birni bisa taimaka musu da yake yi wajen tallafa wa al’ummarsu.

“Mu dai alhamdulillah Shugaban Karamar Hukumarmu yana taimaka mana da dan abin da muke iya warware matsalolin al’umarmu,” inji shi.

Shi kuwa Kansilan Guringawa, Malam Muslihu Yusuf Ali, cewa ya yi, “Kasancewar kansila shi ya fi kusa da al’umma don haka mutane sun fi kawo mana bukatunsu wanda kum ba za mu iya ba kasancewar dan albashi da alawus din da ake ba mu bai taka kara ya karya ba.

“Sai ki ga mun kasa biyan bukatun al’ummarmu. Ba abin mamaki ba ne a wayi gari a samu kansila yana neman rancen Naira dubu daya.

“Shi ya sa kullum nake fadin cewa dole kansila ya kasance yana da wata sana’a ta daban domin samun halin da zai tallafa wa al’ummarsa.”

Ya ce “Duk da cewa muna da kyakkyawar alaka a tsakaninmu da shugaban karamar hukumarmu domin muna bayar da shawarwari ana kuma yi mana ayyukan da suka kamata, ni an yi aiki a mazabata da ya fi na Naira miliyan 100, amma ita kanta karamar hukumar tana fama da kanta.”

Ya yi kira ga jama’a su fahimci yadda ayyukan kansiloli suke cewa ba suke zartar da ayyuka ba, aikinsu bai wuce su bayar da shawara ba.

“A cikin kansiloli, hudu ne kadai ke da ofis sauran ko kujera ba su da ita a karamar hukuma.

“Aikinsu shi ne su bayar da shawara ko su kai bukatar al’ummar mazabunsa. Idan an yi dace akwai kudi a karamar hukuma shi ke nan a aiwatar idan ba kudi sai dai a yi hakuri.

“Sannan akwai bukatar mutane su canja tunaninsu cewa kudi ake samu a siyasa. Ita siyasa aiki ne na hidima wa al’umma,” inji shi.

Kuma ya yi kira ga gwamnatocin jihohi su taimaka su ba kananan hukumomi cikakken ikon tafiyar da aikinsu domin wannan ne kadai hanyar da za a samu ikon tafiyar da ayyukan kananan hukumomi cikin nasara musamman irin su tallafa wa matasa da sana’o’i da sauransu.

Jihar Bauchi

Da yawa daga cikin kanslolin da Aminiya ta zanta da su a Bauchi ya ce rayuwarsu tana da sauki ne in kansila ya tsare fada wa al’ummarsa gaskiya, kuma bai guje su ba.

Sun kuma ce kalubalen da ke akwai shi ne da yawan jama’ar da ke mazabunsu da kowa ke musu kallon gwamna ko Shugaban Kasa da za su iya biya musu dukkan bukatunsu, bisa la’akari da irin matsalolin tattalin arziki da rashin lafiya.

Wadansu daga cikin kansilolin sun ce da wuya ka fito daga gidanka ba ka samu mutum 50 zuwa 100 suna jiranka ba, kuma kowa da bukatarsa.

Daya daga cikin kansilolin ya ce wata rana ya fito daga gidansa da safe sai ya tarar da wadansu mata daya daga cikinsu tana makyarkyata tana faduwa, ba ta da lafiya, kuma babu abinci a gidansu, inda ta ce kwanansu uku ba su ci komai ba.

Sai ya auna mata abin da ya sawwaka ya sa aka kai ta gidansu kuma ya nemi shugaban karamar hukumarsu ya koka masa kan matsalar wannan mata.

Shugaban Kungiyar Kansiloli ta Jihar Bauchi, Alhaji Musa Zango ya ce a gaskiya rayuwar kansiloli 334 da suke Jihar Bauchi sai godiyar Allah domin sun samu dama daidai gwargwado daga Gwamna da shugabannnin kananan hukumomi, saboda kowane wata suna samun albashi, kuma suna samun kudaden gudanar da ayyuka a kowane wata.

Alhaji Musa Zango ya ce bayan sun samu kudaden suna yin taro kowane wata kuma kowa a cikinsu yana gabatar da matsalolin mazabarsu a lokacin taron kuma ana daukar bukatun ana kai wa Ma’aikatar Kananan Hukumomi ana kuma biya musu wadannan bukatu.

Shugaban Kansilolin ya ce sai dai yanayin da ake ciki na matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa ba maganinsa sai fadin gaskiya da taimakawa daidai gwagwado, inda ya ce idan ka ga kansila ba ya zama a gidansa shi ya so don ya dauki abin da ya fi karfinsa ne.

Jihar Kaduna

Kansilan Badarawa/Malali a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, Malam Ibrahim Sarki dan Jam’iyyar PDP ya bayyana cewa rayuwar kansaloli a jihar wahala kawai suke yi saboda matsi da ake samu daga jama’a domin mafi yawan mutane ba su san aikin kansila ba a gunduma.

Ya kara da cewa sannan wadansu shugabanin kananan hukumomi wadanda suke da wuka da nama su suke fitar da wasu abubuwa ba tare da sanin kansila, ba sai dai kawai a ba shi labari.

Ya ce hakan ya sa yawancin kansiloli suke karewa da albashinsu kawai tunda ba su da wani abu da yake shigowa.

Sai kila in wani alawus dinsu ya shigo su tallafa wa jama’a da sauransu.

“Kansila ba ya samun wani abu da ake ba shi domin kula da jama’rsa. Sai dai idan akwai kyakkyawar alaka da shugaban karamar hukuma, idan ka dauki aiki ka kai masa sai ya yi. Idan aka samu wani abu to, irin rayuwar da kansila ke ciki ke nan,” inji shi.

Game da kalubalen da suke fuskanta a wurin jama’a sai ya ce, “Gaskiya mutane ba su fahimci aikin kansila ba, idan suka zo bukatun kansu suke kawowa maimakon abin da ya shafi al’umma.

“Sai ka ga mutum yana fada maka yaronsa ba shi da lafiya. Kawai matsalolin rayuwa da aka shiga ne a gabansa ba aikin mutane ba.

“Kuma ka san wadansu ba su da aikin yi, wadansu iyayensu an sallame su a aiki. Talauci ya damu mutane. Wadansu kuma rashin lafiya ne.

“Amma da wuya ka ji mutum ya ce ga aiki domin ci gaban jama’a ko unguwa.

“Sai dai idan abu ne da ya shafi matasa masu shaye-shaye a nan ne ake daukar kansila da mutunci.

“Amma tsakani da Allah sarakuna da masu unguwanni da malaman Musulunci da fastoci suna taimakon mu domin suna da karfin fada-a-ji a cikin al’umma, don haka idan wani abu ya taso mukan ruga wurinsu mu fada musu, su kuma sai su nemi jama’a su fada musu,” inji shi.

Game da alakarsu da shugabannin kananan hukumomin, sai ya ce “A yanzu matsalolin da ake fuskanta a kananan hukumomi kudadensu daga Gwamnatin Tarayya ba sa shiga cikin asusunsu kai-tsaye.

“Ssannan gwamnoni na sa ido a kai, wannan ya sa da zarar an zare kudin albashi a ciki sai ka ga abin da zai rage ba zai isa a yi wani aiki mai karfi ga jama’a ba.

“To, muna kokarin janyo hankalin shugabannin kananan hukumomi ta yadda za a fara ba da tallafi domin taimakon al’umma a cikin unguwanni.

“Ka san al’ummarmu sun fi son kullum a ba su, amma a yanzu muna janyo hankalinsu wajen ganin sun koyi sana’o’i domin dogaro da kansu,” inji shi.

 

Daga: Lubabatu I Garba, Kano da Ahmed Mohammed, Bauchi, da Mohammed I. Yaba, Kaduna