Rayuwar al’ummomi a kan iyakar Najeriya da Kamaru
kasar Kamaru ta yi makwabtaka da Najeriya daga bangaren gabas . Wannan ya sa al’ummumin da ke kan iyakar kasashen biyu yin zirga-zirga a tsakaninsu domin kasuwanci da kuma yin wasu sana’o’in dogaro da kai. Wannan ya sa wasu ’yan Najeriya gudanar da sana’ar su da fito a kogin Faro da ke tsakanin karamar Hukumar […]
kasar Kamaru ta yi makwabtaka da Najeriya daga bangaren gabas . Wannan ya sa al’ummumin da ke kan iyakar kasashen biyu yin zirga-zirga a tsakaninsu domin kasuwanci da kuma yin wasu sana’o’in dogaro da kai.
Wannan ya sa wasu ’yan Najeriya gudanar da sana’ar su da fito a kogin Faro da ke tsakanin karamar Hukumar Touroua da kuma Beka a arewacin kasar Kamaru.
A kullum jama’a maza da mata ne suke yin kai kawo tsakanin garuruwan biyu da kuma kauyukan da ke kusa. A cikin wannan yanayin ne wakilinmu ya yi kacibus da wasu mata wadanda suke kokarin haye kogin.
Matan sun bayyana cewa a kullum suna ketara wannan ruwan domin biyan bukatunsu kamar su yin nikan gari da za a yi abinci, ko kuma dai sayan wani abin bukata.
Ana amfani ne da babura da kuma kwale-kwale wajen ketarawa. A zantawarsa da daya daga cikinsu, mai suna Hajiya Sutura wadda ta taso daga karamar Hukumar Beka zuwa Bulkere, ta kuma ce hakan take yi a kodayaushe.
Ta ce suna biyan Naira 20 wani lokacin kuma Naira 50 ga masu aikin fiton. Domin kauce wa hadari, idan ruwa ya kawo sosai ba ta iya ketarawa ta wannan gabar, tana canzawa zuwa wani bangare na daban inda ruwan ya ja.
Amma abokiyar tafiyarta mai suna Aisha ta ce ita komai dare tana haye ruwan domin ta koma gida. Wani lokacin kuma komawa da baya take yi ta kwana a garin da ta ziyarta.
Wasu daga cikin masu fiton’yan asalin Najeriya ne, Aminiya ta samu ganawa da daya daga ciki mai suna Ibrahim Joseph Jukun, wanda ya ce ya kwashe shekara 40 a Kamaru, yana gudanar da sana’ar fito a bakin kogin. Ya ce idan ruwa ya ja, yakan koma sana’ar su ne saboda a lokacin jama’a suna iya ketara ruwan da kafarsu.