Rayuwar Bahaushe a kasar Botswana

An dade da sanin yadda Hausawa ke da kwazo wajen neman na kansu ta hanyar sana’o’i da fatauci tare da fantsama a ko’ina a duniya. Domin haka bai zame abun mamaki ba lokacin da Aminiya ta yi kicibis da wani Bazazzagi da harkar cinikin hauren giwa da sauran namun daji ta kai shi uwa duniya […]

Rayuwar Bahaushe a kasar Botswana

 Malam Alasan Sulaiman sanye da farar riga a tsakiya tare da wadansu daliban Najeriya da ke karatu a kasar BotswanaAn dade da sanin yadda Hausawa ke da kwazo wajen neman na kansu ta hanyar sana’o’i da fatauci tare da fantsama a ko’ina a duniya. Domin haka bai zame abun mamaki ba lokacin da Aminiya ta yi kicibis da wani Bazazzagi da harkar cinikin hauren giwa da sauran namun daji ta kai shi uwa duniya zuwa kudancin Afrika. Mannir dan-Ali da ya kai wata ziyarar aiki Gaborone, babban birnin kasar Botswana, ya tattauna da  Alhaji Alasan Sulaiman, dan asalin gida mai lamba I 19 a Layin Wawa na Tudun Wadan Zariya. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Tun yaushe ka zo Gaborone babban birnin kasar ta Botsawana kuma bisa wane dalili?
Alasan: Na zo nan tun a shekarar 1971, wato shekaru arba’in da biyu ke nan na zo nan daga Kinshasa babban birnin kasar Zaire, da a yanzu ake kira Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo.Sai da na kewaye kasar Zaire kafin na nufi Zambiya kuma daga can na iso nan.Da na zo nan sai na samu wani minista ana ce masa Mista Wakomi na ce masa ina son in bude kamfani na General African Arts . Sai ya ce to, ya tambaye ni ko ina da kudi? Na ce ina da su, ya ce suna ina? Na ce suna a banki kasar Zambiya, ya ce to ka aiko. To da na aiko shi ne na zo na bude wannan kamfani na General African Arts.
Aminiya: Wane irin ciniki wannan kamfanin ya rika yi?
Alasan: Wato ina cinikin kayayyaki kamar na fatar kada ko alabe ko belt da dai sauran kayayyaki  irin namu na gargajiya da ake sayarwa, to shine nake yi.
Aminiya: To yaya wannan ciniki ya kasance, kana yinsa ne a cikin Botswana kawai ko kana ketara iyaka zuwa wadansu kasashen?
Alasan: A’a, ina yinsa a cikin Botswana da kuma a wajenta. Wani lokaci na kan je kasashen Swaziland da Namibiya a Walbis Bay, sai in je can in sayar sai in dawo.
Aminiya: Dama ita wannan sana’ar ita ce kake yi a Najeriya har kuma ta fito da kai kasashen waje?
Alasan:  Ita ce nake yi tun a Najeriya sai na zo Zaire na ci gaba da yi. Daga nan kuma sai na karbi lasisin sayen kayan namun daji da ake ce masa ‘Produce Dealers Licence’.  To da muka zo Zambiya sai muka rika sayen hauren giwa muna aikawa Brussels ta kasar Belgium.To daga nan ne na samu kudi a Zambiya. Shine sai na aiko da kudin nan Botsawana na shiga aikin hannu.
Aminiya:  To me ya sa ka baro Zambiya ka dawo Botswana da zama?
Alasan: Cinikin hauren giwa ne ya yi kasa, ba mu samunsa, shi ya sa na dawo nan.
Aminiya: Amma kuma nan Botsawana  kasa ce da ta kai kwatankwacin fiye da rabin Najeria kuma yawancinta hamada ce, baki dayan mutanen kasar miliyan biyu ne, ba ta fi wata jiha a Najeria ba, ta yaya wannan sana’ar take biya don kila babu namun daji nan sosai?
Alasan: A lokacin da na zo nan daga Zambiya inda nike cinikin hauren giwa a nan sai na shiga aikin fata ina kaiwa kasashe kamar su Swaziland da Namibiya da Afrika ta kudu, don duk ana bukatar kayan a wadancan wuraren.
Aminiya: Ka ce wani minista na Botswana ne kuka saba har ya yi maka hanya ka samu iznin cinikinka. Ta yaya ka san shi?
Alasan: Wani jakadan Najeriya a Bots wana da ake ce masa Alhaji Zubairu, wanda ya rasu, shi ne da na zo na hadu da shi, to shi ne ya kai ni wajen ministan ciniki Mista Wakomi.
Aminiya: To da ka zauna nan ka dade haka, ka zama dan kasa ne ko kuwa har yanzu kai dan Najeriya ne, don na ji idan mutum ya zama dan kasar Botswana dole ya yafe kasarsa ta haihuwa?
Alasan: To bayan da na zo nan na bude kamfani na  jima,  sai  minista ya ce to mun ga kayanka suna da kyau, me ya sanya ba za ka zama dan kasa ba? To sai na ce na yarda zan zama. Sai suka ce to in rubuta in nema. Da na yi haka sai suka ce in kawo fasgo dina, sai suka ba ni na Botswana suka karbi nawa na Najeriya.
Aminiya: Wato yanzu ke nan kai ba dan Najeria ne ba?
Alasan: E… ni ba dan Najeriya ba ne, kodayake ina zuwa Najeriya, ba a hana ni zuwa kowane lokaci. Saboda rashin lafiyar idona ne ma yasa na rage zuwa. A da a duk shekara ina zuwa, kuma yanzu duk yawancin ‘yan uwana sun mutu, da uwa da uba duk ba su.
Aminiya: Kai kanka yanzu shekarunka nawa?
Alasan: Shekara ta saba’in da biyu.
Aminiya: To da na ji yadda kake yin turanci da alamar ka yi makarantar boko kafin ka shiga cinikin nan?
Alasan: E.. na soma makarantar, ka san makarantar tamu ta da ba kamar ta yanzu ba, amma ban yi zurfi ba, kuma da na zo nan na ci gaba da karatu ina kuma sana’a ta.
Aminiya: Me za ka ce ya bambanta Botswana da Najeriya, kamar a bangaren cinikayyar da ta zaunar da kai a nan?
Alasan: Ai ka san Najeriya uwa ce ta ko’ina a Afirka,to nan kuma ba za ka zo ka yi ciniki ba kamar yadda za ka yi a Najeriya, sai ka nemi izini, kuma sai abun da ‘yan kasa ba za  su iya ba. Lokacin da na zo nan don ‘yan kasa ba za su iya ba, shi ya sa aka ba ni damar yin wannan sana’a.
Aminiya: Yaya dangantakarka take da sauran ‘yan kasa?
Alasan: E….Ina samun girma kwarai da gaske daga gwamnati da sauran ‘yan kasa kuma suna kira na babansu.
Aminiya: To wajen iyali fa,ka yi aure a nan ko kuwa matanka ‘yan Najeriya ne?
Alasan: Na yi aure a Zambiya na zo da matata ‘yar kasar Zambiya, kuma ina da ‘ya‘ya: Da Muhammadu, wanda yanzu haka tare muka zo wannan masallaci da na hadu da kai, kuma ina zuwa da shi Najeriya; akwai kuma wata da ta mutu. Sauran kuma muna nan Gabarone tare da su, amma suna  makaranta.
Aminiya:To na ji ka tamkar wanda ake ce wa kamar ya ci kafar kare, don ba ka son zama wuri daya. Kace ka zauna a Kinshasa, a can me ka yi?
Alasan: A can ma aikin tireda muka yi har na samu lasisin ‘Tropics Dealers Permit’ ina cinikin hauren giwa.To lokacin da na zo nan na ce ina son yin wannan sana’a sai suka ce kana da lasin? Na ce e. Suka ce a ina ka samu? Na ce a Zambiya.Suka ce in kawo su gani. Da suka gani,  suka ce mu ma za mu ba ka na nan kasar.Yanzu haka ina da wannan lasin din sayen namun daji kowane iri, kuma ina ci gaba da wannan sana’a.
Aminiya: Ko cikin ‘ya’yanka akwai wanda yake wannan sana’a?
Alasan: A’a, a cikin yarana babu wanda ya gaje ni a wannan sana’a, ni kadai ne nike yi. Abin da ya sa na tsaya saboda idona, amma har yanzu ina da takardar izinin cinikin namun daji.
Aminiya: Shin ko akwai Hausawa da yawa masu zama a nan Gaborone?
Alasan: Masu zama a nan Bahaushe dai ni kadai ne. Sai wani da na zo da shi daga Tudun Wadan Zariya ana ce masa Sa’adu yana aikin surfani, to da na ga aikin ya tsaya sai na biya musu kudi su koma, amma dayan shi bai koma ba, har yanzu yana nan yana yi.
Aminiya: To kamar tun wadancan shekarun da ka zo nan zuwa yanzu ta yaya kuke zirga-zirga zuwa Najeriya? Ta mota ko ta jirgi?
Alasan: Ta jirgin sama. Amma na kan bi ta kasa, domin daga Zambiya nike shigowa in je Malawi a mota, in je Maputo ta Mozambikue a mota, kuma idan na zo nan sai in tafi Namibiya a mota, haka kuma a Afirka ta kudu ko ina zan iya zuwa a mota, in je in saida kayana in dawo.
Aminiya: A yanzu bayan da ka zama dan kasar Botswana kana kuwa tunanin komawa Najeria da zama?
Alasan: To ka san komai na Allah ne. Tun da yake na dade a nan kuma ba ni da kowa a gida sai ni kadai, babu kowa can sai dangi na nesa, kuma wadansu idan na je gidan ma ba na ganinsu.To saboda haka ni na ji dadi, ina zaune a nan ba ni da wata matsala.