Rayuwar bahaushiyar da aka fara haifa shekaru 127 a garin Ile-Ife
’Ya’yan Bahaushiyar da aka fara haifa a garin Ile-Ife sun ce, dattijuwar mai shekaru 127, takan yi wanki da tattaki na ta rabin kilomita kuma ta ji da gani sarai
Hajiya Ramatu da ake yi wa laqabi da Iyan Hamisu ita ce Bahaushiyar da aka fara haifa shekaru 127 da suka gabata a unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a garin Ile-Ife da ke Jihar Osun.
’Ya’yanta sun shaida wa Aminiya cewa, dattijuwar mai shekaru 127, duk da yawan shekarunta, amma takan yi wanki da tattaki na rabin kilomita kuma tana gudanar da kasuwanci.
Haka kuma, tana ganin komai da idanunta ta gane mutanen da suke kusa da ita kuma tana ji da kunnenta tare da yin magana da kowa.
Tarihi ya tabbatar cewa Iyan Hamisu ita ce mace ta farko da al’ummar Hausawan suka fara xaura mata aure a wancan zamani. Yau mako uku ke nan da Allah (SWT) Ya karvi ran wannan mata.
- Mulkin shekara 8 Tinubu zai yi —Doyin Okupe
- Kotu ta sallami kananan yara da ake zargi da cin amanar kasa
Aminiya ta ziyarci gidan da marigayiya Iyan Hamisu take zaune kafin rasuwarta a Unguwar Sabo Ile-Ife, inda ta taras da ’ya’yanta uku zaune a kofar gidan suna zaman makokin rasuwarta.
“Biyu daga cikin ’ya’yan nata dattijai ne masu suna Alhaji Ibrahim Abdullahi mai shekara 75 da kuma Alhaji Hamisu Abdullahi mai shekara 65 da xan autansu Alhaji Sulaiman Abdullahi mai shekara 48, wanda a gidansa Allah Ya yi mata cikawa.
Wakilin Aminiya ya samu zantawa da su a kan tarihin rayuwarta, musamman kasancewarta tsohuwar da ta fi kowa yawan shekaru kafin rasuwarta a wannan gari.
A matsayinsa na babban yaya a yanzu, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya ce “Ina zaune a birnin Kano ne amma a nan cikin Unguwar Sabo Ile-Ife aka haife ni shekaru 75 da suka gabata.
“Kuma ina tabbatar maka gaskiyar cewa kakanninmu wato iyayen mahaifiyarmu suna daga cikin Hausawan da suka sare dajin wannan unguwa ta Sabo da sarakunan gari na Yarbawa suka ba su wannan fili domin gina gidajen zama da iyali da gudanar da harkokin kasuwanci.
“An haifi mahaifiyarmu a cikin xaya daga cikin gidajen da Hausawan suka gina a wancan zamani.
“Tarihi ya tabbatar da cewa ita ce ta farko da aka fara haifa a cikin ‘ya’yan Hausawa kuma ita ce mace ta farko da aka aurar da ita ga mijinta wato mahaifinmu Alhaji Abdullahi.
“Mun samu tabbatattun bayanai cewa tabbas an sha samun savani irin na miji da mata a tsakaninta da mijinta amma tun daga lokacin da aka aurar da ita ba ta tava fita daga gidan mijin nata domin komawa gidan iyayenta da sunan yaji ba.
“Kuma bayan rasuwar mijinta shekaru 40 da suka gabata, ba ta sake auren kowa ba har zuwa yanzu da Allah Ya karbi ranta.
“A yanzu haka yawan zuriyarmu ta haura dubu xaya da suka haxa da ’ya’ya da jikoki da tattava kunne da muke zaune a garuruwa daban-daban na ciki da wajen Nijeriya. Muna ziyarta da tuntuvar juna a kowane lokaci da bukatar hakan ta samu.”
Shi kuwa Alhaji Hamisu Abdullahi cewa ya yi, “An haife ni a nan cikin Unguwar Sabo Ile-Ife shekaru 65 da suka wuce kuma na yi karatun allo da firamare da sakandare a nan Ile-Ife.
“Daga baya iyaye suka mayar da ni Kano inda suka sanya ni a Kwalejin ‘Kano Teachers College’. Bayan na kammala karatu a wannan makaranta ne na shiga aikin soja.
“Ina daga cikin sojojin da Nijeriya ta aika da su qasashen Laberiya da Saliyo domin aikin samar da zama lafiya a waxannan qasashe da suka yi yaqin basasa a wancan zamani.
“Yanzu na yi ritaya da ake biya na kuxin fansho. A game da rayuwar mahaifiyarmu, Iyan Hamisu kuwa, sai mu yi godiya ga Allah da Ya raba mu da ita lafiya.
Kyakkyawar shaida
“Ta samu kyakkyawar shaida a kan irin rawar da ta taka a lokacin da take raye musamman a tsakaninta da jama’ar gari da suka haxa da Yarbawa da Hausawa maza da mata da tsofaffi da matasa har da qananan yara, kowa yana haba-haba da ita a kan irin haquri da koyarwar da take yi wa mutane a kan rayuwa.
Lafiyarta garau
“Har zuwa lokacin rasuwar wannan tsohuwa tana yin tafiya na rabin kilomita xaya tare da ganin komai da idanunta da gane mutanen da suke zaune a kusa da ita da sauraron komai da kunnenta tare da yin magana da kowa kamar yadda nake yi da kai yanzu.”
Shi kuwa xan auta, Alhaji Sulaiman Abdullahi, wanda ake yi wa laqabi da Sule Londona ya shaida wa Aminiya cewa, “mahaifiyarmu Hajiya Ramatu Iyan Hamisu ta haifi ’ya’ya maza da mata 17 ne kuma dukkanmu uwa xaya uba xaya aka haife mu a nan Unguwar Sabo.
“Babu wanda aka haifa a wani gari daban. Wasu daga cikin ’yan uwanmu maza da mata sun riga mu gidan gaskiya tun tsohuwarmu tana raye, yanzu mu bakwai muka rage a raye.
“A matsayin xan auta ina shaida maka cewa, ni da nake zaune tare da ita a cikin gidana har zuwa lokacin da ta rasu tana gudanar da wasu ayyuka da kanta kamar xaurayar suturunta da kasuwancin qananan abubuwa a cikin gida.
“Da yake mun yi gadon sana’ar fawa ne, sai tsohuwa ta kasance tana sayar da tsinken gasa tsire da sayar da kayan miya da quli-quli da a cikin gida.”
Da yake qarin haske a wajen addu’ar sadakar kwana bakwai da rasuwar Sarkin Hausawan Ile-Ife, Limamin Babban Masallacin Sabo, Sheikh Aminu Ibrahim Imam, ya ce, “kwana xaya ne tsakanin rasuwar Sarkin Hausawa da wannan tsohuwa. Saboda haka muka yanke shawarar yi masu addu’ar tare a rana xaya.”
Malamin wanda shi ma haifaffen garin Ile-Ife ne ya ce, “wannan tsohuwa ta yi kyakkyawar cikawa domin bayanan da muka ji daga bakin magabatanmu sun nuna cewa rungumar ayyukan bautar Ubangiji (SWT) da kyawawan halayenta tun tana da quruciya da ta ci gaba da yi a gidan mijinta da bayan rasuwarsa sun isa a yi mata shaidar samun rahama Allah.”