Rayuwar ban mamaki da al’ajabi ta tagwaye masu zanen yatsa iri daya

Hajiya Ameena Hassana Sani da Hajiya Hadiza Hussaina Sani tagwaye ne masu kama da suke da zanen yatsu irin daya. Ba sa iya rabuwa da juna tun haihuwarsu a wani lokaci suna bai wa mutane mamaki bisa ga abubuwan da suke yi wanda hakan ya sa sukan bar mazansu su ci gaba da zama da […]

Rayuwar ban mamaki da al’ajabi ta tagwaye masu zanen yatsa iri daya

Hajiya Ameena Hassana Sani da Hajiya Hadiza Hussaina Sani tagwaye ne masu kama da suke da zanen yatsu irin daya. Ba sa iya rabuwa da juna tun haihuwarsu a wani lokaci suna bai wa mutane mamaki bisa ga abubuwan da suke yi wanda hakan ya sa sukan bar mazansu su ci gaba da zama da junansu. Yaya rayuwarsu ta taso wadanne abubuwan mamaki aka gani game da su?

 

Awani lokaci a 1984, ’yan tawayen matan biyu, Hajiya Ameena Hassana da Hajiya Hadiza Hussaina sun je ganin likitan hakori a Babban Asibitin Ilorin fadar Jihar Kwara. Likitar hakorin Ba’indiya ta rikice kan yadda matan biyu suke kama da juna a kusan komai, kamar yadda idonta ya nuna mata. A wannan haduwa likitar hakorin ta ci gaba da ganin abubuwan mamaki kamar yadda tawagayen suka bayyana.

A lokacin da likitar ta duba lalurarsu sai ta gane cewa matsalar tagwayen irin daya ce hakoransu ne suka yi rami kuma dukansu a gefe guda wanda turmi ne ko kuma fikarsu ce ke da wannan matsala amma dai su tagwayen ba za su iya bambance wane ne daga cikin hakoran ba.

Likitar da mijinta wanda shi ma likitan hakori ne sai suka hadu suka cire musu hakoran masu matsalar inda suka gane ba wai hakoran ne kawai iri daya ba hatta ramin da hakoran nasu suka yi ma iri daya ne zurfin ramin da kuma fadinsa duk daya ne.

“Sun cika da mamaki lokacin da suke ta kallon hakoran, suka hada su, daya daga cikin tagwayen ta ce, dayar ta yi dariya suka ci gaba da murmushi da dafa kafadar juna suna tuna irin yanayin da suka ga fuskar likitar.

Suna iya tunawa cewa bayan shekara 35 da faruwar wannan al’amarin suna ci gaba da tuna mamaki da al’ajabin da likitar ta gani.

“Mun yi kokarin mu tafi mu bar su da hakoran saboda ba su gaji da kallonsu ba suna ta mamakin hakoran da suka fito ne daga mutum biyu mabambanta,” Daya daga cikin tagwayen ta bayyana.

Suna zaune wata rana a ofishin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) inda Hajiya Ameena Hassana take aiki sanye da atamfa launin rawaya a tsakanin su akwai tebur mutane na nuna su.

Sama da shekara hamsin da suka gabata ne aka haifi wadannan tagwaye masu abin mamaki da tun daga haihuwarsu suke bai wa mutane mamaki, duk da lokacin da mahaifiyarsu Hajiya Maryam Sani ta samu ciki an tsegunta mata cewa cikin tagwaye ne amma ta musanta cewa ita ba ’yan biyu za ta haifa ba, bayan da ta haifi Ameena Hassana ta dauka shi ke nan ta gama.

“Bayan da ungozomar ta ce mata ta kwanta za ta sake haihuwa ta yi musun haka inda ta ce ita fa ta haihu ba ta tsammanin wata haihuwa kuma ta Hussaina,” inji ta.

Hajiya Maryam ta ce tana tsoron a ce ma ta ’yan tagwaye za ta haifa domin ta taba haifarsu suna mutuwa, ko kuma daya ya mutu ya bar daya.

“Mu ne ’yan tagwayen da aka haifa muka fara zama a wajen mahaifiyarmu ba mu mutu ba,” inji Ameena Hassana.

Ta ce “Hakan ya sa aka mana maki da mabambantan launi domin a bambance mu.”

Sai dai kafin su bar asibiti an gane cewa sun shaku sosai don haka ne a wannan shekarar suka ji cewa ba za su yi aure ba domin kada su rika rabuwa.

Domin idan daya daga cikinsu ta fara yin kuka haka ita ma dayar sai ta yi, a wani lokaci kuma “Muna fara yin kukan ne tare a lokaci daya haka ma idan dariya muke yi inda wannan sautin murya tamu da ke kama din take burge mutane. Idan mahaifinmu zai kira mu yana kiranmu da sunan Hajiya ne kawai domin idan ya kira duk wacce ta amsa daga cikinmu sai mahaifiyarmu ta ce me ya sa kika amsa kamar dayar,” inji Hadiza Hussaina. Ta ce, “Koda mahaifiyar tamu ta yi kokari ta rarrabe mu bai yiwuwa domin ko a waya daya daga cikinmu ta kira ta sai ta tambaya wace ce daga cikinmu.”

A cewarta a lokacin da suka isa Jami’ar Ilorin sun yanke shawarar karanta wasan kwaikwayo, kuma akwai wasan kwaikwayon da za a yi a jami’ar na wasu ’yan tagwaye amma daya ta rasu su kuma sun zo a kurarren lokaci suka nemi a kara musu wa’adin wata biyu don suyi rajista da suka shiga ofishin Shugaban Sashi (HOD), kafin su yi magana ma kamaninsu ya nuna abin da suke so saboda haka aka kara musu wa’adi suka yi rajista har aka zo suka gudanar da wasan kwaikwayon maimakon sai an sake rubutawa.

Tagwayen sun tuna wata kalma na Zulu Sofola inda idan daya ta dauko wakar sai daya ta karasa da aka gansu sai suka tuntsure da dariya suna tafawa da juna.

Suka ce da suka je Jami’ar Jos an ba su gurbin karatu a bangaren nazarin wasan kwaikwayo suka bari suka koma Jami’ar Ilorin saboda su wasan dabe suke son karantawa.

Abin takaici wannan sashi na jami’ar har ya kammala shirya wasan kwaikwayon da za a yi ta ’yan tagwayen sai daya daga cikinsu ta rasu a farkon wasan abin da ya sa aka ba su gurbi ke nan don maye wadancan.

Hakan ya sa suka je hukumar jami’ar suka bayyana korafinsu inda sashin yake da bukatar ’yan tagwayen don wannan wasa, hakan ta sa jami’ar ta kara musu wannan wa’adi domin ba su dama su yi rajista suka yi kuma yi nasara.

A wancan lokaci sai ya zama abin mamaki ganin su‘’yan tagwaye ne don hawa wancan wasa da aka shirya tun farko, inji Ameena Hassana.

Ba za ka dauki rayuwa wani abu ba don ruda mutane ba, a cewarta saboda haka zan raba tsakaninku inda daya za ta kasanace a bangaren wasan kwaikwayo daya kuma ta kasance a bangaren wakoki.

Hadiza Hussaina ta kara da cewa ita kullum sha’awarta ta yi waka haka take gaya wa ’yar uwarta sai ta yi dariya, amma zai zama da wahala a gare su wajen yanke hukunci.

Duk da cewa an raba su amma tunda suna sashi guda ne kuma dama ba sa rabuwa suna zuwa ajin karatu ne tare, inji Hussaina.

Ta ce kuma hatta iyayensu suna wahala wajen raba su idan suka yi yunkurin hakan.

Tagwayen suna da wata irin baiwa wadda idan daya ba ta da lafiya dayar ma tana kamuwa da ciwo, daya daga cikinsu ta kamu da ciwon hakori sai kakarsu ta shawarce su da suje su ga likitan hakori tare ita kuwa mahaifiyarsu ta jajirce cewa sai dai ita mai ciwon hakorin ce kadai za ta je, bayan an kai ta asibiti an dawo sai washegari dayar ma ta kamu da ciwon hakorin. Acewarta a wasu lokuta idan daya ta yi jinya aka yi mata magani tana warkewa sai dayar ta kamu da irin wannan ciwon. Haka ya sa iyayen suke ganin da sun raba su tun suna kanana da hakan bai faru ba.

“Hadiza Hussaina ta ce akan tura su wajen ’yan uwansu mabambata tun suna kanana sai kowace ta fara laulayi amma da zarar an dawo da su gida sun hadu bayan kamar minti goma sai komai ya daidaita” inji ta.

Hakan ya sake tabbatuwa a lokacin da aka tura su hidimar kasa (NYSC) jihohi daban-daban inda aka tura Ameena Hassana, Jihar Imo ita kuwa Hadiza Hussaina aka tura ta Jihar Legas.

Hakan ta sa aka kwantar da Ameena Hassana a asibitin Nekede, Hadiza Hussaina kuma aka kwantar da ita a wani asibiti a Legas mahaifiyarta ta kasance tare da ita.

“Mun gwada raba su tun suna yara amma hakan ya gagara, haka muka hakura” inji ta. Hakan ya sa wani kawunsu ya roki Hukumar NYSC ta hada su a waje guda suna ganin juna.

Bayan ba sa rabuwa wani abu da aka gano shi ne tagwaye ana samunsu da nau’in jininsu daban-daban amma wadannan nasu iri daya ne, Ameena AS Hadiza AS kuma dukansu ajin jinin ma iri daya ne.

Bayan sun gama hidimar kasa a gidan Talabijin na Kasa (NTA) tagwayen sun samu kansu a fagen wasan kwaikwayo inda suka samu daukaka.

’Yan tagwayen suna bai wa mutanen gari sha’awa a duk lokacin da aka gan su a hanya.

Hajiya Hadiza, ta ce duk da cewa ba abin da suka so karantawa a jami’a aka ba su ba, amma har yanzu suna sha’awar kasancewa a gidan jarida, amma dai suna kuma bukatar shirya wasan kwaikwayo da ba sai sun bayyana a ciki ba.

Lokacin da suka samu labarin tsohon Daraktan Gidan Talabijin na Kasa (NTA), Yaya Abubakar ya zama Shugaban Rediyon Muryar Najeriya sai suka garzaya ofishinsa suna neman aiki, duk da kasancewa sun taba aiki a karkashinsa a NTA lokacin suna hidimar kasa inda daya kawai yake gani daga cikinsu bai san cewa tagwaye ba ne sai da suka zo gabansa duka su biyun.

“Kuna son ku ce min ku tagwaye ne mutum biyu ne ku ba daya ba” Yaya Abubakar

ya tambaye su. Sai tagwayen suka sheke da dariya.

Lawal Yusuf Saulawa, wani dan jarida abokin aiki sai ya tabbatar wa Yaya Abubakar cewa ai shi yana ganinsu duka amma ba a lokaci daya ba, hukumar gidan ne ta yanke shawarar ba za ta ajiye su a sashi daya ba, inda Hadiza Hussaina aka kai ta sashin labarai ita kuma Ameena Hassana aka kai ta sashin shirye shirye amma hakan bai taimaka ba.

“Da wani ya ga Ameena Hassana a saman beni ni kuma ya gan ni a kasa, sai ya yi ihu ya ce Jesus (Yesu),” inji Hadiza wai bai dauka mu biyu ba ne.

Ta kara da cewa a wani lokacin idan aka bai wa Ameena Hassana aiki idan suka gan ni sai a ce ba ke na bai wa aiki jiya ba, na ce ki yi abu kaza ba ki yi ba. Nakan ce musu ba ni ba ce ’yar uwata ce, amma ba sa yarda sai su ce me ya sa zan yi musu haka.

Ita kuma Ameena cewa ta yi wani lokaci idan aka gan ta sai a ba ta takarda a ce ta yi abu kaza, sai ta dauko ta bai wa Hadiza ta ce wani a sashinsu ya ce ta yi abu kaza.

Bayan kamar shekara daya da rabi suna wajen sai Ameena Hassana ta samu aikin banki za ta tafi, har ila yau kuma irin hakan ya sake faruwa a lokacin da za su tafi karo karatu don yin digiri na biyu a Jami’ar Ilorin, saboda yadda take son darasin lissafi Ameena ta zabi sashin kasuwanci da mulki, ita kuwa Hadiza ta zabi harkar mulki inda suka yi watanni shida ba sa tare. Ameena ta dan samu tsaiko ne saboda bankin da take aiki suna da ka’idoji da sai an bi kafin su bar mutum ya tafi karo karatu.

Da zarar Ameena ta bullo don fara nata karatun sai malaman jami’ar da suka karantar da ita watannin shida da suka gabata sai suka dauka ita ce za ta sake yin wani darasin a lokaci guda, lokacin da shugaban sashin gudanarwa ya ziyarce ta a gida wata rana tare da maigidanta a nan ne ya gane ashe tagwaye ne ba mutum daya ba ne.

 

Abin da Allah Ya hada aure ma ba zai raba ba

Koda yake dukkansu yanzu suna aiki ne a gidajen jaridu sun zabi su yi aiki a wurare daban-daban ne don su daina rudar da jama’a, inji Ameena da take aiki da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) kuma aikin nasu yana da matukar muhimmanci a gare su.

“Duk abin da ya shafe mu ya shafi tsare-tsarenmu sannan a dukan lokuta maza ba sa fahimtarmu saboda yana da wahala su gane, idan mace ta tashi a aiki kokari take yi ta tafi gida ta bai wa ’yar uwarta labarin abin da ya faru a wajen aiki.

Idan ina sauraron wata hira da suka nada a faifai ba na bambance wace ce ta fara amma dukansu ne suke kammala shi, da na gane ba sa zuwa aiki musamman tare da maza ’yan Arewa sai na zana musu layi su ci gaba da zama tare, layin da nake nufi na zana musu sai na raba su da mazaj aure domin su zauna tare.

Kamar matan Arewa dalilin aurar da su shi ne don su zauna tare amma wadannan tagwayen su damuwarsu ita ce su zauna tare da junansu.

Ameena ta yi karin bayani cewa addini Musulunci ya bayyana cewa ba lallai ko dole ba ne a yi aure idan mutum zai iya kiyayewa ya kame kansa.

Rayuwar tagwaye ta fi wahala domin kowa kwansa ake yi daban, amma su kwai daya ne aka raba shi biyu tunanin daya yana wajen daya, inji Hadiza Hussaina.

Bayan marmarin kasancewa tare sannan su dawo gida su bai wa juna labarin abin da ya faru a wajen aiki a wannan ranar tagwayen da ba sa rabuwar tunaninsu shi ne su bai wa

’ya’yansu tarbiyya tagari, Ameena Hassana tana da ’ya’ya uku ita kuwa Hadiza Hussaina tana da ’ya’ya biyu, a tsakaninsu suna da jikoki shida da suke fatan su kasance tare cikin rayuwa mai nagarta.

Wani abin al’ajabi shi ne dukan mahaifan ’ya’yan nasu wato mazansu sun rasu ba da dadewa ba bayan sun rabu da su.

Ba su da wata matsala a tsakaninsu da ’ya’yansu amma sun fi shakuwa da jikokinsu inda har suka sake samun wasu jikokin ’yan tagwaye, Hassan da Hussaini, inda ita Ameena Hassana ta dauki Hassan ita kuma Hadiza Hussaina ta dauki Hussaini.

Wani abin mamaki shi ne a lokacin da jikokin nasu Hassan da Hussaini suka kai shekara daya da rabi idan suna rarrafe Hassan bai taba yin rarrafe ya shiga dakin Hadiza Hussaina ba, haka shi ma Hussaini bai taba rarrafe ya shiga dakina ba, inji Ameena Hassana.

Wata rana da yammaci daya da cikin jikokin Hassan da Hussaini sai ya fara waka yana oyoyo oyoyo kafin ya ga alamarta tana dawowa yana wakar kafin minti goma sai aka ga daya daga cikin kakannin nasa daya ta shigo.

Zanen yatsun hannu

Sama da shekaru zanen hannu akan yi amfani da shi ne wajen bambance mutane domin kowa da irin nasa amma batun na Ameena da Hadiza ba haka yake ba.

“Muna da zanen hanu iri daya mun kuma gane hakan ne a shekarar 2011 lokacin da muka je yankan rajistar zabe,” inji Hadiza Hussaina.

A zahirin gaskiya kwararru sun tabbatar da cewa hakan yana faruwa ne ga mutum daya a cikin mutum miliyan 64 amma tunda yanzu ana da mutane biliyan bakwai ne a duniya hakan ya sa ba a cika samu ba hakan ya sa wadannan tagwaye ma ba a san da nasu ba.

Har yanzu kuma ban tabbatar da za a samu wadansu mutum biyu da suke da irin wannan zanen yatsu iri daya ba. Lokacin yin rajistar tagwayen sun zauna kusa-da-kusa ne da juna.

“Ni aka fara daukar hoton yatsuna da bayanaina ina kokarin matsawa waje na gaba sai ’yar uwata a lokacin da ake kokarin daukar nata hoton yatsun sai kwamfutar ta fara wani iri ta ki daukar nata,” inji Hadiza Hussaina.

“Sai suka fara tambayar dasta don na goge yatsuna,” inji Ameeena, sai suka kwashe da dariya dukansu.

Suka kalle mu duka zuwa wani dan lokaci sai za a sake daukar hoton yatsunta a cewarta, sai kwamfutar ta sake kin karbar hoton yatsunmu ba mu dauka wani abu ba ne da hakan dai suka lallaba suka dauki hoton yatsun nata.

A lokacin da katin ya fito suka je karba sai ya kasance sunan Hadiza Hussaina ne kadai ya fito ba katin kuma, “Sunana ne ya fito na ta bai fito ba sai muka tambaya me ya faru har dai zuwa wannan lokaci ba mu dauka wani abu ba ne,” inji ta.

“Ba mu samu gamsasshen bayani ba a kan ko me ya faru ba sai bayan wasu shekaru da muka hadu da Shugaban Hukumar INEC ta Kasa a wajen wani taro muka tambaye shi muka nuna masa shaidar katin na wucin-gadi da aka ba mu sannan Shugaban ya gamsu sai dai a binciken da ake yi an gano kwamfuta ta ki karbar yatsun Ameena ne saboda zanen yatsunta ya yi daidai da na ’yar uwarta,” inji su.

Haka ma suka sake samun matsala da katin shaidarsu ta zama dan kasa inda aka fara daukar bayanan Hajiya Hadiza Hussaina amma daga baya ya ki karbar bayanan Hajiya Ameena.

Wani abu shi ne sun yi ta bibiyar katin zabensu har zuwa yanzu inda aka jiran su dangwala dan yatsa su karba, katin shaidar dan kasa kuma har yanzu suna kan jira.

A yanzu da suke shekara hamsin da haihuwa tagwayen suna kokari ne wajen ganin ba su ruda mutane ba a bangaren iyaye da ’yan uwa da abokai har mda abokan aiki ba, haka wajen daukar bayanai da kuma zanen hannu suna ta kokarinsu na ganin ba su sa wani ya rude a kansu ba.

A wani lokaci da muke yara idan muka kalli hotunanmu mu kanmu muna kasa gane junanmu inda muke jayayya da juna wajen ce wa ni ce nan, ni ce can da muka gane hakan sai ya zama muna gaya wa juna cewa me ya sa muke kama da juna, domin ko mura ne tare muke yi idan daya ta yi atishawa dayar ma za ta yi a daidai wannan lokaci haka muka lura komai tare muke yi.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta