Rayuwar Duniya: Labarin Malam Shagalalle (2)

Ya masu karatu, Assalamu alaikum! Bayan haka, muna yi wa masu karatu maraba da sake saduwa a wannan fili. A makon jiya ne muka faro wannan labari na rayuwa, wanda ke dauke da wasu darussa da za su kaifafa mana tunani, sannan su yi mana jagora game da rayuwar nan tamu ta duniya. Yau za […]

Rayuwar Duniya: Labarin Malam Shagalalle (2)

Ya masu karatu, Assalamu alaikum! Bayan haka, muna yi wa masu karatu maraba da sake saduwa a wannan fili. A makon jiya ne muka faro wannan labari na rayuwa, wanda ke dauke da wasu darussa da za su kaifafa mana tunani, sannan su yi mana jagora game da rayuwar nan tamu ta duniya. Yau za mu dora daga inda muka tsaya, Allah Ya sa mu dace da alheri, amin. Mu sha karatu lafiya:

Yana ta bin matar nan kuma yana ta yin tunani iri daban-daban. “Shin wannan mata wace ce ita? Kila ’yar wani hamshakin attajiri ne. To, me ya kawo ta cikin kasuwar nan, me take nema?” Saurin da yake yi ya fara wuce misali, ya soma gudu-gudu, kuma bai damu da cewa cikin kasuwa yake ba, mutane kuwa suna kallonsa, shi kuwa bai ma kula da haka ba. Burinsa guda daya ne – ya samu isa wurin matar nan, wacce ta kara kudewa zuwa wata shiyyar kasuwar.

Mutumin nan dai ya hanzarta bin matar nan, ita kuwa sai kara yi masa nisa take, yana gani ta karya kwana ta shiga shiyyar masu sayar da kayan fada, kamar su takobi, bindigar gargajiya, kwari da baka, garkuwa da sauransu. Yana saurin bin bayanta dai amma kafin ya isa wurin sai ya ga ta karya kwana ta shiga bangaren masu sayar da man girki. Ya bar bangaren masu sayar da makamai, sai ya ga matar nan ta shiga bangaren masu sayar da fatu da kiraga. Ta dai yi masa nisa sai kara sauri take, shi ma sai kara azamar bin ta yake yi cikin sauri har da sassarfa.

“To, amma me ya sanya wannan matar ta ki tsayawa, sai ci gaba da tafiya take? Ko dai mahaukaciya ce?” Tambayoyin da mutumin ya rika yi wa kansa ke nan, kuma bai tsaya domin ba kansa amsa ba sai ya ci gaba da bin bayanta. Bai tsaya da bin ta ba har sai da ta fita daga cikin kasuwar, ta shiga cikin gari. Suka ci gaba da tafiya dai, tun suna cikin gari har dai matar nan ta fita zuwa bayan gari. Shi kuwa gogan naka yana ta wahalar bin ta zagai-zagai.

Kash! Masu karatu, za mu diga aya nan, sai kuma mako na gaba, inda za mu ci gaba da wannan mashahurin labari. A ci gaba da biyo mu, domin ci gaba da amfana da darussan da ke zizara mana sinadaran rayuwa. Allah Ya yi mana jagora, amin.

 

 

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos