Rayuwar guragun Abuja a baca bayan shekara 15 da alkawarin gina musu mazauni
Guragu da sauran nakasassu da Ma’aikatar Kula da Birnin Tarayya Abuja ta yi alkawarin samar musu da matsuguni a kauyen Karmajiji da ke wajen birnin, sun koka da matsalar rayuwa musamman a bangaren muhalli. Aminiya ta ziyarci yankin a karshen mako, inda ta zanta da Sarkin Nakasassun Abuja, Alhaji Muhammad Sulaiman Katsina da kuma wadansu […]
Guragu da sauran nakasassu da Ma’aikatar Kula da Birnin Tarayya Abuja ta yi alkawarin samar musu da matsuguni a kauyen Karmajiji da ke wajen birnin, sun koka da matsalar rayuwa musamman a bangaren muhalli.
Aminiya ta ziyarci yankin a karshen mako, inda ta zanta da Sarkin Nakasassun Abuja, Alhaji Muhammad Sulaiman Katsina da kuma wadansu daga cikin mukarrabansa.
- 2023: ‘Gwamnonin APC na son daya daga cikinsu ya gaji Buhari’
- Sojoji sun cafke dan kasar wajen da ke taimaka wa ’yan ta’adda a Sakkwato
Alhaji Muhammad Katsina ya ce a baya suna zaune ne a wurare irin su Garki Village da Eriya 1 da New Market da ke cikin kwaryar Birnin Abuja, kafin a kawo su yankin a zamanin Ministan Abuja Malam Nasir El-Rufai wanda saukarsa daga mulki tare da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya haura shekara 15 a yanzu.
Sarkin ya ce gwamnati ta kai su wajen ne a matsayin zaman wucin-gadi kafin ta yi masu gini a wani wuri na dindindin da ke yankin Dobi kusa da Gwagwalada, Abuja.
Fili kawai aka nuna mana
“A lokacin da aka kawo mu nan, daukacin yankin nan ba komai sai gonaki.
“Akwai dai tsohuwar Karmajiji da ke kusa da babban titin da ya nufi filin jirgin sama na Abuja inda ’yan asalin yankin Abuja wato Gwarawa suke zaune, su ne kadai wadanda muka samu a can gefen titi a lokacin da gwamnati ta kawo mu nan,” inji shi.
Ya ce koda gwamantin ta kai su wajen ba ta yi musu komai ba in ban da nuna masu wajen kasancewar ta ce za ta gina masu gidaje a yankin Dobi da ke Gwagwalada.
“Kusan duk wanda ka gani a nan a cikin bacan kwano yake ba ma yin na katako don gudun gobara,” inji shi.
Ya ce wajen ya kunshi dukkan masu larurar nakasa da ta hada da guragu da makafi da kutare da kurame da sauransu.
Aminiya ta gano cewa ban da fadar sarkin, kusan duk gidajen na baca ne, inda a wani zubin ake samun magidanta hudu a gida guda.
Malam Ibrahim Sagir mai sayar da kayan kwalliyar mata, shi ne shugaban ’yan kasuwa a fadar Sarkin Guragun, ya ce ba wanda yake da sha’awar yin gini a wajen koda yana da halin hakan, saboda gwamnati ta ajiye su a wajen ne a matsayin na wucin-gadi.
Ya ce magidanta ba su wuce dari ba a lokacin da aka kai su wajen, “Sai dai a yanzu magidanta kadai sun haura 500 kuma ba a maganar ’ya’yansu da suke tare da su”.
Da yake bayani kan matsalar rayuwa a cikin bacocin, Malam Ibrahim ya ce, “Ka ga na farko akwai yoyon daki a lokacin damina, ga daukar zafi da rana sannan yanayin sanyi a lokacin hunturu shi ma babu dadi, akwai kuma saurin lalacewa na cin kasa daga kasa.”
Ya ce hakan na jawo rashin jituwa a tsakanin mazauna waje guda a-kai-a-kai.
Ya ce yawancin rigingimun Sarkin ne yake warware su, a yayin da wanda ya shafi na mata zalla kuma Jakadiyarsa mai suna Rahina Haruna ke zuwa gidaje ta warware.
‘Mu muka gina wa ’ya’yanmu makaranta’
Daga cikin abubuwan tallafa wa rayuwa da ke wajen akwai makarantar boko da Sarkin ya ce su ne da kansu suka fara aikin ginin har aji hudu, kafin wata kungiya mai zaman kanta ta karasa masu zuwa aji shida, sannan Hukumar Ilimin Firamare ta Karamar Hukuma (L.E.A) ta dauki nauyin malaman makarantar a yanzu.
Da yake karin haske, Sarkin ya ce akwai karamin asibiti da Karamar Hukumar Birnin Abuja ta gina kamar shekara biyu ke nan inda iyalansu ke zuwa idan suka samu rashin lafiya.
Idan abin ya fi karfin wajen ne suke zuwa asibitoci kamar na Wuse ko Maitama da ke cikin gari.
Aminiya ta gano cewa daukacin tallafi da al’ummar suke samu yana zuwa ne daga bangaren kungiyoyi masu zaman kansu.
Daya daga cikinsu ita ce wata cibiyar koyar da sana’a da ta hada da dinki da kwamfuta da kade-kade da sauransu wadda ya ce wani dan Cif Rochas Okorocha mai suna Enem ya yi masu.
Haka shi kansa Cif Rochas Okorocha yana zuwa ya tallafa masu ta gidauniyarsa mai suna Rochas Care.
“Haka kuma akwai rijiyar burtsatse da masallaci da wani bawan Allah ya gina mana, baya ga taimakon da muke samu daga kungiyoyi musamman a lokutan azumi da Sallah da sauran bukukuwa,” inji shi.
Ya ce wadansu daga cikinsu suna gudanar da sana’o’insu ne a cikin kwaryar birni kuma iyalansu na zaune a nan, kuma suna zuwa makaranta.
Muna bukatar marakarantar sakandare
Malam Ibrahim ya bukaci agajin hukuma kan sama masu makarantar sakandare a yankin don saukake masu kudin mota da suke biya ga masu zuwa wurare masu nisa don yin karatun a kullum.
Ya kuma bukaci a gyara masu motar bas da uwargidan marigayi Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa, Hajiya Turai ta saya masu a lokacin mulkinsu.
Ya ce suna amfani da motar ce wajen zirga-zirgarsu ta yau da kullum, ciki har da kai majinyata kamar mata masu nakuda zuwa asibiti, kafin motar ta durkushe.
Sarkin ya bukaci Ma’aikatar Birnin Tarayya ta cika masu alkawarin da ta dauka na gina masu muhalli a filin da ta ware masu don saukake masu rayuwa.
Kamar ’Yangoje, mu ma a waiwaye mu
“Gwamnati ta yi wa kutare nasu na musamman a yankin ’Yangoje da ke Karamar Hukumar Kwali;
“Zan yi amfani da wannan dama don yi mata tuni a kan namu alkawarin da a yanzu ya shafe sama da shekara 15,” inji Sarkin.
Tuni yankin ya tumbatsa da tarin gine-ginen na sauran al’umma, inda ya hade da yankuna sauran al’ummar gari.
“A gefe guda unguwar ta Guragu na iyaka da wani sashi na makabartar sojoji ta kasa sai kuma gonakin ’yan asalin Abuja.”
Da Aminiya ta tuntubi Babban Daraktan Sashin Kula da Walwalar Jama’a na Hukumar Birnin Tarayya, Abuja Malam Sani Amar don jin ta bakin gwamnati, ya ce yana halartar wani zama inda ya yi alkawarin tuntubar wakilinmu bayan taron.
Sai dai har zuwa lokacin bai yi hakan ba, inda walinmu ya sake tuntubar sa ta waya a ranar Talatar makon jiya, amma babu amsa.