Rayuwar mahaifinmu ta qare ne wajen yi wa addini da al’umma hidima – Alqali Salisu Tureta

Aqali Salisu Abubakar Tureta babban xa ne ga Sheikh Abubakar Tureta wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Lahadin da ta gabata. A  zantawarsa da Aminiya, ya bayyana cewa rayuwar mahaifinsu ta kare ne wajen yi wa addini hidima.   Ka gabatar mana da kanka? Ni ne babban xan Sheikh Abubakar Tureta kuma ina […]

Rayuwar mahaifinmu ta qare ne wajen yi wa addini da al’umma hidima – Alqali Salisu Tureta
Rayuwar mahaifinmu ta qare ne wajen yi wa addini da al’umma hidima – Alqali Salisu Tureta

Aqali Salisu Abubakar Tureta babban xa ne ga Sheikh Abubakar Tureta wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Lahadin da ta gabata. A  zantawarsa da Aminiya, ya bayyana cewa rayuwar mahaifinsu ta kare ne wajen yi wa addini hidima.

 

Ka gabatar mana da kanka?

Ni ne babban xan Sheikh Abubakar Tureta kuma ina da shekara 51 a duniya. Kasancewar shi Malam Abubakar Tureta malami ne da ya duqufa wajen karantar da addini a tsari irin na karatun zaure kusan karatuna na farko a wajensa na fara. Saboda haka shi ne babban malamin da ya karantar da ni a duniya. 

Kuma tun daga lokacin da aka haife ni ba mu tava rabuwa da shi na tsawan wata guda. Saboda haka a koda yaushe muna tare da shi. 

Vangaren karatu malam ya yi karatu ta vangare daban-daban kama daga kawunsa wanda yake qauyensu zuwa Zamfara da Sakkwato da Gusau daga nan kuma ya zo Zaria. Makarantar malam Na’iyya na daga cikin mahimman wurin da ya yi karatu. 

 

‘Ya’yan malam da ya bari nawa ne?

Mu 39 ne kuma jikoki yana da 84 masu rai. 

 

 Ya yi fama da jinya ne kafin rasuwarsa?

Eh, ya yi fama da jinya. Ya tava samun haxarin mota, tun dai daga wannan haxarin ne. Ya kai shekara uku da wannan haxari amma har ya kai ga bai iya motsawa.

Amma kuma wani abin mamaki da bamu mancewa a lokacin da malam ya samua haxarin mota ya tafi wani aiki ne na addinin musulunci a Jigawa. Bai kai ga zuwa aikin ba ya yi haxarin.

Kwance cikin mota ya ce a kai shi sai ya aiwatar da wannan aiki. Sai da ya je ya yi wannan aiki ya gama. Domin irin qwadayi da yake da shi na ayyukan addinin musulunci. Duk wanda ya san rayuwarsa, ya san cewa ya qare rayuwarsa ce kan kula da addini da xaukar nauyin al’umma. 

A sanina idan ba ‘yan shekarun nan ba, ko fanka malam bai da shi. Bai tava mallakar na’urar sanyaya xaki ba. Kuma shimfixarsa ba ta wuce tabarma da bargo ba.

Idan ka shigo sai dai duk gefensa litattafai ne. Amma wani abu na jin daxi kamar firiji bai tava saye ba ko ya mallake.

 

Wani hali kake ganin sauran al’umma musulmi za su yi koyi da shi daga halayen malam?

Halayensa ta ko wani vangare abin koyi be. Vangaren karatu abin koyi ne,vangaren aiki da karatun abin koyi, jajircewa da abin da ya sa a gaba bin koyi ne. 

 

Wane abu za ka riqa tunawa da shi a zamanka da Malam?

Eh, toh ni babban abin da zan iya tunawa da ba zan mantawa ba shi ne jajircewar da ya yi a kaina ya sa da ina so da bana so sai da na bi hanyar da ya bi. Kuma ina godiya domin ina tsammanin yanzu ya kai shekara biyar hatta makaranta ni ke riqe da ita, kuma karantun da yake bayarwa ni ke yi. 

Wannan shi ne abin da ya yi min wanda ba zan tava mantawa ba.  Ka ga banda abin mantawa sai dai in ci gaba da yi masa Addu’ar Allah Ya gafarta masa.