Rayuwar Matasa a Dandalin Abota na Intanet (1)
Asalin wannan makala wata lacca ce da na gudanar a taron shekara na TSANGAYAR ALHERI a Makera Motel, da ke kan titin Daura a Katsina, ranar Asabar Janairu 5, 2013Ray Lam dai wani matashi ne a birnin bancouber ta Jihar British Colombia da ke kasar Kanada; ya kamala karatun jami’a, ya kuma yi ayyuka sosai […]
Asalin wannan makala wata lacca ce da na gudanar a taron shekara na TSANGAYAR ALHERI a Makera Motel, da ke kan titin Daura a Katsina, ranar Asabar Janairu 5, 2013
Ray Lam dai wani matashi ne a birnin bancouber ta Jihar British Colombia da ke kasar Kanada; ya kamala karatun jami’a, ya kuma yi ayyuka sosai wajen ganin ci gaban rayuwarsa. Ganin haka tasa ya yi tunanin shiga siyasa, don kawo sauyi a mazabarsa. Nan take ya dukufa da yakin neman zabe, jama’a suka ta zagaye shi: “Sai ka yi…sai ka yi…sai ka yi,” kamar dai yadda ake yi wa ‘yan siyasar mu a yau. Ya shahara sosai, har abokan hamayyarsa suka fara neman yadda za su kayar da shi, amma abu ya ci tura. Sai ta hanyar Dandalin Facebook suka ci nasara.
Yana da shafi, inda yake kamfe a dandalin, wanda ke cike da hotunansa na zamanin samartaka. Daga ciki akwai wadanda ya dauka yana dafe da kirjin budurwarsa a gidan rawa ana holewa, da kuma wadanda ya dauka masu bayyana al’aurarsa. Nan take suka dauko wadannan hotuna suka yi ta rabawa; ana mannawa a wurare. Wannan ya rage masa shahara, da cewa, ashe dan iska ne, har yana bayyana tsaraicinsa ga duniya. Wannan bai kamata ya zama shugaba ba. Wannan ya tilasta masa fita daga jerin ’yan takara, abokan hamayyarsa suka samu nasara a kansa. Babban dalili shi ne, katobarar da ya yi wajen dora hotunansa marasa kyau, masu nuna rayuwarsa ta baya, wanda hakan ya kai shi ya baro .
Jama’a, ina mana barka da shigowa wata sabuwar duniya a cikin wannan duniya tamu, wadda har yanzu ba mu gama sanin hakikaninta ba. Duniya ce mai cike da annashuwa, da raha, da saukin rayuwa, da saukin mu’amala, da saukin sadarwa, da saukin yin abota, da hanyoyin samun fadakarwa, da hanyoyin gabatar da fadakarwa, da sauran hanyoyin gabatar da harkokin rayuwa a wani tsari mai kama da hakika. Kai, ba kama ba ce, rayuwar hakika ce, sai dai a wani irin yanayi mai cike da mamaki, irin wanda ke wautar da fahimtar dan adam. Domin a yayin da wannan sabuwar duniya ta mu ke bamu wadancan hanyoyi na farin ciki da annashuwa da bayaninsu ya gabata, har wa yau dai ita ce ke cike da abubuwan mamaki na bakin ciki, da damuwa, da shagwaba, da rudi mara iyaka, da wasu munanan halaye masu jefa mutum cikin irin halin da matashi Ray Lam ya samu kansa a ciki, kamar yadda kuka ji a farko.
Wannan duniya dai ba wata ba ce, illa sabuwar duniyar da ci gaba a fannin kimiyyar sadarwa da fasahar sarrafa bayanai ta tsunduma mu ciki tsundum, daidai gab da karshen karnin da ya gabata. Wannan ita ce sabuwar duniyar tsarin sadarwa ta Intanet, wadda a farkon lamari ta faro da ‘yan kwamfutocin da ba su shige 100 ba, amma a halin yanzu akwai sama da biliyan uku masu dauke da bayanai da muke aikawa a tsakaninmu. Samuwar fasahar Intanet da yadda bunkasarta ta kasance abu ne mai cike da mamaki ga duk wanda ya san asalin lamarin, amma bai kai irin mamakin da ke dauke da sabuwar duniyar da ta tsiro a cikinta bayan ’yan shekaru kasa da 10 da suka shige ba. Wannan duniya dai Jama’a, ita ce duniyar gamewar mu’amala a muhallin sadarwa. Daga kowace nahiyar duniya a yau jama’a sun game, sun zama daya; suna samun sanayya a tsakaninsu. Wannan ta kai ga samun natsuwa, da kuma ruduwa, inda aka wayi gari jama’a suka sake; komai na rayuwarsu ma suna iya bayyana shi; cikin rubutu ne, ko hotuna ne, ko zane ne, ko murya ce, ko kuma hoton bidiyo ne mai motsi. Ba abin da ya shafe su. Wannan shi ne irin rudin da ya jefa matashi Ray Lam cikin halin da ya samu kansa. Ta yaya wannan sabuwar duniya ta tsiro daga muhallin giza-gizan sadarwa ta duniya?
Samuwar Dandalin Abota a Intanet
Tsarin samar da bayanai a Intanet ya kasu kashi biyu. Tsarin farko shi ne tsohon tsari; wato hanyar samar da bayanai ta gidan yanar sadarwa. Wannan shi ne tsohon yayi, kuma shi ne abin da a farkon zamanin mu’amala da fasahar Intanet ya shahara. Da tafiya tayi nisa, harkar kasuwanci ta fara habaka a duniyar Intanet, sai ‘yan kasuwa suka shiga binciken sanin hanyoyi ko irin bukatun da masu sayen hajojinsu a Intanet ke da su ko suke bi. Wannan ta sa aka fara kirkirar gidajen yanar sadarwa ko mudawwanai masu bai wa mai ziyara a gidan yanar sadarwa damar fadin albarkacin bakinsa kan hajar ko abin da yake so ko yake sha’awa. A daya gefen kuma sai ga manyan gidajen yanar sadarwa – irin su Yahoo!, da MSN, da Google – sun kirkiro hanyoyin da masu ziyara ke haduwa suna tattaunawa kan bukatunsu na rayuwa, da dandanonsu kan rayuwa, da abubuwan da suke bukata, da dai sauran abubuwan da suka shafe su. Hakan kuwa ya samu ne ta hanyar Majalisun Tattaunawa da Zaurukan Hira (wato Cyber Communities – ko “kauyukan Intanet”), wadanda kuma suka hada da Groups, da Internet Chat Rooms, da Communities, da kuma Bulletin Board ko Forums. A wadannan wurare, masu karatu da masu ziyara da masu saye da sayarwa ne ke tattaunawa a tsakaninsu kan bukatunsu da dandanonsu. Kuma wannan tsari, a harshen Kimiyyar Sadarwa ta Zamani, shi ake kira User Content; wato tsarin samar da bayanai ta hanyar mai ziyara. Samuwar wannan tsari ne har wa yau, ya haifar da samuwar ire-iren dandamalin abota da ake da su a Intanet a yau, irin su Facebook, da NetLog, da JHoos, da LinkedIn da dai sauran makamantansu.Wadannan su ake kira Social Networking Sites .
A mahangar Kimiyyar Sadarwar Zamani, idan aka ce“Social Network” ana nufin dandalin shakatawa ne da yin abota. Wuri ne ko ka ce “Dandali” ne da ke hada mutane daga wurare daban-daban, masu launi daban-daban, masu harshe daban-daban, daga wurare daban-daban, masu matsayi daban-daban, masu matakin ilimi daban-daban, kuma masu manufofi daban-daban.Haduwar wadannan mutane a “muhalli daya” shi ke samar da wani dandali budadde, mai kafofi daban-daban, inda kowa ke zabar abokin huldarsa ta hanyar masarrafa ko manhajar kwamfuta da aka kirkira a irin wannan dandali. Kafin mu yi nisa, yana da kyau masu sauraro su san cewa, wannan dandali ba wani abu ba ne illa wani gidan yanar sadarwa ne na musamman da wasu ko wani kamfani ko mutum ya samar don wannan manufa. Manufar a farko ita ce samar da muhallin da mutane za su tattauna da juna ta hanyar yin abota da yada ra’ayoyinsu kan wasu abubuwa da suke sha’awa. Wannan manufar asali ke nan. Amma a yau wannan manufa ta sauya nesa ba kusa ba. Akwai manufar kasuwanci, da yada manufa ta siyasa ko addini, da samar da hanyoyin bincike kan dandanon mutane da ke dandalin .
Za mu ci gaba