Rayuwar Matasa a Dandalin Abota na Intanet (3)

Asalin wannan makala wata lacca ce da na gabatar a taron shekara na TSANGAYAR ALHERI a Makera Motel, da ke kan titin Daura a Katsina, ranar Asabar Janairu 5, 2013 Idan muka dawo Nahiyar Afirka, kasashen da suka fi mu’amala da Dandalin Facebook su ne: Masar (mutum miliyan 12.1), da Najeriya (mutum miliyan 6.7), da […]

Rayuwar Matasa a Dandalin Abota na Intanet (3)

Asalin wannan makala wata lacca ce da na gabatar a taron shekara na TSANGAYAR ALHERI a Makera Motel, da ke kan titin Daura a Katsina, ranar Asabar Janairu 5, 2013

Idan muka dawo Nahiyar Afirka, kasashen da suka fi mu’amala da Dandalin Facebook su ne: Masar (mutum miliyan 12.1), da Najeriya (mutum miliyan 6.7), da Afirka ta Kudu (miliyan 6.4), da Maroko (miliyan 5), sai kuma Aljeriya (miliyan 4).  A bangaren dandalin Twitter kuma, kasar Afirka ta Kudu ce a gaba da yawan sakonni sama da miliyan 5 a shekarar 2011.  Sai kasar Kenya da sakonni sama da miliyan 2.  Sai kuma kasarmu ta gado Najeriya, mai sakonni sama da miliyan 1.6.  A Nahiyar Afirka, kashi 57 na sakonnin Twitter da ake aikawa duk ta hanyar wayar salula ne.  
Kashi 60 cikin 100 na masu amfani da Dandalin kuma duk matasa ne ’yan shekara 20 zuwa 29. kididdiga kuma ta tabbatar da cewa duk masu rajista a Dandalin Twitter, suna da rajista a Dandalin Facebook, da Youtube da Google+ da kuma LinkedIn.  A duniya gaba daya, kashi 23 cikin 100 na masu mu’amala da shafukan abota a duk rana matasa ne. Kuma kamar yadda bayanai suka gabata, matasa sun fi shawagi a Dandalin Facebook, saboda kebantattun siffofin da yake da su.  Don haka, sauran bayanan da ke tafe kan tsarin mu’amalar matasanmu a dandalin abota na Intanet, za su takaita ne kan wannan dandali.
Sana’ar matasanmu a Dandalin Facebook: A bayyane yake cewa, akwai matasanmu da yawa a Dandalin Facebook; tsakanin ’yan mata da samari da tsofaffi da zawarawa da gwagware da tuzurai, duk sun yi rajista kuma suna sada zumunci iya gwargwado. Babban abin da ya saukake yaduwarsu a wannan dandali kuwa dalilai ne guda biyu.  Abu na farko, shi ne, samuwar wayar salula a hannun jama’a, wadda ta game gari da duniya baki daya.    
Abu na biyu, shi ne, saukin mu’amala. Shafin Facebook yana da saukin mu’amala.  Wannan ya sa duk wanda ya shiga sau daya ko sau biyu, ba ya bukatar wani darasi kuma.  Cikin amfanin da matasanmu ke samu a Dandalin Facebook akwai sadarwa da yin abota da samar da sanayya mai amfani da amfanarwa da fahimtar rayuwa, ta hanyar kallon yadda wasu ke tafiyar da rayuwarsu a duniyar da suke. Akwai kuma samartaka tsakanin ’yan mata da samari da koyon addini da siyasa da raha da fadakarwa da ma sambatu.
A daya bangaren kuma, akwai majalisu da matasanmu suka kafa masu amfani sosai. Akwai zaurukan tattaunawa na musamman masu amfani su ma. Akwai kuma shafukan gwaraza da suka bude don koyi da su ko karantarwarsu.  Akwai zaurukan zumunta na musamman. Wasu daga cikinsu sun hada da: Zauren Sahabban Manzon Allah (mambobi 7,608) da Dandalin Marubuta (7,292), da Tsangayar Alheri (4,570), da Dandalin Ilimantarwa da Nishandantarwa (1,614) da Dandalin Tsaraba daga Mimbarorin Jumu’a (1,392), sai Dandalin Tambayoyin Musulunci (273).  Sauran sun hada da: Dandalin Zauren Sunnah (2,845) da Dandalin Buhariyya Zalla (10,293) da Dandalin Siyasa (5,283), da Dandalin Iyantama (13,377), sai kuma Dandalin Dariya (8,801).  A banganren shafukan gwaraza, kuma akwai shafin Sheikh Dokta Mansur Sakkwato (mutum 5,707) da shafin marigayi Sheikh Ja’afar (mutum 23,670), sai zaure na musamman mai take: Zauren Malam Ja’afar (10,454). Duk wannan adadi, tsakure ne cikin daruruwan shafuka da zaurukan da matasanmu suka bude kuma suke aiwatar da sadarwa a tsakaninsu a wannan dandali.
A daya bangaren kuma, wannan dandali ya bai wa matasanmu wata sabuwar hanyar fadakarwa da karantarwa da tunatarwa da kuma gayyata. Wannan tsari ya samar da wata hanya ta gayyatar biki, ko suna, ko taro, ko duk wani sha’ani na yau da kullum. A bangaren siyasa ma haka abin yake; kowa na bayyana ra’ayinsa yadda yake so, ba tare da tsangwama ba.  Wadannan kadan ne daga cikin nau’ukan amfanin da matasa ke samu a wannan dandali.
Manyan kalubale:
A duk inda aka ce samari da ’yan mata sun hadu, a yanayin da ba a ganin juna, a yanayi mai jefa hankali da zuciya wata nahiyar nishadi mai girma, to, dole a samu ’yar karkata.  Domin tatsuniyar Gizo, kamar yadda muka sani, ba ta wuce koki.  Daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar matasanmu a wannan dandali, shi ne, na rashin alkibla a galibin lokuta, musamman a shafukansu.  Wannan ke sa a kashe lokaci ana lilo a shafin Facebook, amma in ban da sambatu ba abin da ake yi.  A daya bangaren kuma muna yawan ruduwa da hotunan ’yan mata, wadanda suka fi yawan abokai a shafukansu su ne mata, a duk fadin Dandalin Facebook.  Dalilin hakan kuwa ba sai na gaya muku ba.  Su kansu ’yan matan sun fahimci haka.  Wasu daga cikinsu kan loda hotunan da ba nasu ba, musamman idan ba kyawawa ba ne su. Idan ka ga irin yabon da samari ke yi kan hotunan ’yan mata, kare ba zai ci kalaman ba.  
kalubale na gaba, shi ne, rashin kiyaye sirri. Kowa da irin tsarinsa a rayuwa, amma wannan ba ya nufin komai na rayuwarka sai ka bayyana wa jama’a a shafinka ba. Kada mu manta da lamarin marigayiya Cynthia, wacce wasu samari suka ruda a bara, a karshe suka yi mata fyade, suka kuma kashe ta bayan sun gayyace ta birni Ikko, tun daga Jihar Nasarawa.  Da yawa mukan rubuta sirrin rayuwarmu, mu loda hotunan sirri a shafinmu da duk abin da ya shafe mu, ba tare da tunanin cewa, wani na iya dauka ya sarrafa su don wata mummunar manufa ba. Bayan haka, mu fadaka; akwai jami’an leken asiri na gwamnati da na barayi, masu neman inda rauni ko sakaci yake, don tattaro bayanai kafin su aiwatar da aikinsu, mummuna ne ko mai kyau.  Galibin lokuta har wa yau mukan sanar da duniya jujjuyawarmu a shafinmu.  Wannan akwai kuskure a ciki, iya gwargwadon matsayinmu a rayuwa. Da yawa cikin ta’addancin da ake aikatawa a zamanin yau, tsakanin kasashen Turai da namu, masu yin hakan na samun bayanan ne ta hanyar Dandalin Facebook.
Daga cikin kalubale da ke fuskantar matasanmu a Dandalin Facebook akwai matsalar yaudara da karya wajen bayyana asali da tarihi a shafi. Wannan matsala ce mai girma. Da yawa cikinmu kan rubuta cewa, mun yi makaranta a kasa kaza, ko mu mazauna kasa kaza ne, alhali watakila ko kwaryar jiharmu ba mu taba bari zuwa wata jiha ba.  Wasu kuma mazaje ne, amma sai su bude shafi na musamman da sunan mata da hotunan mata, har da lambar waya na bogi. Duk wannan bai kamaci mutum natsattse mai dattako ba. Su ma ’yan mata suna da nasu. Yaudara cikin zance da yaudara cikin hotuna.  Wasu kan loda hotuna masu motsa tsimin namiji, don su ji me za a ce. Duk wannan bai kamata ba. Manyan dalilan da ke haddasa su su ne: sakakkiyar ’yanci da rashin tarbiyya da yawan ruduwa da kyale-kyale da kuma rigima wajen latse-latse. Da yawa cikin mutane a wasu kasashe sun rasa rayuwarsu, wasu sun rasa dukiyarsu, wasu sun rasa mutunci da darajarsu, wasu kujeru da mulkinsu, duk ta sanadiyyar latse-latse marasa kan-gado a shafin Facebook. Wadannan kadan ne daga cikin kalubalen da ke fuskantar matasanmu kan abin da ya shafi mu’amala da juna a Dandalin Facebook.
Hanyoyin Gyara:
Ga dukkan alamu wannan tsari na rayuwa a Dandalin Abota da ke Intanet wani abu ne da ya zo, kuma akwai tabbacin ya samu gindin zama musamman a zukatan matasa. In kuwa haka ne, to dole a kullum a nemi hanyoyin gyara cikin tafiyar, tunda tafiya ce doguwa. Bayan dogon nazari da bincike kan irin nau’ukan wauta da sakaci da ganganci da gidadanci da tumasanci da kauyanci da ke faruwa a Dandalin Facebook, tashar talabijin ta hukumar Kanada mai suna CBC, cikin wani shirinta na musamman mai take: Facebook Follies, ta nemi shawarar Mista Graham Cluly, daya daga cikin manyan ma’aikatan kamfanin SOPHOS, kuma shahararre a hanyoyin kariyar bayanai da tsarin sadarwa a kwamfuta da Intanet, dangane da hanyoyin da jama’a za su bi wajen samun natsuwa a Dandalin Facebook, sai ya fara da cewa: “Facebook ba kyauta ba ne, domin sun fi ka riba ma, duk da cewa kana ganin kyauta kake komai a ciki, ba ka biyan kudi.  To, amma ya kamata mutane su san cewa, duk abin da ka latsa a shafin Facebook, ko ka rubuta a shafinka ko a shafin wani, ko ka “so” (like), ko duk wani hoto da ka loda ko bidiyo, duk kudi ne a gare su.  A takaice ma dai, kai ne hajar da masu shafin Facebook ke tallatawa.”
Graham Cluly ya ci gaba da cewa: “Ya kamata kuma mu san cewa, duk abin da ka rubuta shi a shafin Facebook, ko wani hoto da ka loda a shafin, to, ka rasa shi ke nan har abada.  Domin ba ka da wani iko a kansa. Wani na iya dauka ya yi duk abin da yake so a kai.”Abin da wannan batu ke nufi shi ne, in dai kana da wani abu da ka san sirri ne na rayuwarka; hoto ne, bayanai ne, kasida ce, bidiyo ne, sauti ne, to kada ka loda a shafin Intanet.  Domin kamar ka kai kasuwa ne ka ajiye, duk wanda ya yi masa, zai iya tayawa.  Shi ya sa a gaba Cluly ya ci gada da cewa: “Muddin ka san ba za ka iya zuwa tsakiyar kasuwar garinku ka daga murya kana gaya wa jama’a sirrin rayuwarka ba, to, ko kadan kada ka rubuta ko loda su a shafin Facebook.  Duk abin da ka san ba ka son kowa ya sani, kada ka rubuta shi a shafin Facebook.” Wannan sakon a fili yake, ba ya bukatar sharhi.
Dangane da abin da ya shafi yin amfani da shafin Facebook wajen aikata miyagun ayyuka da laifuffuka kuwa, Graham Cluly ya ce: “Dandalin Facebook ne shafin miyagun laifuffuka da ayyukan yanar gizo da ya fi saurin habaka a duniya yanzu. Akwai satar bayanan sirri da yada kwayoyin cutar kwamfuta da aikata miyagun ayyuka da laifuffuka da ake yi a Dandalin Facebook fiye da kowane irin shafin Intanet a duniya.Idan kana son zuwa babbar matattarar ’yan ta’addar yanar sadarwar duniya a yanzu, to ka je Dandalin Facebook.” Wani mai sharhi kan harkokin sadarwar Intanet ya sanar da Umar Shehu’Yanleman, wakilin BBC Hausa da ke Legas, cewa: “Mu’amala a shafin Facebook lalube a cikin duhu ne. Ba ka san abu ba bai sanka ba. Ba ka ganshi ba, bai ganka ba.”  Wannan shi ne hakikanin gaskiya wanda babu tantama  a cikinsa.
Kammalawa:
A karshe, rayuwar matasanmu a Dandalin Facebook abu ne da ya zo, kuma za a dauki tsawon lokaci yana tare da mu. Abin da ya rage kawai shi ne neman hanyoyin gyara dabi’u da tarbiyyar kai da manufa kakkarfa da kiyaye sirri da kaffa-kaffa da miyagun abokai da kamewa daga sha’awa mara kan gado da kuma tsantseni.  Wadannan su ne manyan guzurin da suka kamata duk wani mai shawagi a duniyar Intanet na zamanin yau ya rike su, don samun isa masauki lafiya lau. Allah Ya yi mana jagora, amin.