“Rayuwar Shettima na cikin hatsari, a saya masa sabon jirgi”

Kakakin ya dole ne a sauya wa Shettima jirgi don kaucewa shiga halin-ha’u-la’i.

“Rayuwar Shettima na cikin hatsari, a saya masa sabon jirgi”

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya ce rayuwar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima na cikin hatsari sakamakon jirgin saman da yake hawa ya tsufa.

Lawan ya bayyana hakan ne, bayan da Shettima ya soke tafiyarsa zuwa taron Samoa.

An dakatar da tafiyar ne bayan da wani abu ya daki jirgin Shettima a New York.

Abin da ya doki jirgin, ya lalata wasu sassa na jirgin, ciki har da gilashin gaban matuƙin jirgin.

Lawan, ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta samar wa Shettima sabon jirgi don gujewa jefa rayuwarsa cikin hatsari.

Ya ce jirgin Mataimakin Shugaban Ƙasar ya fuskanci matsaloli da dama a baya, kuma ba a yi wani abu ba har yanzu.

“Ina miƙa jajena ga gwamnatin Najeriya, musamman ma ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa da tawagarsa kan abin da ya faru a birnin New York,” in ji Lawan.

“Haka kuma ina gode wa Allah bisa ceton rayuwar Mataimakin Shugaban Ƙasa da dukkanin waɗanda ke cikin jirgin.”

Ya ƙara da cewa, ya kamata gwamnatin Najeriya ta gudanar da bincike game da abin da ya faru a filin jirgin sama na JFK.

Lawan ya jaddada cewa rayuwar Shettima da ma’aikatansa na cikin hatsari saboda jirgin tsoho ne, kuma ya jima yana bayar da matsala.

Tun farkon wannan shekara, majalisar wakilai ta bayar da shawarar a siyo sabbin jirage ga Shugaba Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima, sai dai iya Tinubu aka saya wa sabon jirgin.