Rayuwar ’yan gudun hijirar Najeriya a Nijar
Kimanin ‘yan gudun hijira 6, 000 ne daga Jihar Barno suka ketara zuwa karamar Hukumar Bosso da ke lardin Diffa ta kasar Nijar don neman mafaka tun bayan da aka fara farautar ‘yan bindiga da sojojin Nijeriya ke yi a wadansu kauyukan da ke yankin jihar ta Barno.‘Yan gudun hijirar, kamar yadda bincike ya nuna, […]

Kimanin ‘yan gudun hijira 6, 000 ne daga Jihar Barno suka ketara zuwa karamar Hukumar Bosso da ke lardin Diffa ta kasar Nijar don neman mafaka tun bayan da aka fara farautar ‘yan bindiga da sojojin Nijeriya ke yi a wadansu kauyukan da ke yankin jihar ta Barno.
‘Yan gudun hijirar, kamar yadda bincike ya nuna, sun fito ne daga kauyukan Tumbun-Dabino da dankatsina da Karaka da Dogon-Marya da Malam-Fatori da Tumbun-danjuma da ke karamar Hukumar Abadam ta Jihar Barno. Wadansu kuma sun fito ne daga garuruwan Kukawa da Mobar da Guzamala, duk dai a jihar ta Barno.
Garin Bosso karamar hukuma ce a lardin Diffa da ke kasar Nijar amma kuma kimanin tafiyar kilomita uku ne zuwa kauyen Malam-Fatori da ke karamar Hukumar Abadam a Jihar Barno.
Binciken da Aminiya ta yi ya nuna cewa, a yayin da mafi yawan ‘yan gudun hijirar ke ketarawa ne zuwa kasar Nijar ta kananan hanyoyin ratse ta cikin dajin da ke tsakanin kasashen biyu, samari daga cikinsu kuwa suna ketarawa ne a kan Babura. Sannan kuma an gano cewa wadansu daga cikin samarin suna zuwa ne da yamma su kwana a can sai kuma da safe su koma garin na Malam-Fatori.
ketarawar ‘yan gudun hijirar ta ta’allaka ne da yanayin da matanen kauyukan suka samu kansu, inji daya daga cikin ‘yan gudun hijirar, Malam Yunusa Ali. Ya kara da cewa, “a duk lokacin da aka samu afkuwar wani al’amari na tashin hankali to mutane da yawa sukan gudu ne kasar ta Nijar, amma idan da akwai kwanciyar hankali sai ka tarar cewa mutane na zaune a gidajensu.”
“Amma dai mutane da yawa sun ketara zuwa Nijar a ranar Asabar da ta gabata a sakamakon shawagin da jiragen yaki guda biyu suka rika yi a tsakanin iyakokiin Nijeriya da Nijar. Jami’an tsaron Nijeriya har yanzu suna farautar ‘yanbindiga a wadansu kauyuka na karamar hukumar Abadam ta jihat Borno. Daga lokaci zuwa lokaci za ka rika jin karar harbe-harbe da fashewar bama-bamai a yankunan da ake tsammani maboyar ‘yan bindigar ne. A ranar Asabar din da ta gabata jiragen yakin guda biyu sun harba bama-bamai a wajajen kauyukan Tumbin-Dabino da dankatsina da Karaka,” inji dangudun hijirar.
Wata ‘yar gudun hijira mai suna Malama Halima Abdullahi cewa ta yi, “mun yi tafiya a kafa tun daga Malam-Fatori zuwa garin Bosso domin mu kare rayuwarmu da ta ‘ya’’yanmu. A gaskiya ba mu san abin da zai faru da mu ba idan har muka kuskura muka tsaya a kauyen Malam-Fatori , domin ko a ranar Juma’a da ta wuce sai da ‘yan bindiga suka kashe wani jami’in ‘yansanda da wani farin kaya a kauyen, saboda haka ne muka gudu zuwa Bosso.”
“Duk mun bar dukiyoyinmu a garin na Malam-Fatori, mun ketaro ne da ‘ya’yanmu da suturunmu. Mata da kananan yara sun sha matukar wahala, amma ba mu da yadda za mu yi, illa dai mu bar kauyukanmu don tsira da rayukanmu sakamakon irin ukubar da muka ji ta fara da mutanen Baga. Ba za mu so sojojin su huce haushinsu a kanmu ba,” inji ta.
Malam Muhamma Ibrahim, wanda shi ma wani dan gudun hijira ne, ya shaida wa Aminya cewa,
“Mahaifiyata ce ta umarce ni da in gudu daga garin Malam-Fatori zuwa Bosso a ranar da aka kashe jami’in ‘yansandan. Mun samu labarin cewa wanda aka kashe din jami’in CIB ne na ‘yansanda. Mutane da dama sun gudu zuwa Nijar a wannan rana.”
Ya kara da cewa, “mun zo garin Boso ne a kan Babura amma za mu koma a yau domin mu ga yadda iyayenmu suka kwana. Idan mun ga babu matsala to za mu zauna a can, amma idan mun ga har yanzu akwai alamun tashin hankali za mu dawo nan Bosso tare da dukkanin iyalanmu.”
Amimiya ta lura da cewa ‘yan gudun hijirar suna kwana ne tare da mutanen Bosso a cikin gidajensu ba a cikin sansanoni ba. An karkasa su ne zuwa unguwannin Duwani da Mairi-Unguwar-Sarki da Unguwar-Mahauta da kuma Balagama, duk a cikin garin na Bosso. Kamanin ‘yan gudun hijira 50 zuwa 60 ne ke kwana a gida daya.
Da yake zantawa da Aminiya, Magajin Garin Bosso, Alhaji Bako Mammadou ya ce, “mun yanke shawarar karbar ‘yan gudun hijirar Najeriya ne don su ma ‘yan uwanmu ne. Gwamnatinmu ta taimaka musu sosai kuma za ta ci gaba da taimakonsu matukar za su zauna da jama’armu lafiya.”
Mammadou ya kara da cewa, “a lokacin da muka fuskanci ‘yan gudun hijirar na karuwa sai muka nemi gwamnati da ta kara samar da ruwan sha don gudun yankewarsa, wanda a domin haka ne gwamnati ta umarci ma’aikatar ruwa da ta kaddamar da aikin samar da ruwan sha da aka yi a nan a Bosso wanda a sakamakon haka yanzu ruwa ya wadata a garin.”
“A kididdigar da muka gudanar mun gano cewa sama da mutane 6, 000 ne suka ketaro daga kasar Nijeriya zuwa Bosso a makonni biyu kawai. Kodayake ba wai mun kebe musu wurin zama ba ne a garin nan ba, amma mun umarci jama’armu da su ba su wurin kwana a gidajensu. Sai dai duk da haka wadansu na kai-komo ne a tsakanin Bosso da kauyukansu a Najeriaya. Kuma mun gayyaci kungiyar agaji ta Red Cross domin ta taimaka wa ‘yan gudun hijirar, inda ta taimaka musu da kayayyakin abinci da na sakawa. A yanzu haka kimanin ‘yan gudun hijira 1, 500 ne suka karbi taimako daga kungiyar.
‘Yan gudun hijirar sun ce har yanzu ba su samu gudummuwa daga gwamnatin Jihar Borno ko ta tarayyaba kwanaki bayan da suka gudu zuwa kasar ta Nijar.
Iyani Sani, wadda ta koma Bosso da ‘ya’yanta shida, ta shaida wa Aminiya cewa, har yanzu ba su samu wani tallafi daga gwamnatin Najeriya ba kimanin makonni biyu da komawarsu Bosso daga Malam-Fatori.
Ta ce yanzu haka tana zaune a gidan kanwarta ce tare da ‘ya’yanta Salisu daYusuf da Bakiru da Fatima da Abudullahi da Amina, tana mai cewa, “dukkaninmu nan muke ci muke sha tare da kanwata da ‘ya’yanta. Amma har yanzu ba mu samu wani taimako daga Gwamnatin Borno ko ta tarayya ba.”
Aishatu Muhammad Melfo, ta shaida wa wakilinmu cewa an kwantar da mata da yawa a asibiti a garin Diffa sakamakon wahala da suka sha lokacin gudun hijira zuwa Bosso. “Mun sha matukar wahala, domin tafiya ce wadda ba mu shirya mata ba kuma ga yara da ‘yan kayayyakinmu da muka taho da su. Gaskiya tafiya ce mai ban tausayi domin mun galabaita ainun.’’
Ita maMaimuna Audu, cewa ta yi, saura kiris ta haihu a daji a lokacin da take gudun hijira zuwa Nijar daga karamar hukumar Abadam ta Jihar Barno.
Al’amarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 2013 a lokacin da Maimuna take kan hanyarta ta zuwa garin Bosso na kasar Nijar daga kauyansu na Malam-Fatori a karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.
Aminiya ta gano cewa, an sallami Maimuna daga asibiti da ke a garin Diffa a ranar 22 ga watan na Mayu bayan da akayi mata aiki aka cire dan da ke cikinta. Da Maimuna da dan da ta haifa duk suna cikin koshin lafiya a lokacin da wakilin Aminiya ya ziyarce su a Unguwar-Mauhata a garin na Bosso.
‘Yan gudun hijirar dai sun ce sun koma kasar Nijar ce domin kare rayukansu da kuma neman abin da za su ci, suna musu bayyana cewa, “ba mu da abincin da za mu ci a kauyukanmu kuma ba mu son sojoji ko ‘yanbindiga su kashe mu.”
Mafi yawan ‘yangudun hijirar da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana cewa a yanzu haka akwai matsalar rashin abinci a kauyukansu. kauyukan da abin da ya shafa sun hada da dan-Katsina da Malam-Fatori da Kanikaram da Kaiyakaru da Afulori da Melfo da Tunbum-Dabino da Dogon-Marya da kuma Tumbun-danjuma, inji wani dan gudun hijira Umar Grema.
Grema ya shaida wa Aminiya cewa, mafi yawan mata da kananan yara sun gudu daga kauyukansu sun bar ‘yan samari da tsofaffi da dabbobi kawai.
Ya ce wadansu sun koma Nijar ne domin su zauna a can, wadansu kuwa neman abinci kawai yake kai su, domin sukan dawo kauyukansu da marece. Ya ce ko wadanda ake bari a kauyukan nasu suna ta’allaka ne da Biredi da gyada da gari a matsayin abincinsu, kuma wadannan kayan ma ana kawo su ne daga garin na Bosso.
Ya kara da cewa, “bayan haka fulani makiyaya sun barnatar mana kayan gonakinmu da muka shuka. Makiyayan sun yi amfani da halin da muke ciki suka kora shanunsu cikin gonankinmu suka cinye duk amfanin goanakinmu a kauyuka da dama.”
Grema ya bayyana cewa, ko da bayan an kare wannan fitina to hakika mutanen kauyukan da abin ya shafa za su fuskanci matsanancin rashin abinci a sakamakon barnatar mana da amfanin gonanakinmu da Fulani suka yi. A saboda haka ya dace gwamnati ta yi wani hobbasa don yin rigakafi tun kafin al’amarin ya faskara.
Ya ce a rashin shige da ficen motoci a kauyukan da abin ya shafa ya taimaka gaya wajen kawo karancin abinci a kauyukanmu, yana mai cewa, ‘’a yanzu haka ba a shigo da kayan abinci daga sauran kauyukan da ke makwabtaka da mu ko kuma daga kasar Nijar wanda hakan ya kara dagula
al’amurra. “Mu dai muna kaiwa da komowa ne a tsakanin Malam-Fatori da Bosso a kullli-yaumin. Muna tafiya ne da safe mu kuma dawo da yammaci. Muna dawowa ne domin kulawa da ‘yan kayyakin da muka bari a kauyukanmu, saboda ba zamu iya tafiya da su can Bosso ba sakamakon rashin shige da ficen motoci.
Shi ma da yake zantawa da Aminiya, Malam kasim Bukar, wani matukin mota da yake kaiwa da komowa tsakanin Bosso da kauyukan Bornon, ciki har da Malam-Fatori, ya ce a yanzu haka sun daina shiga Najeriya saboda matsin lamba da suke fuskanta daga jami’an tsaro a shingayen bincike a kan hanyarsu ta shiga Najeriya.
Bukar ya ce, “sai ka tsaya a kimanin shingayen bincike kimanin 30 don a yi maka bincike kafin ka isa garin Malam-Fatori, kuma a wadansu lokuta sai ka bayar da cin hanci kafin su barka ka wuce da kayan da ka dauko. To kaga idan har ka ci gaba da haka to babu shakka ba za ka fuskanci wani abin kirki ba a sana’ar taka. A karshe dai mun yanke shawarar daina zuwa Najeriya daga Bosso.”
Hafsatu Alhaji danfulani, wata ‘yar gudun hijira ce, ta shaida wa Aminiya cewa, “mun koma kasar Nijar ne domin neman abin da za mu ci saboda ba mu da abin da za mu ciyar da ‘ya’yanmu. Muna kashe N1, 800 a harkar abinci a kullum. Domin idan muka tsaya a Malam-Fatori ba za mu samu abincin da za mu ci ba.”
Ta ce mijinta ba ya gari a lokacin da aka yanke shawarar ketarawa kasar Nijar, amma sai ya umarce ta da yin hijrar tare da sauran mutanen kauyen nasu. Ta kara da cewa, ya aiko mata da kudi ta hannun abokinsa Malam Ibrahim Musa. Ta ce, “a yanzu haka na kama daki a kan kudi Naira 1, 000 a wata a Unguwar Mahauta.”
Ta kara da cewa,“Akwai kimanin matan aure ‘yan gudun hijira guda 20 da yara 50 da kuma magidanta 15 a nan a Gidan Babani. Mata da kanan yara muna barci ne a tsakar gida, su kuma magidanta sukan yi ne a filin Allah Ta’ala a kofar gida. Na kuma samu labarin cewa akawai matan aure kimanin 30 a Gidan Ali Gangama da Yara 60 da kuma magidanta maza guda 17,” Inji ta.