Rayuwar ’yan kama-wuri-zauna a Abuja
A cikin unguwar kuma akwai masu zama tare da matansu da ’ya’yansu. Wani za ka samu ya yi baca daki guda daya amma tare suke kwana ciki da ’ya’yansa da matarsa.
Yawanci idan aka ambaci rayuwar Babban Birnin Tarayya, Abuja, musamman ga wanda ba mazaunin birnin ba, abin da ke zuwa ransa shi ne rayuwa mai cike da wadata da walwala da sukuni da kuma ingancin ababen more rayuwa fiye da sauran sassan kasar nan.
Sai dai kuma ga yawancin mazauna Abuja, ma’aikata da ’yan kasuwa da dangoginsu, kallon kitse ake wa rogo. Abin da ya fi ci musu tuwo a kwarya shi ne batun muhalli. Domin kuwa, irin muhallin da suke ganin ya dace da su, ko irin wanda suke zaune a garuruwansu, ya fi karfinsu a Abuja, saboda tsananin tsadar kudin haya, baya ga tsadar rayuwa a birnin.
Bincike ya nuna cewa hauhawar farashin kayan gini, karancin tsari a bangaren gine-gine masu saukin kudi, da kuma rashin aiwatar da tsare-tsaren gidaje na gwamnati sun jefa mutane da dama—musamman ma’aikata masu karamin albashi da masu kananan sana’o’i—a mawuyacin rayuwa a wuraren da ba su dace da zama ba.
Ba Abuja kadai ba, gidajen haya musamman na masu karamin karfi sun yi karanci sosai musamman a manyan birane, inda kudin haya ya yi tashin gwauron zabo. Wannan ya tilasta wa mutane da dama rayuwa cikin gidaje marasa kyau, wasu ma a cikin wurare marasa tsaro da tsafta.
Wannan ya sa yawancinsu ke rayuwa a muhallai mai inganci, kamar cikin kango ko baca— gidajen wucin gadi da aka gina da katako ko rufin kwano, wansunsu ma a matsayin na haya. Mazauna irin wadannan matsugunan wucin gadi suna fama da yawan rusau daga hukumominn gwamnati, wanda ke tilasta musu tashi, baya ga ayyukan rashin da’a kamar sace-sace da rashin tarbiyya, da ake dangantawa da rayuwar bariki.
Ma’aurata da ’ya’yansu na kwana a ɗaki daya
Alhaji Jamilu Adamu, wani ma’aikaci daga Zariya da ke zaune a Abuja, ya siffanta wa Aminiya yadda unguwar da yake zaune take, halin da ake ciki da kuma yadda ke rayuwa a cikin baca a unguwar.
“Ina tsakiyar birnin Abuja a wata unguwa wadda akwai matsakaita da masu karamin karfi. Gidaje ne da aka yi su katako ko langa-langa, aka yi su babu tsari, babu makewayi. Kawai duk wanda ya zo zai samu wuri ne ya gina iya wurin da yake so.
“Abin da ake nufi da baca shi ne daki ko gida da aka yi shi da galan-galan ko da katako ko kwalaye. Yawanci an fi samun nasu karamin karfi a wannan unguwa, wanda za ka ga wasu kamar leburori ne, wasu sai da daddare suke dawowa su kwana a ciki, amma da rana duk za su fita daga unguwar.
“Unguwa ce da kamar ba su ma san ko gwamnati tana yin wasu ayyuka ba, su dai suna zuwa ne su samu matsuguni inda za su iya kwana a ciki. A cikin unguwar kuma akwai masu zama tare da matansu da ’ya’yansu. Wani za ka samu ya yi baca daki guda daya amma tare suke kwana ciki da ’ya’yansa da matarsa.
“Wani lokaci ko ruwa sai sun je nesa za su yi amfani da shi; haka ma idan za su yi wanka ko wani abu da sauransu, duk ba su damu da wannan ba.”
‘Dole ta sa mu zama a baca’
Baya ga tsadar kudin haya, a cikin garin Abuja, kudin hayar daki guda kan kai kimanin Naira miliyan guda a wasu unguwanni. Wasu masu gidajen ma ba sa karbar kudin shekara guda, sai shekara biyu ko fiye. Baya ga haka, ana yawan samun karin kudin haya.
Wani dan haya a Abuja ya ce, “Sai ka gama hada abin da za ka tara a shekara za ka biya kudin haya da duka, ka shiga sabuwar shekara kuma ka fara nema,” domin biyan na shekara mai zuwa.
A kan haka ne a shekarar 2022 aka gabatar da kudirin dokar wajabta takaita biyan kudin haya zuwa wata shida-shida a Abuja domin sama wa ma’aikata da masu karamin karfi sauki, amma lamarin ya gamu da cikas.
Wani mazaunin baca a Abuja ya ce, “Kama gida ba wai babban gida ba a cikin gari, na mai karfi ne. To sau tari su kansu wadannan dakuna da kake gani irin na katako wasu haya suke yi. Wasu su suka buga katako da leda, a sa kwali, a dan gyaggyara ciki, muhalli dai inda ruwa ba zai zuba ya jika ka ba.
“Wasu kuma suna ɗan samun wakilan unguwa da suke ɗan wuri da suka dan fara tara mutane, su ɗan nemi alfarma, su ɗan bada na goro, sai a ɗan yanka musu inda za su dan buga baca.”
Wani dan haya a baca a unguwar Jabi daki biyu da ke kwaryar birnin Abuja, ya ce, “Duk wanda ya ce maka shi yana so ya kare rayuwarsa dindindin a irin wannan dakin ya yi maka karya. Saboda wuri ne da ake yin rayuwa iya daidai karfi ne, amma duk wanda ya zo ya gani, ya san cewa irin wannan wurin bai kamata a ce dan-adam ne yake kwana a cikin irin wurin ba.”
Da wakilinmu ya tambaye shi yadda yake ji game da rayuwarsa a baca, ya sai ya ce baca ya fi, idan aka kwatanta da masu kwana a bakin titi ko a kofar shaguna. “Alhamdu lillahi tunda dakin da nake ba ya zuba, kuma kayana suna saye. In na tashi zan iya kulle kofata in tafi sabgogina, idan na dawo na san inda zan kwanta; ya fikwana a bakin titi ko irin kasan wani abu haka.”
Yaya makewayin mazauna baca yake?
Ko yaya mazauna baca suke yi idan ruwan sama ko iska ta taso, yaya kuma suke biyan bukatunsu idan ta taso musu a irin wadannan dakuna marasa makewayi? Wani mazaunin unguwar Jabi daki Biyu ya ce gidan wanka suke zuwa su biya domin biyan wadannan bukatu.
“Gaskiya sai na fita waje na je na yi wanka sakamakon babu fili a daidai wurin. Ba yadda za a yi ko da sarai, iya na wanka za a yi, ba za mu iya tona sokawe mu yi bandaki a wurin ba. Dole sai mun fita mun je gidajen wanka da aka dan yi a gefe, muna biya mu yi wanka, mu dan biya bukatunmu a wurin mu dawo.
A yanayin damina kuwa, ya ce, “Idan ana ruwa da iska, za ka shiga wani yanayi saboda jijjigawar wurin, kana tunanin iska za ta iya dauke wurin a koyaushe. Kana cikin tunani, sai an dauke ruwan sannan hankalinka zai kwanta. Sau tari idan wani wurin ya dan jika sosai, ka san leda da kwali, to idan ta dan narke, sai ka dan nemo tsumma kana ajiye a wurinka, don inda kake kwance ya jike.”
Rusau na hana ’yan baca sukuni
Baya ga haka mazauna suna cikin zullumin yiwuwar tashinsu ko yin rusau daga hukumomin gwamnati.
“A shekara biyar da na yi a wannan unguwar, an yi rusau akalla sau shida, kuma yawanci ’yan baca take shafa,” in ji wani dan kasuwa a garejin Utako da ke makwabtaka da unguwar Jabi daki Biyu, wadda ke da bacoci da kuma gidajen bulo.
Shi ma wani mazaunin unguwar ya ce, “A cikin azumin nan aka fara rusau a Filin Ball, bayan kwana biyu kuma a sake dawowa aka yi. Duk kayan da ke dakina ’yan bola sun kwashe a lokacin da masu rusau suka zo.
Wasu na danganta yawan rusau a Abuja da bukatar masu fili na gina filayensu da aka gina bacoci a kai, wani lokaci kuma zargin ayyukan bata-gari da hukumomi ke zargin cewa yawanci a baca suke zama.
“Da duk wurin nan da kake gani bacoci ne, sun fi dakuna 100, amma da aka zo rusau aka murkushe su. Da unguwar nan sai a hankali, duk irin sharholiyar da kake tunani ko bata-gari, za ka iya samu, maza da mata. Wasu a nan suke zama wasu kuma zuwa suke yi su yi harkokinsu su koma inda suka fito. A da, ko cewa ka yi a Jabi daki Biyu kake, sai an sake kallon ka, saboda yadda unguwar ta yi kaurin suna.”
Matsayin doka kan muhalli
Wani masanin shari’a, Barista Yusuf Salau Aminu Mutum Biyu ya ce, “Lallai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya yi bayani a kan hakkin dan kasa kuma alhakin da ke kan gwamnati ta tabbatar da cewa an samar da matsugunai masu sauki da nagarta ga ’yan kasa, sawa’un fili ne ko kuma gidan kansa, ko wani wuri daban.”
Sai dai ya bayyana cewa babu wani karfi na doka da ke bai wa mutum damar kai kara kai tsaye kan rashin samar da gidaje daga gwamnati. A maimakon haka, kungiyoyi da kungiyoyin farar hula ne ke da damar matsa lamba ko kai kara domin ganin an samar da wadannan hakkoki.
Bayanin masana tsara birane
Masana tsare-tsaren birane sun bayyana cewa daya daga cikin hanyoyin magance matsalar gidaje shi ne samar da ingantaccen tsarin gine-gine ga birane da ma karkara. Sai dai, sun bayyana cewa rashin bin wannan tsari na daga cikin manyan matsalolin da ke haddasa rikice-rikicen gine-gine da kuma karuwar unguwannin da ba su da tsari.
Wani masani a fannin, Tanko Lana Muhammadu Lawal Ubale, ya ce rashin isassun ma’aikata, kayan aiki da kuma kudade na daga cikin kalubalen da hukumomin tsare-tsaren birane ke fuskanta. Haka kuma, ya zargi wasu daga cikin jama’a da rashin bin doka, inda suke gina gidaje ba tare da izini ba.
Ya ce irin wadannan gine-gine kan haifar da matsaloli kamar toshe mgudanan ruwa, rage fadin tituna, da kuma kkara hadarin ambaliyar ruwa.