Rayuwar ’yar gagara
Karuwanci bakar sana’ace da wadansu mata da ba su samu tarbiyar kirki ba ko wadanda Shaidan ya samu kutsawa cikin zukatan suke yi.Zai yi wuyar gaske a samu babbar mace wato mai yawan shekaru wadda ta shiga harkar karuwanci kai-tsaye, mafi yawa karuwa takan tsunduma harkar ce lokacin da take budurwa. Galibin karuwa ko ’yar […]
Karuwanci bakar sana’ace da wadansu mata da ba su samu tarbiyar kirki ba ko wadanda Shaidan ya samu kutsawa cikin zukatan suke yi.Zai yi wuyar gaske a samu babbar mace wato mai yawan shekaru wadda ta shiga harkar karuwanci kai-tsaye, mafi yawa karuwa takan tsunduma harkar ce lokacin da take budurwa. Galibin karuwa ko ’yar gagara takan fara nuna sha’awar shiga harkar ce sanadiyar rashin tarbiyya.Daga nan sai kwadayin abin duniya da kuma hangen na wani ya rika shiga mata zuciya. Mafi yawa, za ka ga karuwa mace ce wadda ba ta da gashin wance amma kuma tace tana son kitso irin na wance! Daga nan za ta fara ’yan sake-sake ina za ta samu kudin da za ta rika sanya atamfa mai tsada ko cin mai dadi asha mai dadi ko rike waya mai tsada?
Hanyar farko za ta yi kokarin kulla kawance da matan da ke da duk irin wadannan abubuwa da take burin ta ga ta samu. Wata ke nan yayin da wata kuma za ta je kai-tsaya ga namijin da take hangen duk abin da ta tambaye shi za ta samu. Daga nan ne fa tafiya za ta fara nisa.Bayan ta kulla kawance da ’yan uwanta mata ko maza tilas ne za ta zamo mai yin biyayya gare su domin abubuwan da take samu daga wurinsu. Daga nan sannu a hankali za ta fara aikata duk wasu abubuwa da suke aikatawa domin ganin ta samu zama daram a cikinsu. Zai yi wuyar gaske ka samu karuwar da ba ta yin shaye-shaye ko wadda ba ta fara da shaye-shaye ba. In tafiya ta yi nisa za ta fara raka kawayenta wuraren fati da shakatawa daga nan za ta fara cin karo da manema mata wanda kowanensu da zarar ya ga sabuwa babban kokarinsa shi ne ko nawa ne zai kashe mata domin ya yi lalata da ita. A lokacin ne za ta fara kama kudaden da ba ta saba kamawa a gidansu ba, daga nan sai idonta ya kara budewa inda za ta rika kallon mutanen gidansu da sauran wadanda ba sa yin wannan harka tamkar ba su waye ba.
Za ta ci gaba da cin karo da manema mata iri-iri kowa zai zo mata da irin tasa dabara ko hikimar don ya kai ga biyan bukatarsa a gare ta. A wannan lokaci maza za su yi ta rige-rigen zuwa wurinta kuma duk abin da take bukata za su yi mata ba tare da bata lokaci ba, kai wani lokacin ma har gasa ko gwaninta mazan za su rika yi, idan wannan ya ba ta taro, wannan zai ba ta sisi. Tauraruwarta za ta rika haskakawa na tsawon lokaci a wannan lokaci za ta rika jin duniya tana yi mata dadi tamkar tana kan shillo.
Haka za ta yi ta barje guminta tana sheke ayarta babu abin da yake bata mata rai kuma duk kudaden ta take samu za su rika karewa ne wajen sayen kayan sawa da man shafe-shafe da sabullai masu tsada da kuma kayan shaye-shaye da zuwa wajen ajo da lika wa mawaka kudi. Haka za ta yi ta sharholiyar har ta kama dakin haya a gidan magajiya inda za ta ci gaba da gudanar da bakar sana’ar tata. Sai dai ana haka ana haka mazan da suke tarayya da ita duk wanda ya biya bukatarsa da ita a hankali a hankali za su rika guje mata inda za su rika komawa ga sabuwar shiga. A haka kasuwarta za ta rika ja da baya. Idan tafiya ta yi nisa ruwa ya fara kare wa dan kada sai ta rika zuwa gidan sayar da abinci ko shagon sayar da abinci da magabatanta karuwai ke da su ta rika taya su aikin abinci. Haka tafiya za ta yi ta tafiya a karshe ita ma ta bude nata shagon sayar da abincin. Haka za ta yi ta rarrafawa idan tura ta kai bango jarin tuwo-tuwon ya kare a karshe za ta koma kofar gidan magajiya ko wata ’yar rumfa ko karkashin wata itaciya tana sayar da taba sigari da goro.
Tsufa na kara shigo mata Naira na kara yi mata nisa. Za ta yi ta lallabawa da wannan sana’ar sigarin da goron a karshe jarin sigarin zai yi mata nisa sai a rika ganinta ta kasa ’yan kwarorin goro a tire, tun tana samun na atamfa sai a ga na sabulu na neman ya gagare ta. A lokacin da ta kai kanta wannan yanayi za ka ga wadancan maza da suka yi tarayya da ita lokacin da tana cikin ganiyarta za su guje ta domin lokacin ta tsufa kuma ta zama abin kyama gare su.
A wannan yanayi da ta jefa kanta a ciki goron da ta ci da tabar da ta yi ta zuka lokacin da take holewarta za su taso mata haikan ta yi ta fama da ciwon tari da ciwon kirji babu mai son ta rabe shi!
Haruna Muhammad Katsina
Shugaban Kungiyar Muryar Jama’a ta Jihar Katsina
07039205659 ko 07057491050